labarai

Ziyarar neman shawarwari daga Komitin harkar tsangayoyi Ta Jahar Yobe

August 08, 2020 admin الأخبار العامة News
News photo

Komitin ta Samu kafuwa ne daga magatakardan jahar Alhaji Malum Wali 29 ha watan june 2020 sabi da inganta tsarin karatun tsangayoyin,sabi da shi gomnan jahar ya tsaya tsayin daka chewa bazai hana tsarin karatun ba kuma ba zai mai da wa' yenda ba yen jahar garuruwansu.Shugaban komitin wanda yake shine komishinan makarantun sekandare Dr Muhammad sani idris shi ya shugabanchi komitin ya zuwa masaukin na shehi a babban birnin tarayyar Nijeriya sabi da neman shawararsa,sheik shariff ibrahim saleh ya yaba matuka wa Gomnan jahar mai mala Buni sabo da yadda yabada kulawa ga tsarin a jahar,kuma shehin ya bada goyon baya matuka ga yanayin tsarin.

Chikin mambobin komitin sun hada da:- ustaz  Baba gana mamalam kyeri wanda yake mai bada shawara ne ga Gomnan jahan kan abinda ya shafi addini,da professor musa alebe wanda yake shugaban jahar na SUBEB,da Malam Muhammad baba Goni Gujba,da malam Abba lawan,da malan yahuza hamza Gaidam da kuma sauran malamai.

Babu wassu bayanai yanzu.
Bukatar bayanan sirri

sai kashiga chiki saboda bada bayani.

Shiga chiki