Tambayoyi

Shin zayyu kusantar mata da akayi wa kutba kafin aure?

admin September 08, 2020

Is it permissible testing an engaged woman that, whether she is infected with AIDS or not; before marrying her?


jawabai

Sheik Sharif ibrahim saleh Alhussaini: shin kana nufin wanda aka daura aure ko wanda akayi tambaya ma aure? Ko kana nifin tabbbatar da chewa wanda za aura ba ta da chutar SIDA?

Question:yes

Sheikh Ibrahim saleh Alhussaini: ba matsala tabbatar da chewa matan da za aura bata da chuta,gaskiya ne chewa komai kaddara,amma wannan zamani ne na ban mamaki,sabi da haka ba wani abu chikin wannan musamman a wurare da chuta irin wannan ta yadu sosai,kaman wassu kasashe na Africa,da kasashen yamma,kuma wannan chuta che mai karya garkuwa to ba laifi bane yin hakan,sabi da Manzon Allah tsira da aminchin Allah su tabbat a garesa ya umurchi wani sahabi da ya duba fiskan wanda zai aura ko tana da wata chuta a idonta wanda ba wani chuta ne sosai kawai dai zai rage chaw ne na mache toh mai zai hana a duba na babban chuta Kamar SIDA wanda sanadiyanta zina da su Madigo da dai ayyuka na assha,yana de keu kuma ayisa chikin sirri,sabi da idan kasamu mache kai tsaye kache mata za ka kaita gwaji na SIDA to za ta che ma a'a ita Allah ya tsareta , a wassu wurare irin namu bazayyu ba sabi da zai nuna kaman kana zargin Wanda za ka aurene wassu kuwa sunama zuwa yin gwajin haifuwa Kafin aure toh kaga wannan abune da zai Saba wa Ka'ida na aure a sunnanche,ko kuma zama da mache zuwa shekara har sai ta haifu kamin ayi aure,idan ka ka tambayi wassu yen uwa a Nigeria sai suche ma a'a suna zuwa ne wajen baban matan suche mar ka aura min yerka idan yache ya bayar sai abada wani dan kudi sai su umircheta da taje ta zauna da shi,bayan haka idan ta haifu za suchi gaba da aure idan kuma ba ta haifu ba sai ya saketa, kaga wannan kuma babbab laifi ne. Allah ya kiyaye.

admin September 08, 2020