Tambayoyi
Shin ya halatta yin salla a Jirgin Sama
Is it permissible to pray inside airplane according to Maliki school of thought?
jawabai
Sheikh Ibrahim saleh Alhussaini: mu a malikiyya bamayin salla a jirgin sama
sai dai idan jirgin yana kasa,amma in har jirgin yana sama da Ka'aba to bamayin
salla a chiki, amma naga dayawa daga chikin mutane sunayin hakan, akwai wata
tawaga ta mutanen Egypt da suka taba samuna akan na jagwarchesu salla a jirgi,
nache musu ni banayin salla a jirgi sabi da ni mazahaban malikiyya nake bi,
amma ga wani daga Abuja zai iya zama muku limami, ni dai banyi salla ba sai da
muka sauka nayi a zahar,idan kana tafiya za ka deyawa chikin mutane suna salla
a zauna jirgin sama,amma ni bana goyon
bayan hakan,amma idan jirgin yana kasa toh ba wani matsala,wanna shine ra'ayina
kan wannan kuma bani chanzawa sai in na sami hujja mai karfi.