labarai

Fatawa Kan Batun Sallan Idi karama

August 06, 2020 admin الأخبار العامة News
News photo

(Maulana sheikh Shariff ibrahim saleh ya gabatar da wanna fatawa ne a shekara 1441AH -2020 )

Lokachin Annobar chutar Corona

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Tsrira ga Aminchin Allah su tabbata ga mafifichi Halitta Annabi Muhammadu

Wannan fatawa an bada ita ne jawabi ga tambaya da sarkin musulumai Alhaji Muhammadu saadu Abubakar IIICFR shugaban (NSCIA)wanda Yanemi bayanin daga komitin kuma hakazalika komitin (JNI)hakama shuwagabannin  komitochi na addini daban daban na na kasa da na waje kan yanda annobar take ta dauke rayuka a duniya,ya kuma  za a gudanar da  sallar idi.

A wannan lokachin kuwa ba wata kafa ko Gomnati da ta nuna chewa taron Jama'a zai iya yada chutar .wand fatawar ta kasanche ne 23 ga watan shabaan 1441AH wanda yayi dai dai 16 April 2020

A lokachin akanyi sallolin farilla da na jumma dama tarawihi da tahajjud amma da Tazara tsakanin mutane.

Sai dai wannan fatawa ta shafi sallan Karaman idi ne a wannan annoba.

Sabi da ita sallan idi tana daga chikin sunnoni da dimbin jamaa suka rawaito daga Manzo Allah tsira da aminchin Allah su tabbata agarrsa,ana gudanar da sallan idi ne a budadden waje mai girma ba chikin masallachi ba,kuma yana da muhimmanchi mata da maza su Halarta, kuma ana bukatar masallatan da su Halarta chikin kyekkyewar tufa da kuma yin anfani da tirare in ya samu,kuma mustahabbi ne da suji dibino kamin suje.

Idan har da kwai wani dalili da zai hanasu yin sallan a budadden waje kaman Chanjin yanayi,ko rashin zaman lafiya,ko kuma wata annoba Kamar ta corona,wanda za ta iya hana tafiye tafiye,ko kasuwanchi,domin stare rayuka wanda yana daya daga chikin maqsudi na Shara'a,to yana da ga chikin sunna da Ayi sallan idi a gida ba tare da yin huduba ba.

Marubuchin takardan mukhtasar ya bayyana a chiki inda yache "ha wanda sallar idin batazamo dole akansa ba ko ya rasa sallan idi"

Imamul kharshy yayi bayani chewa mustahabbi ne kan wanda sallan jummaa ko idi ba ta wajabta Kansa ba da yayita shi kadai ko kuma chikin jamaa.

Marubuchin takardan minahul Jalil a bayaninsa kuwa,ya che wannan bayanin na Mukhtasar yache wannan bayanin ya na baiwa mutum daman yin sallan shi kadai ko chikin jamaa.way'nnan za a iya anfani da su kan wannan matsala.

A wani bayanin kuwa ,ana bukatar masallachin da yayi sallar shi kadai ne ba'a kuma bukatar sa da yayi chikin jama'a.

A ra'ayin Abul Hassan Ibn Arafah muwallafin takardan Taudih kuwa a irin wannan yanayi mutum bazayyi sallan idin chikin jamaa ba kuma bazayyita shi kadai ba.

Mu kuwa muna bada fatawa chewa a irin wannan yanayi mutum yayi sallan idin a gida tare da iyalansa.muna kuma kafa hujja ne da hadisi da imam Bukhari ya rawaito wanda yake hadisi ne mai ingantacchiyar riwaya,wanda Anas dan malik Allah yayarda da shi ya a rawaito,da kwai lokachinda yayi sallan idi d shi da Iyalansa a wani waje da ake kira Az Zawiyya a layin Basra.

Sallan idin ana yinta ne yayinda imam din zai Rakaa biyu,a Taka'an ta farko zayyi kabbara 7 sai ya karanta Fatiha da suratul-Ala ko kuma ko wata sura daga Alqura'ani,a raka'an na biyu kuwa zayyi kabbara 5 sai ya karanta fatiha da suratul-qashiya ko kuma ko wata sura,sai ya qaddamar da huduba,sai dai ba'a yin huduban in a gida akayi sallan .

A wannan yanayi da killachwa bai zama na gaba daya ba to za a iya yin sallan a budadden waje ko kuma a masallachi,a chikin dukaan yanayin guda biyu ya kamata a kula da yin tazara tsakanin masallata,wanke hannaye da kuma saya takunkumi na fuska sabi da sunna ne kada mai lefi ya jawo wa kansa kamuwa da chuta.

A chikin wannan yanayi na annoba ya kamata a Gujewa duk wani abu da ake shakka sabi da a kare rayuwan al umma.

A karshe kuwa muna kira ga dukkanin shuwagabanni da su kula kwarai da abinda zai jawo hadin kai tsakanin al ummu, kaman yanda Allah ya che "a riki igiyar Allah baki daya kuma a gujewa rarrabuwa"(Al imran :103)

Yana da muhimmanchi Musani chewa kowanmmu makiyayi ne kuma ko wannemmu za a tambeyesa ranan Gobe  kan abinda akabasa da yayi kiwonsa,mai mulki makiyayi ne kuma za atambayesa kan wanda yake mulka,mai gida makiayi ne kama za a tambayesa kan iyalansa,mache mai kiwoche kuma za a tambayeta kan mijinta da yaranta, hakazalika kowa makoyayi ne kuma za atambaysa kan abinda yake kiwo.Abdullahi bin umar Allah ya kara masa yarda ya rawaito.Bukhari da muslim

Allah ya bamu nasaran da shiryiwa !

Allah kuma ya albarkacheku baki daya!

Shekh shariff ibrahim saleh Alhusaini,CON

Shugaban komitin fatawa na (NSCIA)Nigerian supreme counsil for islamic affairs

Kuma shugaban Jama'atu Nasril Islam (JNI)

27 ga watan Ramadan shekara 1441

Wanda yayi dai dai da

20 ga watan may shekara t 2020

Babu wassu bayanai yanzu.
Bukatar bayanan sirri

sai kashiga chiki saboda bada bayani.

Shiga chiki