Tambayoyi
Shin ana shiga aljanna da aiki ko Rahman Allah?
I request you to explain us a difference between Prophets’ Quote “Any of you will not enter Paradise unless God bless you with His mercy” and the Almighty’s revelation “Enter Heaven by what you did.” Is entering Paradise by means of this verse or by Hadith?
jawabai
Sheikh Ibrahim saleh Alhussaini: fadin Annabi SAW kan wannan shine ba wani
daya chikinku da zai shiga Aljanna da Aikinsa, sahabbai suka tambayesa:ko kaima
ya Annabin Allah,ya che:ko nima sai dai Allah ya lillibeni da Rahamansa,sai
kuma fadin Allah " ku shiga Aljanna da ayyukanku" wannan yana nuni ne
chewa Allah yana baiwa muminai izinin shiga Aljanna da ayyuka wanda in ba dan
rahamansa ba sa ba su samu daman aikatasu ba ,toh kaga basu shiga Aljannan ba
sai da rahamansa,to kaga fassarar hadisin da ayan Alkura'ani ayana tana nuna
zahiri hadisin kuwa yana nuna badini ne, hakikan lamari shine azimin
mutum,sallansa,da sauran ibadunsa,duk suna da alaka da rahaman Allah,bazai zamo
mutumin kirki ba sai da rahaman Allah,bai iya yin koman da ikonsa ko
karfinsa,shi yasa aka koya mana chewa duk abinda za muyi mufarasa da anbanton Allah,da
kuma sanin chewa ba abinda za mu iya yi sai da ikon Allah,"Allah shi ya
halicchemu da duk abinda mukeyi" sabi da haka da mu da ayyukanmmu duk na
Allah ne,kaman yadda Manzon Allah SAW ya che wa wani " kai da arzikinka
duk sa na mahaifinka ne" kana ganewa ?
Fassaran hadisin da ayan shine ,hadisin yana fassara karshen matsalan chewa
duk wani aiki da kayi yasamu ne da rahaman Allah,kaga ansami izinin shiga
Aljanna ne da rahaman Allah,kuma dukammu munsan Aljanna Rahama che ta Allah
amma ba mu isa musameta da ayyukanmu ba,kaman yadda ya che a suratullail
"wanda yayi alheri da tsoron Allah za mu sawwake mar,amma wanda bai bayar
ba to za mu sawwake mar hanyar ba"wannan yana nuna chewa Allah ya Sanya
maka shaidu a sassan jikinka da ayyukanka a matsayinka na mumini,kana ganewa
koh?
Amma idan musulumi baya salla,baya azimi,baya bada zaka,yaya za agane chewa
shi mumini ne,ayyukansa shaida ne a garesa kuma suna tabbatar da chewa shi yana
kan hanya madaidaichiya idan kuma yana aikata ayyuka tsabanin haka kuwa to lalle
tana hanyan bata.