Saƙon Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhussainiy (RadhiyalLahu ta’ala Anhu) zuwa ga jagororin Ansaruddeen – Tijaniyya – Najeriya, Lokoja, 2022(
Zuwa ga masu girma mambobin majalisar zartarwa na Ƙungiyar Ansaruddeen – Tijaniyya, da dukan halifofi, da muƙaddamai, da muridai, da sauran ɗaukacin Musulmai a Jahar Kogi- Najeriya, da ma dukan sassan duniya - Allah ya kiyaye su duka da kiyayewarsa, Amin.
Assalamu alaikun wa rahmatulLahi ta’ala wabarakatuhu,
Bayan haka:
Ina farin cikin sanar da ku cewa: lallai a cikin yanayi na farin ciki, da murna, da jin daɗi muka amshi takardar gayyatarku da kuka aiko, domin halarci halarta, da kuma gabatar da jawabi a taronku na shekara- shekara, karo na huɗu, wanda –da ikon Allah- za a yi shi a wannan shekarar, daga 6 zuwa 8 ga watan Junairu, 2022 a Jahar Kogi, Najeriya, ƙarƙashin taken: (Hanyoyin da Annabi ya bi wajen warware matsalolin bil’adama).
Wannan kenan, a daidai wannan lokacin da muke gabatar da hanzari na rashin halarta, da gabatar da jawabi; saboda yanayin lafiya da muke ciki, da kuma irin yanda annobar Korona take ƙara yaɗuwa a ‘yan baya- bayan nan a ƙasashe masu yawa, abin da yake sanya damuwa, inda hakan ya wajabta yin aiki da matakan kare kawuna da yin riga- kafi, saboda aiki da sunnar masoyinmu zaɓaɓɓen Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a irin wannan yanayi da yake bijirowa, haka ma aiki da bayanan hukumomin da abin ya shafa a ƙasarmu – Najeriya game da abin da ya shafi lafiyar dukan mutane, saboda kiyaye rayuka da shari’a ta bayar da umurni, lallai za mu yi amfani da wannan dama domin bayar da gudummuwarmu a wannan taro mai girma, na tunawa da haihuwar Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), rahamar da Allah ya yi wa halittu baiwa da ita, kuma ni’imar da Allah ya kwarara wa ɗaukacin halitta, da wasu bayanai da muka ciro daga shiryatarwasa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a fagen daidaita tsarin rayuwar Musulmi, da tsayawarsa akan madaidaiciyar hanya da ikon Allah, duka wannan yana cikin babin nasiha, da tunatarwa, da kuma yi wa juna wasici da gaskiya a tsakaninmu da ɗaukacin waɗanda Allah Maɗaukakin Sarki ya ba su daman halarta da gabatar da bayanai da kawunansu a wannan taro mai girma, ko kuma suka bibiyi taron ta hanyoyin sadarwa na zamani.
Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: (Ina rantsuwa da zamani; saboda yawan abubuwan da ya ƙunsa na ban mamaki da lura. Lallai kowane mutum yana cikin wani nau’i na asara; saboda rinjayar da son zuciya da sha’awa da suka taru suka yi masa yawa. Sai dai ban da waɗanda suka yi imani da Allah, suka kuma aikata ayyuka na gari, suka kuma yi ɗã’a da biyayya, suka kuma yi wa juna wasici da riƙo da gaskiya wajen i’itiƙadi da furuci da aiki, suka kuma yi wa juna wasici da haƙuri akan abubuwa masu wahala da suke bijiro wa duk wani wanda ya yi riƙo da addini, waɗannan kam, su ne masu tsira daga wannan asara, masu kuma babban rabo a duniya da lahira) [al- Asr: 1-3].
