Sheikh sharif ibrahim saleh an haifesa ne adaren asabar
12 ga watan mayo shekara 1983 a kawyen iredibe,inda qabilar shuwa arab take
fatauchi,kusa da karamar hukumar Dikuwa a jihar Borno,mahafinsa shine sheikh
Muhammad Alsalih,da ga yunus Alnawwy,mahaifinsa shahararren melamine mai yawan
ibada,mahaifiyarsa Fatima yer sheikh Muhammad albashir alhusaini,ta shahara da
karamchi da kuma yadda dukkan mutanen wajen suke mutuntata,tana kuma daga masu
bada tarbiya da kuma son neman ilimi,ta rasa mai dakinta ne yayinda dansu yake
da shekera bakwai,ita ta kula da tarbiyansa har ya girma.Ba shakka ita tazamo
jagora sheikh Ibrahim saleh har ya kasanche shahararren jigon malami a
duniya.ta kasanche mai hanasa yin kasuwanchin dabbobi saboda kar ya shiga mar
gaban karatunsa,yayinda yake da shekara sha biyar mahaifiyarsa ta kasanche mai
sa ido kan duk wassu lamura da danta yakeyi.
Sheikh Ibrahim ya kasanche chikin dunniyar
alquarani yayinda yake dan karami kasanchewar mahaifinsa mutum ne mai yawan
nafilfili chikin dare,hakan yasa shi ya haddache yawa surori tin kan akaisa
makarantan alquraani,abinda yasa yawanchin almajiran babansa chikin rudani
yayinda yake musu gyra in sunyi kuskure,duk da kasanchewansu suna gaba da shi a
karatu, kasanchewar dukkanni bangarori biyun na mahaifansa shaharraru ne a
ililimin addini wannan ya sa suka dage tukuru wajen ganin dannasu ya zamo wani
jigo a ilimin addini.
A shekara ta 1944 zuwa 1964 sheikh Ibrahim saleh ya jajirche wajen neman
ilimin alquraani dakuma ilimai da suke da dangantaka da fahimtar alqurani
kamansu mandiq da falsfa,da balaqa wato ilimin fasaha,nemansa ga fitattun
malaman alqurani ya fara ne daga chikin gidansu zuwa ga shararrun makarantun
alquraani da ka fi saninsu da tsangaya ko tsangayoyi,a Maiduguri,da kuma makwabta,saninsa
ba da wuya bay a kasanche Kaman wani gobara da ta mamaye ko ina game da zirfin
da yayi wajen sanin alqurani da ilimiin addini,ya zamo sananne sabi da ziyara
da yake wajen neman ilimi a wurare kamansu Tarmuwa,Gulumba,Gide,Maishimari,da
kuma Maiduguri,ya zamanto madaukaki kuma shaharre chikin daliban ilimi har ma
da fitattun malamai sabo da hazakarsa wajen neman ilimi da dadin karatunsa na
alquraani da kuma kyewawan dabiunsa.
Da kawai shararrun malamai da sukayiwa
shehin kyekkyewar shaida kuma suka yaba mar kwarai yayinda yake dalibi yanan
neman ilimi,kamansu sheikh muhammadul habib,jika ga sheikh ahmadu
tijjani,yayinda ya ziyarchi Maiduguri da ga kasar Algeria,da sheikh Muhammad
Mustafa Alawi,da Shekh kadi lari abani,da sheikh Mustafa birshi,da sheikh ahmad
ali abulfathi,da sheikh gibirima dagira,da sheikh tijjani usman,da sheikh
Abubakar atiku,da dai shehinnai masu dimbin yawa da gaske.
Daga chikin manufofinsa da aka fi saninsa
da su shine ko wani dalibin ilimi yana da wani jigon malami da yake son zama
misali garesa,shi ko sheikh ya kasanche yana son zama Kaman imam Algazali,da
kuma alhafiz bin hajar Alasqalani chikin ilimin hadisi,wajen ilimin wake kuwa
da shaharren mawallafinnan imam abdulwahhab sharani,kuma ya kasanche ya na
masaltuwan matuka da wayennan malaman ga dukkan wanda ya sanhi.
Heikh ya kasanche malami ne wanda ya nemi
iliminsa chikin gida nan Nigria kuma hada da neman malami wajen Nigeria abinda
yasa shehi yaje ziyara neman ilimi garuruwa da dama chikin kasashen Africa har
ma da sauran kasashe.
A shekara 1963 shehi yayi tafiyarsa ta farko zuwa kasa
mai tsarki domin sauke farillar hajji da kuma samun ijaza wato shaida daga
malaman ilimin hadisi,qurani da riwayoyinsa da kuma ilimai na addini baki
daya,inda ya hadu da shararrun malamai kuma fittattu kan wayennan bangarori na
ilimi da yaje nema,kaman sheikh umar bin ali alfaruq Alfullati,da sheikh Alawi
bin Abbas almaliky,da shekh muhammad arabi altubbani,and sheikh hassan bin
ibarahim alashari,da su ka tabbatr da chanchantarsa da yasamu numban yabon daga
wajensu,hakazalika shekh ya sami ijaza ta yabo da ga malaman kasar egypt a
wajen ilimin hadisi daga sheikh muhammadul hafiz,kuma daga wassu bangarori na
ilimin addini kaman ilimin kartuttunkan alqurani ya sami shaidar yabo daga
wajen shararren makaranchi sheikh mahmud khalil al husari,da kuma shekh Amir
bin usman alsayyid,chikin wadanda suka mar lamba ta yabo da shaida kan ilimim
hadisi ha ila yau dakwai sheikh Ahmad nur albarmi daga kasar pakistan,sheik
muhammad zakariya bin yahya alkhan dahlawi daga kasar india,dakuma sanannen
malaminnan na islama sheikh ibrahin inyass daga kasar senegal.
