Tambayoyi
Me hukunchin bin sallah ta hanyan ji ta speaker?
What is the Islamic ruling, on the prayer with the assistance of loud speaker or through radio sound, and what will do if the sound got disconnected during the prayer?
jawabai
Sheikh Ibrahim saleh Alhussaini: Mamu bazai bi liman ba in baya jin duk
wata harka da yake yi,Idan kuwa limamin yana da nisa sosai to sai kaje
masallachi ko kada kabisa idan kana da wani uzuri da zai hanaka zuwa
masallachi,wannan fa idan baza ka iya jin duk wani motsi da limamin ya ke yi
kuma baka da tabbachin binsa dai dai,a malikiyya ansani chewa ana iya bin
limami da yake da nisa kaman wanda yake qubais zai iya bin limamin ka'aba,haka
Imam malik yache,kuma Mamu zai iya bin limami ko da akwai tabki da ya raba
tsakaninsu ko hanya,sabi da haka za aiya be ta speaker idan tana da inganchi
bata Yankewa,amma bazayyu abi ta hanyan radio ba kaman yadda su sheik Ahamad
ibn Al-sadiq Al-amari da sheikh Abdullahi ibn Al-siddiq Al-ammari Suke da
ra'ayin chewa za a iya bin salla ta radio ko ma ta hanyan wayan tangaraho ko da
akwai tazara mai nisa tsakanin mamu da imam,wannan kuma zayyu ne kawai idan
babu banbanchin lokachi tsakani,Misali idan mai watsa labarun radion yana makka
ne kuma mai bi ma yana makka ne a haram amma yana nesa toh wannan zayyu ko kana
gida kabi,amma ni bana goyon bayan haka,amma wannan shine ra'ayinsu hakama
makiyansu,kana dai ganewa ko? Ansan dai dole ne mai bin yazama yan jin duk wani
motsi na imam,idan kuma za a iya dauke wutana lantarki Muryan ya yanke to bai
kamata yabishi ba,idan kuwa yabi ya samu raka'a sai ya yanke to sai yakare daya
yayi nafila yayanke kuma yafara sabon salla.