Bayani ya zo a cikin Hadisi mai girma da aka ruwaito daga Abu Ruƙayya, Tamim Bn Aus ad- Dariy (Allah ya ƙara yarda da shi), Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Addini nasiha ne), sai muka ce: ga wane? Sai ya ce: (Ga Allah da Manzonsa da shugabannin Musulmai da gama- garinsu) [Muslim da ma wasu]
Allah ya sa mu dace,
1. Da farko muna ƙara jaddada kira, da tunatarwa ga ɗaukacin Musulmai, musamman malamai, da masu da’awa duk da bambancin matsayi da garuruwansu, muna kira zuwa ga wajibcin yin riƙo da karantarwar Annabi mai girma wajen kira zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki; saboda koyi a nan dole ne, da kuma nesantar bidi’a da bin son zuciya da yake rarraba abin da Allah ya ƙulla na ‘yan uwantaka na imani, Allah mai girma ya ce: (Lallai muminai ‘yan uwan juna ne..) [al- Hujrat: 10], haka ma Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Ya ku waɗanda kuka yi imani, kada ku gabatar da kowane irin umurni cikin al'amurran addini da na rayuwa ba tare da Allah da Manzonsa sun ba ku umurni ba, ku sanya wa kanku katangar da za ta kare ku ga barin azabar Allah ta hanyar bin shari'arsa, lallai Allah na matuƙar jin duk abubuwan da kuke faɗi, saninsa kuma ya mamaye komai. Ya ku waɗanda kuka yi imani, kada ku yarda ku ɗaga muryoyinku birbishin muryar Annabi (SallalLãhu alaiHi wa alihi wa sallam) idan yana magana, ku ma kuna yi, kada kuma ku daidaita muryoyinku da muryarsa –kamar yadda kuke magana da junanku- gudun kada ayyukanku su lalace ba tare da kun san sun lalace ba) [al- Hujrat: 1- 2], haka ma Allah mai girma yana cewa: (Ya ku waɗanda kuka gasgata gaskiya, kuka kuma yi mata biyayya, ku amsa wa Allah a cikin zukatanku akan duk abin da ya ba ku umurni akansa, ku kuma amsa wa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) wurin isar maku da abin da Allah ya bayar da umurni akansa, idan ya kira ku zuwa ga umurnin Allah da hukunce- hukuncen da suke ɗauke da rayuwar jikkunanku, da na ruhinku, da hankulanku da zukatanku, ku sani cewa lallai Allah shi ne yake tsaya wa zukatanka, yana fuskantar da su yanda yake so inda shi ne yake shiga tsakaninku da zukatanku idan son zuciya ya tunkaro su, shi ne yake tseratar da ku daga gare shi, idan kun bi hanya madaidaiciya, kuma lallai dukanku za ku taru a ranar alƙiyama, kowa zai sami sakamakon aikinsa) [al- Anfal: 24], haka ma Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Kada ku kuskura ku kauce wa turbar da na shata maku, domin dai ita ce miƙaƙƙiyar hanyar da za ta sada ku da jin daɗin duniya da lahira, ku bi ta kawai, kada ku bi hanyoyin ɓata da Allah ya hana ku, gudun kada ku rarraba, ku koma ƙungiyoyi da jam’iyyu masu gaigayar juna, hakan sai ya nesanta ku da miƙaƙƙiyar hanyar Allah. Lallai Allah yana ƙarfafa bayar da umurnin ku nesanci saɓa masa) [al- An’ami: 153].
An ruwaito Hadisi daga Abu Najih, al-Irbadh Ibn Sãriyah (Allah ya ƙara yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa Ălihi wa sallam) ya yi mana wa’azi, wa’azin da ya sanya zuciya kaɗuwa, idanuwa kuma suka zubar da hawaye. Muka ce: ya Manzon Allah, kamar wa’azin mai ban kwana!, to yi mana wasiyya. Ya ce: (Ina maku wasiyya da tsoron Allah maɗaukaki mabuwayi, da ji da biyayya, koda kuwa bawa ne yake shugabantarku, domin duk wanda ya rayu a cikinku zai ga saɓani mai yawa. Ina horanku da sunnata da sunnonin halifofi na shiryayyu masu shiryatarwa, ku kama su da kyau, ahir ɗinku da sababbin al’amurra marasa asali a cikin addini, domin kowace bidi’a ɓata ce). [Abu Dawud da al-Tirmizi suka ruwaito, al-Tirmizi ya ce: Hadisin hasanun sahihun ne].