Yana da matukar muhimmanchi sanin
chewa sheikh ya kasanche shararren dalibin ilimine chikin shekaru ashirin
kachal,inda ya samu horaswa ta ilimi anan kasa nigeria sai da hakan baya nuna
chewa bai da malami akasan wajen kaman yadda ya gabata,sabo da gogayyarsa da
malamai na chikin kasa tasa yazamo sannanne ga malamai dake kasan waje.
Duk da yake shekh ya sami dukkan
iliminsa ne chikin kasa Nigeria hakan yasa duk wani abu da akeyi na ilimi a
Nigeraia sheikh na da hannu chiki,sabo da ba wata aya da za akaranta da sheikh
bai samo wani hadisi dake bayani akanta ba,ko kuma maganan wani sahabin annabi
akanta,kuma sai ya anbachi dalilin da yasa aka sauko da wannan aya wato
(asbabunnuzul),kuma sai ya ambachi shin wannan aya ko an soketa da wata ayar
wato abinda malamai suke kira (nsikh wal mansukh) yakan anbachi duk wannan kan
ko wani aya.
Baichin zirfin ilimi da shehi
yayi a Bangarori na ilimin addinin islama da muka anmbata hakanan shehkh ya
zirfi chikin ilimin tauhidi da fiqhu inda yasan duk wata fahimta ta duk wani
malami kan ko wacche mas’ala kuma yasan sabanin ra’ayi tsakanin wayennan
malamai,dakuma kan wata hujja wayennan malamai suka gina ra’ayinsu,masala idan
har kan addini ne baya daukanta da sauki,yasan fahimtar imam malik kwarai da
gaske hakama dukkanin sauran mazhabobi musamman kuma abinda yakara mar sani kan
sauran mazhabobin kakkyewar alaqarsa da malaman da suke alaqa da mazhabobin.
A shekara 1963 shekh ya zamo mai
shiryawa gomnatin arewachin nigria yadda za su maida tsangayoyin alqurani suna
masu bada ilimin alqurani tare da ilimin zamani,a kasar Borno kuwa lokachinda a
ka bude makarantar bada huraswa kan ilimin addinin islama da shara’a (BOCOLIS)Gomnatin
Borno ta sanya sheik shine mai gudanar musau da yanda za atafiyar da koyarwa a
wannan makranta,bayannan sheikh yazama daya daga chikin masu fada aji kan
sha’anin makarantu(schools governing boad)daga shekara ta 1984 zuwa 1990 kuwa
ya zamo shine shugaban wannan gungiya ta masu fada aji akan harkar makaranto a
kasar Borno,a shekara 1990 ha ila yau aka zabi shehi da yazamo shine shugaba na
harkadda ta shafi aikin hajji a jahar Borno wato (chairman of the state pilgrim
welfare boad)ya shafe shekaru biyu yana wannan matsayi daga bisani yakoma kan
matsayinsa na shugaban harakadda ta shafi ilimim a makarantar BOCOLIS.
Sheikh ya kasanche ya na alaqa da
gumnati ta kasa baki dya inda ya kasanche ashekara 1976 mai bada shawara na din
din din kan harka da ta shafi
addini da makamatan hakan,haka kuma
yakan wakilchi Nigeriya a duka wata harka ta addini akasan waje kaman kasar
saudiya,iran,Egypt,Turkey,Libiya,Morrocco,Malesiya,Indunusiya,Pakistan,Senegal,Iraqi,Sudan,da
de sauransu,ya kuma shafe shekaru yana wa’azi a watan azimi afadar shugaban
kasa a Lagos,kuma yayi wannan ga shwadannin kasa da dama,shekh yana kan gaba ko
da yaushe kan wayarwa mutane muhimmanchin zaman lafiya da hadin kai tsakanin
musulumai da muhawara ta salama tsakanin addinai anan kasa Nigeraia da duniya
baki daya.
Sonsa ga rubuche rubuche da kuma dukufa da zirfin nazari chikin ilimi hakanne yasa shekih ya wallafa litattafai 400dasuka hada da kasidu sama da dari da ya rubuta a tararruka daban daban da harshen Larabchi,wadanda suka shafi ilimin alquraani mai girma da hadisan manzon Allah tsira da amichin Allah yatabbata a gresa,tarihin falsafa,ilimin fiqhu,ilimin taurari,ilimin sanin harshen larabchi,ilimin sufanchi,ilimin siyasa a musulinchi,ilimin shria kan abinda ya shafi gado,ilimin zamantakewa ta zaman lafiya tsakanin al-ummu.