Tambayoyi
Ya halatta ga mache mai haila ta taba Alkura'ani?
Is it permissible for a menstruating woman to touch a part of the Qur’an, whether she is a teacher or a student. Is a part of Quran and entire Qur’an equalized in this matter?
jawabai
Sheikh Ibrahim saleh Alhussaini: mache da take haila za ta iya karanta
Alkura'ani amma bazayyu ta taba Alkura'ani ba ko wani sashe daga Alkura'ani, ko
da ita mai koyarwa che ko mai koya,taba wa da malamai suke maganan zayyu ga
dalibi shine na mara alwala ba na mai haila ba,haila rashin tsarki ne babba
wanda ya ke da ban banchi da na rashi
alwala,amma mai haila za ta iya karanta Alkura'ani kaman ayatul-kursy ko
Laqad-ja'akum ko wani sashe a Alkura'ani wanda ta haddache, amma taba
Alkura'ani sai mai tsarki,to ba zayyu ta taba ko Juzui ba ko dai wani bangare
wato na Alkura'ani.
To amma zayyu ta daga kaya wanda da kawai Alkura'ani a chiki?
Eh wannan zayyu sabi da ba tabashi tayi ba,ba kai tsaye ta tabashi ba,
Me ma'anan fadin Allah SW " ba mai tabashi sai masu tsarki" kuma
me hukunchin bada Alkura'ani mai fassara ga wanda ba musulumi ba sabi da su
karanta su san sakon da ke chikinsa na
musulinchi?
Sheikh Ibrahim saleh Alhussaini:
Hakane "ba mai tabashi sai masu tsarki" a wani tafsirin yana bada
ma'anan chewa ba mai tabashi sai mala'iku,a wani bayanin kuwa ba mai tabashi
sai wa'ayenda suka imani da Allah,wani ma'anan kuwa ba mai tabashi sai su
tsarki da alwala,ka na ganewa ko?
Kan maganan a baiwa wanda ba musulumi ba kuwa,kasani chewa muna wani zamani
wanda marasa imani sun fi karfi a chiki,wani zamani da ba wanda zai iya fadan
gaskiya wa mutane,idan har da bukatan ayi haka to ya kamata a fassara chikin
wani yare amma kar asa rubutun larabchi chiki,sai a baiwa duk wanda akeso a
baiwa,amma yanayin yadda akeyi yanzu ana badashi a matsayin kewta ko ko sarwa
wanda ba musulumi ba a rubuche da larabchi abune da ba halatta ba,sabo da
Manzon Allah tsira da aminchin Allah ya tabbata a gareshi ya hana ma tafiya da
alquraani garin musrikai,za mu iya chewa toh kuwa da Manzon Allah SAW yananan
yanzu haka za hana wannan ma.