2. Aiki da taimakekeniya da gaske, kuma saboda Allah, da mantawa da kai, wajen samar da haɗin- kai tsakanin ɗaukacin Musulmai, da kuma tsakanin mabiya ingantaccen Sufanci na Ahlus Sunna, musamman tsakanin almajiran Maulana Sheikh Ahmad Tijani (Allah ya ƙara yarda da shi), Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: (Ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗayanku, kada ku kuskura ku rarraba..) [Ali Imran: 103], haka ma yana cewa: (Ku yi taimakekeniya a tsakaninku wajen aikata alhairi, da wajen dukan ayyukan biyayya da ɗa’a, kada ku kuskura ku yi taimakekeniya wajen aikata saɓo, da ƙetare iyakokin Allah, ku kiyayi uƙubar Allah da kamunsa, lallai Allah mai tsananin uƙuba ne ga duk wanda ya saɓa masa) [al- Ma’ida: 2].
3. Cigaba da wayar da kan muridai da talakawa cikin almajiran Maulana Sheikh Ahmad Tijani (Allah ya ƙara yarda da shi) a duk inda suke, akan muhimmancin ilimi da nemansa, da gina cibiyoyin ilimi, da ba su kulawa ta musamman; ba wai kawai ilmomin addini ba, a’a dukan ilmomin waxanda da su ne za a iya raya rayuwar duniya. Haka ma dole ne a yi riƙo da manhanjinsa (Allah ya ƙara yarda da shi), wanda ya ginu ne akan karantarwar Alƙur’ani da Sunna, da koyi da tarihinsa mai daraja, wajen ƙoƙarinsa da ijtihadinsa, da wurin zikirinsa da auradunsa, da wurin kyawawan ɗabi’unsa masu daraja, da wurin tawalu’unsa da sauƙin kansa tare da halittun Allah, da kuma wurin tsananin riƙon da yake yi wa Sunnar Annabi mai daraja, da kuma wurin kai- komonsa a koda yaushe wajen kawo gyara cikin hikima da azanci da kyakkyawan wa’azi, da bai wa ɗariƙarsa da manhajinsa na ilimi kariya, a kowane irin fage. Haka a ƙarfafa almajirai wajen neman aikin yi na samu, ta hanyoyin da Shari’a ta amince da su, saboda kowa ya samu ya dogara da kansa, cikin yanayi na kamewa da kuma tsafta, da yi wa addini hidima bakin- rai bakin- fama da duk abin da ya mallaka, kaman dai yanda al’amarin yake a farkon Musulunci.
4. Wayar da kawunan mutane game da haƙiƙanin Ɗariƙar Tinajiyya, da bayyana masu cewa babu komai a cikinta da ya wuce Istighfari da Salatin zaɓaɓɓen Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), da kuma kalma mai girma da dukansu suke cikin lazimin safe da na yamma, da wazifar da ake yi a kowace rana, da zikirin Juma’a wanda ake yi bayan sallar La’asar na ranar Juma’a. Wannan ne Ɗariƙar Tijaniyya a matsayinta na manhajin yi wa zukata tarbiyya, da tsarkake su, duk abubuwan da ba waɗannan ba, to suna cikin ilmomin Sufanci ne na Ahlus Sunna, da sauran ilmomi mabambanta. Haka ma Ɗariƙar Tijaniyya ɗariƙa ce ta malamai, babu ruwanta da siyasa ta kowace hanya. Tijaniyyawa suna da ‘yancin su shiga cikin siyasa a rayuwarsu ta yau da kullum a ƙasashe da garuruwansu, daidai da tsare- tsaren shugabanci a ƙasashensu, dukansu daidai da maslaharsu, a matsayinsu na ‘yan ƙasa da suke daidai da sauran ‘yan ƙasa, waɗanda suke da haƙƙoƙi da wajibai daidai wa daida, amma kuma ba tare da an shigar da sunan ɗariƙa a cikin siyasa ba.
