Tambayoyi

Shin zayyu a rantsar da mai shaida?

admin September 08, 2020


jawabai

Sheikh Ibrahim saleh Alhussaini: Wannan ya kunshi ijtihadi,sabi da shaidu ba'a sasu rantsuwa,sabi da an tabbatar masu adalchi ne kuma mutum da yake da adalchi ba ya rantsuwa,sabi da rantsarsu yana nufin tuhumatsu,amma ra'ayin malamai shine chewa yadda zamaninnan rashin amana yayi yawa kuma aka rasa halaye da kwarai toh yakamata a rantsar da mai bada shaida,ka gane?kaman Kaman ka ari Kudi a wajen wani sai kasami wani idan ka batar da kudin ya shaida chewa ba ayi haka ba,ko kuma mai dinki a daa idan kabashi dinki kuma wani abu ya bata,toh ba komai sabi da akwai yarda a lokachin kaman yadda sayyidna Ali ya fada,amma yanzu lokachi ya chanza,sabi da haka shaidu ya kamata a rantsar da su a wannan irin zamani wanda adalchi shaidu yake da wiya chiki.kuma wannan fatawa tana iya chnzawa da chanjin wassu sharruda sa yanayi,kaman yadda wani misali a larabchi ya ke chewa (igiyarka tana wuyanka kuma kane mai shi)wanda yake nufin kana da chikakken iko,kuma yana nufin na sakeki) ka gane? A wanchan lokachi ma"anan da zai zo wa matan shine saki,idan yache ba ya nufin komai to za a tuhumesa da chewa yayi niyyan wani abu kuma ya janye, idan kuma yache yana nufin saki ne to lalle ta saku,idan kuma wanda bai shiga da matar ba to za a daukeshi saki daya,amma a daa wa'yennan abubuwa sun sha ban ban sabida ala'adunsu daban da namu,sabi da haka su a lokachinsu ranstuwa tana nuna tuhuma ne da rashin yarda.

Amma a wannan lokachi idan ba kayi haka ba to za karasa hakkinka, toh haya mafi sauki shine yanemi mai shaida tare da rantsar da shi. Ka gane?

admin September 08, 2020