SHISIC

Chibiyar Musulinchi ta sheikh Shariff Ibrahim Saleh

Chibiyar tana babban birnin tariyya ya Nigeria Abuja

Chibiyar an kafata ne da manufan bada taimako ga wanda suke da Binchike mai zirfi a ginshikin musulinchi da kuma hada kan al-ummah ba a Nigeria kada ba hada da yammaachin Africa baki daya

Ankuma kafa chibiyar ne saboda karanchin madogara da za tahada malaman da suke da ra'ayi akan wata mas'ala wanda za su iya hada al umma baki daya domin karfafa danganta tsakaninsu

Dukkan chibiyoyi na musulinchi da suka bada gudunmawa sosai sun Gaza wajen kula da aiki da magabata suka rubuta sabo da litattafnsu a yau suke fiskantar barazana

Ire iren way'ennan raunuka da suke fuskantar musulumai da musulumai su saka sa aka zage wajen kafa wannan chibiya

Chibiyar baza ta tsaya kawai kan koyarwa ba za tahada ne da binchike mai zirfi da nazari kan al-aadu da dabi-u da kuma waraware duk wani abu da yake addabar musulumai

Manufofi na kafa chibiyar

Daga chikin manufofin kafa chibiyar ana son ta kasanche babbar chibiya da ke kula da harkar karatu ta musulinchi da kuma kulawa da yaduwar zaman lafiya a ko ina

Hange :chibiyar ta na da hangen samar da fitattun binchike ga Daliban ilimi da fatawowi da bada shirye shirye da horo ga dalibai,da wallafa takardu,da tsare tsare da za su hada kan musulumai,wanda za sukasanche sunayin hakanne tare da chibiyoyi na musulinchi da suke duniya tare.

Yanayin chibiyar

Ginin masallachi na zamani da zai ishi massallata fiye da 900 maza da mata,wanda kuma za a iya yin Salman Jumma'a a chiki

Ginin ma'aikata wanda ya ke beni mai hawa biyu ne  wand zai zamo tsakiyar chibiyar

Da kwai kuma ginin babban daki na koyarwa da na bada horo da zai dau akalla mutane 500 da kuma ginin dakin takardu da dakin karatu,da kuma studio da wajen na karatun ilimin taurari da kuma wajen daki na taro da shawarwari

Akwai kuma wajen zama na malami da ya hada da wajen zama na limami da gidan chin abinchi