5. Cigaba da wayar da kan Tijaniyawa a dukan garuruwa akan muhimmancin tsarkake zukata da tsaftace su da ɗaukaka su ta yanda za su fahimci manufofin Allah, tare kuma cikakken nesantar al’amurran duniya masu zuwa da gushewa, waɗanda suke haddasa ƙiyayya tsakanin abokai, ko suke dagula tsarkin ‘yan uwantaka na imani a tsakaninsu, ko waɗanda suka ƙara rarraba kawunan Musulmai saboda tarkacen duniya. Dole ne su ƙara himma wajen karanta littattafan Tazkiyya, da na ladubba, da tsarin rayuwa –ga su nan da yawa, cikinsu har da littafinmu “Annahjul Hamid..” da yake ƙunshe da tataccen abin da ake buƙata a wannan fagen- , da haka ne za su fahimci cewa lallai fatahi na haƙiƙa da ya kamata saliki ya yi alfahari da shi, muridi na gaske kuma ya yi farin ciki da shi, shi ne: sanin Allah, ba wai samun duniya da tarkacen cikinta ba, irinsu: matsayi, da dukiyoyi da sauransu da suka ratayu da duniya, suke kuma zama alaƙaƙai wajen tafiya zuwa ga Allah. Haka ma dole ne su san zamaninsu da kyau, saboda su zama cikin masu kawo gyara na haƙiƙa, waɗanda kuma suka cancanci su zama haka, masu tsoron Allah da kuma hangen nesa, da basira, da amana, da dabarun da dukan al’umma suke komawa zuwa gare su idan matsaloli sun kunno kai, saboda mayar da al’amurra zuwa ga yanda suke na asali. Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: (Su kuwa muminan da suka zo bayan "al-Muhãjirun" da "al-Ansãr" suna cewa ne: Ya Ubangijinmu ka gafarta mana zunubanmu, mu da 'yan uwanmu da suka riga mu yin imani, kada ka sanya ƙiyayyar waɗanda suka yi imani a cikin zukatanmu. Ya Ubangijinmu lallai kai mai yawan rangwame da rahama ne) [al- Hashri: 10], haka ma Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: (Ya ku waɗanda duniya ta ruɗe su, ku sani cewa lallai rayuwar duniya ba wata abu ba ce, ban da wasan da ba shi da amfani, da wargin da yake shagaltar da tunanin mutum ga barin abin da zai amfane shi, da kuma yin alfahari da kuke wa juna da gusassun dangantaka, da rududdugaggun ƙasusuwa, da kuma yin fankama da yawan dukiya da 'ya'ya, kwatankwacin wannan shi ne kamar ruwan sama da tsirran da ya fitar, wanda yake burge manoma, sannan ya ci gaba da girma har ya kai ƙarshensa, bayan haka kuma sai ka ganshi ya zama fatsi-fatsi ya fara bushewa, daga nan kuma sai ya zama karmami ya fara kakkaryewa a murmushe shi, ta yadda babu wani abu mai amfani da zai yi saura a tare da shi, a lahira kuma ga azaba mai tsanani ga duk wanda ya fifita duniya, ya kuma ci ta ba tare da haƙƙi ba, da kuma gafara daga Allah ga wanda duk ya fifita lahirarsa akan duniyarsa. Duniya ba komai ba ce ban da tarkacen da yake ruɗi, wanda ba shi da tabbas ga duk wanda ya aminta da ita, bai sanyata ta zamo masa kadarko na wucewa zuwa lahira ba) [al- Hadid: 20].
6. Muna kira ga ɗaukacin almajirai, da masoya da suka amfana da ilmomi, da albarkatu, da karantarwa, da shiryatarwar mai girma Sheikhul Islam, wa sa’adatul Anam Maulana Sheikh Ibrahim Niass (Allah ya ƙara yarda da shi), musamman mambobin Ƙungiyar Ansaruddeen- Tijaniyya, da ma wasunsu cikin almajirai da masoya a duk inda suke, da kada su yi wata- wata wajen bai wa Shehu (Allah ya ƙara yarda da shi) kariya, Sheikh ɗin da ya gudanar da gaba ɗayan rayuwarsa wajen kira zuwa ga addinin Musulunci a cikin dukan maƙamansa guda uku, ya rayu a matsayinsa na mujaddadi na haƙiƙa a cikin wannan addinin, ba wai kawai a fagen ruhi ba, a’a, har da dukan fagage. Lallai (Allah ya ƙara yarda da shi) ya kasance cikakken jigo ne mai kawo gyara a rayuwar zamantakewa da ba a yi irinsa ba, sannan kuma shi ɗin jagora ne a wajen masu tunani na Musulunci, shugaba ne mai girma a fagen jinƙai da mutuntaka, a gefe ɗaya kuma, tafiyayye a fagen soyayyar Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), abin da ya sanya ya yi zarra a zamaninsa wajen yi wa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) biyayya a wajen maganganu, da ayyuka, da halaye, ba shi da wani aiki banda kiran mutane zuwa ga Allah Mai girma da ɗaukaka, cikin ilimi da basira kaman yanda yake faɗi cewa: “Su kuwa al’umma, manufa ta akansu ita ce: in kora su zuwa ga halarar Allah al- Barru, ar- Rahimu Ubangijinmu”, shi ne kuma yake cewa: “Idan fiyayyen cikin mutane ya cira ina nan zan bi bayansa, idan kuma ya sauka a wani wuri, to kowace irin tafiya nisa take yi mini”.
Daga nan ne za mu gane cewa: lallai wajibi ne akanmu duka mu kuɓutar da Sheikh (Allah ya ƙara yarda da shi) daga dukan bidi’o’i da saɓa wa shari’a, da ɓata, da soki- burutsu, kai har ma da aikata saɓon Allah, da aikata abubuwan da aka haramta, waɗanda suka bayyana a ‘yan baya- bayan nan da sunaye mabambanta irinsu: haƙiƙa da sauransu, waɗanda ake yunƙurin yarfa su a manhajin Maulana Sheikhul Islam, alhalin ba shi ba su.
7. Muna ƙara kwaɗaitar da ɗaukacin al’umma wajen girmama alamomin da suke nuni zuwa ga Allah, waɗanda ya bayar da umurnin a girmama, haka ma da girma waɗanda suke da dangantaka da Allah Maɗaukakin Sarki, da yi masu ladabi, musammam Sharifai ‘yan gidan Manzon Allah masu tsarki, da dukan waliyyai da salihai, da malaman Musulunci a duk inda suke ba tare da bambanci ba, saboda aiki da maganar Allah Maɗaukakin Sarki da yake cewa: (Wannan kenan, duk wanda yake girmama alamomin da suke nuni zuwa ga Allah, to kuwa lallai hakan da yake yi alama ne na tsoron Allah da yake cikin zukata) [al- Hajji: 32], haka ma Allah mai girma yana cewa: (Wannan ne abin da Allah yake yi wa bayinsa da suka yi imani da shi, suka kuma aikata ayyuka na gari albishir da shi. Ya RasulalLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), ka ce: Ni fa ba na tambayarku wani lada akan abin da nake isar maku, banda soyayyar makusanta ne, duk wanda ya aikata abu mai kyau za mu yi masa ƙari da abu mai kyau, lallai Allah mai yawan gafara da godiya ne) [as- shura: 23], haka ma mai girma da ɗaukaka yana cewa: (Ya ku waɗanda kuka bayar da gaskiya da Allah da Manzonsa, idan an neme ku buɗa wa junanku a wuraren tãruwãr jama'a, to ku buɗa, kú ma Allah zai buɗa maku, idan an nemi ku tashi daga wuraren tarukanku, to ku tashi, Allah yana ɗaukaka darajar muminai masu tsarkake shi a wurin bauta, da waɗanda aka ba su ilimi, duka Allah yana ɗaukaka darajarsu, Allah yana da cikakkiyar masaniya akan abin da kuke aikatawa) [al- Mujadala: 11], a Hadisi mai girma kuma an ruwaito cewa: (Wanda bai girmama babba ba, bai kuma tausaya wa ƙarami ba, bai kuma bayar da umurnin aikata abubuwa masu kyau ba, bai kuma hana aikata munanan ayyuka ba, to ba shi a cikinmu) [Ahmad, al- Bazzar ya ruwaito irinsa, da Ɗabaraniy a taƙaice, ya yi ƙari da: (Bai kuma san haƙƙinmu ba)].
8. Wajibi ne a faɗakar game da hatsarin naɗa kai a matsayin shaihuntaka da da’awar haka, da kuma kutsawa cikin muƙaman keɓaɓɓun bayin Allah da kowace irin sura na yaudarar al’umma, saboda a tara tarkacen duniya, da kayan ƙawan cikinta masu ƙarewa, abin baƙin ciki wannan ya yaɗu sosai a wannan zamanin namu, Allah Maɗaukakin Sarki muke roƙo ya kiyaye mu. Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: (Ya ku waɗanda kuka yi imani, ku ji tsoron Allah, ku kuma kasance tare da masu gaskiya) [at- Tauba: 119], Allah ya ƙara rahama ga wanda yake cewa: “Akwai masu da’awar shaihuntaka da yawa ta hanyar matsayi da iko, amma ƙirazansu suna ƙunshe da munana zukata. Akwai mutane da yawa da suke da’awar shaihuntaka ta hanyar sanya tsofaffin tufafi, amma manufarsu ita ce: jawo wa kawunansu zinare da azurfa. Akwai mutane masu yawa da suke da’awar shaihuntaka ta hanyar nuna wauta, alhalin a haƙiƙanin al’amarin babu wata wauta a tare da shi”.
Lallai malamai na Allah, da waliyyai, da salihan bayi suna da sifofin da ake bambance su da saura, ta hanyar gaskiyarsu da yi domin Allahnsu, babban alama da take bambance su ita ce: tsananin riƙon da suke yi da littafin Allah mabuwayi, da Sunnar Annabi mai daraja, wani daga cikinsu yana cewa: “Kawai ka auna su da ma’aunin gaskiya, da riƙon amana, da kiyaye iyakokin Allah, da riƙo da addini, da bin tsararrun ayoyin da suka zo a cikin Alƙur’ani, da bin Sunnar Annabi ba tare da inda- inda ba, lallai waɗannan abubuwa ne da suke yi wa shaiɗan da ‘yan tawagarsa cikin mutane da aljannu wahala”. Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: (Kada ku sayar da alƙawarin da kuka yi da Allah da ‘yan kuɗi ƙanƙani, ku sani abin da yake wurin Allah ya fi zama alhairi, in dai kun san haka) [an- Nahli: 95], haka ma yana cewa: (Ku gasgata Alƙur’ãni mai girma wanda na saukar da shi, yana mai tabbatar da abin da yake wurinku na littafi, da kaɗaita Allah da bautarsa, da kuma adalci tsakanin mutane, kada ku yi gaggawar musanta Alƙur’ãni, balle ku zamanto farkon waɗanda za su kafirce masa a lokacin da kamata ya yi ku zamanto farkon waɗanda za su yi imani da shi, kada ku bar ayoyin Allah ku ɗauki wani makwafi kaɗan na karikitan duniya da za su gushe, ku ji tsorona ni kaɗai, ku bi hanyata, ku kawar da kai ga barin ɓata) [al- Baƙra: 41].
9. Muna kiran kawunanmu baki ɗaya mu koma zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki, mu cigaba da addu’a a ɓoye, da a fili, Allah Maɗaukakin Sarki ya datar da shugabanninmu na Najeriya a dukan matakai, musamman mai girma shugaban ƙasa/ Muhammadu Buhari –Allah ya kiyaye shi- a dukan ƙoƙarin da suke yi ƙarƙashin jagorancinsa wajen kawo gyara a ƙasa da rayuwar al’umma a dukan fagagen tsaro da na tattalin arziki, ta yanda aminci, da zaman lafiya za su karaɗe rayukansu da abubuwan da suka mallaka, a samu kwanciyar hankali a rayuwar zamantakewa na garuruwansu. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya yaye mana wannan annobar da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa ta korona da dukan matakanta, ya kuma nesanta ƙasarmu da ma sauran ƙasashe daga dukan bala’o’i da fitintunu, da girgizar ƙasa da matsaloli na zahiri da na baɗini. Haka ma mu yi wa dukan shugabannin Musulmai addu’a ta kariya da dacewa a ƙoƙarin da suke yi ba dare ba rana wajen haɗa kan al’ummar Musulmai da aiki tuƙuru wajen cigabanta ta yanda za ta hau matsayin da ya dace da ita a cikin al’ummomi, ta zama jagora, mai fuskantarwa da kuma tsamar da ɗaukacin bil’adama daga hatsarurruka da suke barazanar ƙarar da al’umma a wannan zamanin, da ma cigaban duk wata al’umma da suke son soyayya da zaman lafiya.
10. Haka ma za mu yi amfani da wannan damar, mu gabatar da cikakkiyar godiya, da yabawa ga dukan waɗanda suka bayar da gudummuwa wajen nasarar wannan babban taro, gudummuwa na kuɗi, da na aiki, da na ƙarfafa gwiwa, ko da addu’o’i, duka saboda girmama Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), da ƙara bayyana Sunnarsa, da taimakonta, da kuma ba ta kariya, da ambaton sifofi da kyawawan ɗabi’unsa masu girma, ta yanda ɗaukacin bil’adama za su yi koyi da shi, ganin cewa an aiko shi ne (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) domin ya zama rahama a gare su. Allah mai girma yana cewa: (Lallai a cikin Attaura –baya ga Alƙur’ani- mun tabbatar da cewa ita wannan ƙasar bayina salihai ne za su gaje ta. Lallai a cikin haka akwai isar da saƙo ga mutanen da suke bauta wa Allah. Ba mu aiko ka ba sai domin ka zama jinƙai da rahama ga talikai) [al- Anbiya’i: 105 -107].
Godiya ta musamman zuwa ga mai girma gwamna Alhaji Yahya Adoza Bello –Allah ya kiyaye shi- gwamnan jahar Kogi, wanda jaharsa ce ta amshi baƙwancin wannan babban taro mai girma, shi kuma ya gabatar da duk abin da ya kamata mumini ya gabatar saboda Allah, domin soyayyarsa da Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam). Haka ma godiya ta musamman ga dukan mataimakan gwamna a dukan fagage, da masu girma da daraja, da martaba, shugabanni, da manyan ƙasa da sarakunan gargajiya, da halifofi cikin jikokin Maulana Abul Abbas, Sheikh Ahmad Bn Muhammad al- Tijaniy (Allah ya ƙara yarda da shi), haka ma da halifofi cikin ‘ya’ya da jikokin Maulana Sheikhul Islam wa sa’adatul Anan Sheikh Ibrahim Niass (Allah ya ƙara yarda da shi). Haka ma godiya ta musamman zuwa ga mai martaba Sarki, kuma Halifa Muhammadu Sunusi II, da malamai, da muƙaddamai waxanda hotunansu ya ƙawata katin tsare- tsaren wannan taron, da ma wasunsu cikin ɗaukacin Musulmai da suka niƙi- gari, suka ɗauki dukan wahalhalun tafiya domin halartar wannan babban taro mai girma, Allah ya kiyaye su gaba ɗaya, ya kuma saka masu da mafificin alhairi.
11. Za mu ƙarƙare da abin da muka fara da shi na yin nasiha saboda Allah, da wasicin da Allah ya yi wa Annabawa da Manzanni a baya, Allah mai girma yana cewa: (Lallai mun yi wasici ga waɗanda aka ba su littafi kafinku, da ma ku akan ku ji tsoron Allah..) [an- Nisa’i: 131], haka ma yana cewa: (Lallai ƙofar wuta a buɓe take, idan har ba ku ji tsoron Allah ba, ya ku waɗanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah, tsoron da ya kamata, ta hanyar aikata abin da aka bayar da umurnin a aikata, da nesantar abin da aka hana, ku dawwama cikin Musulunci har zuwa lokacin da za ku haɗu da Allah. Ku yi riƙo da addinin Allah gaba ɗayanku a tare, kada ku kuskura ku aikata abin da zai kai ku zuwa ga rarrabuwar kawuna, ku tuna da ni'imar da Allah Maɗaukakin Sarki ya yi maku, a da lokacin jahiliyya kuna adawa da juna, sai ya haɗa zukatan ku ta hanyar addinin Musulunci, kuka zamo masu soyayyar juna; saboda kafircin ku da rabuwar kawunan ku kun zamo kuna gefen ramin wuta ne, sai addinin Musulunci ya tseratar da ku, da ire-iren wannan bayani mai ban sha'awa ne a koda yaushe Allah Mai girma yake bayyana maku hanyoyin alhairi; domin ku dawwama akan shiriya. Kuma lallai cikakkiyar hanya guda ɗaya da za ta haɗa ku akan gaskiya, ƙarƙashin inuwar littafin Allah da sunnar Manzon Allah ita ce: ku kasance al'umma ɗaya da za ta riƙa kira zuwa ga dukan abin da zai zamo gyara ne na duniya da lahira, kuna umurni da aikata ayyukan biyayya, da hani ga aikata saɓo, lallai waɗanda halin su ya zamo haka su ne masu cikakken babban rabo. Kada nuna-halin-ko-in-kula ga umurni da ayyukan alhairi, da hani kan munanan ayyuka, da za su haɗa ku akan alhairi da addinin gaskiya, ya sanya ku zamo kamar waɗanda suka yi biris da umurni da aikata ayyukan alhairi, da hani kan munanan ayyuka, a sakamakon haka sai suka rarrabu ƙungiya-ƙungiya, suka yi saɓani a cikin addinin su, bayan bayyanannun hujjoji da suke bayyana gaskiya sun zo masu, lallai waɗannan da suka rarrabu suka kuma yi saɓani suna da azaba mai girma) [Ali Imran: 102 – 105]. Haka ma yana cewa: (Ya Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa alihi wa sallam) ka ce masu: ku yi aiki kawai, da sannu Allah da Manzonsa da sauran muminai za su ga ayyukanku, kuma da sannu za a mayar da ku zuwa ga masanin abin da yake a ɓoye da wanda yake a fili, shi kuma ya ba ku labarin abubuwan da kuke aikatawa) [at- Tauba: 105], haka ma yana cewa: (Ya ku iyalan Annabi Dawud, ku gabatar da godiya a aikace, kaɗan ne daga cikin bayina suke yawan godewa) Saba: 13].
Ina yi maku cikakkiyar fatan alhairi a dukan lokutanku, Allah ya datar da mu zuwa ga abubuwan da yake so ya kuma yarda da su, ya kuma haskaka mana madaidaiciyar hanya, ya amshi ayyukanmu, ya sanya su zama dominsa shi kaɗai, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki, albarkacin mai babban matsayin a wurinsa, wanda muke murna da shi, wanda shi ne mai babban ceto, shugabanmu, macecinmu, jagoranmu mai babban daraja Shugabanmu Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya amsa mana addu’o’inmu, lallai shi mai yawan ji da sani ne, kada ya mayar da mu ba tare da rabo ba, lallai shi mai yawan ji ne da kuma yake kusa, mai kuma yawan amsar roƙon bayi.
Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai.
Wassalamu alaikum warahmatulLahi ta’ala wabarakatuhu
Allah ya maimaita mana.
Masoyinku saboda Allah, mai fatan samun luɗifin Ubangijinsa, hadimin Sunnar Annabi, kuma mabuƙaci a wurin Allah Maɗaukakin Sarki:
Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhussainiy CON
Shugaban kwamitin bayar da fatawa a majalisar ƙoli ta addinin Musulunci a Najeriya
Shugaban Cibiyar Muhammadus Sadis ta malaman Afrika, reshen Najeriya
Mamba a Majalisar Dattijan Musulmai.
Abuja: Alhamis 3 ga watan Jimada al- Akhir, 1443
6 ga watan Junairu, 2022
Abubakar Muhammad Al-amin - shekara 2 ago
Bukatar bayanan sirri
sai kashiga chiki saboda bada bayani.
Shiga chiki