Takaitacchunn qasidu
Jawabin Shekh shariff Ibrahim saleh shugaban majalasin fatawa Na Nigeria da yayiwa malaman Africa kan Kafa kungiyar sarki Muhammad na shida Na malaman Africa da za ayi
Yayi jawabinne ne a madadin malaman Africa kan kafa kungiya malamn African
a babban birnin Casablanca na kasar Morocco 26 ga watan Ramadana shekara
1436 H wanda yayi daidai da 13 ha watan
yuliyo shekara 2015
Da sunan Allah mai Rahama ma jin kai
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin dukkanin talikai,salatin Allah kuma su
tabbata da Manzon Allah fiyayyen dukkanin Annabawa,da malayensa da sahabbansa
wanda suke garkuwa daga makiya masu kuma kira ga hanya madaidaichiya.
Bayan Haka:
Shugab Saraki muhammad na shida shugaba ga muminai garkuwa da addinin
Allah.Allah ya kara maka nasara kuma kare maka mulkinka.Ameeen
Allah subhanahu wa ta ta'ala yana chewa a littafinsa mai tsarki (ya ku
wanda kukayi imani ku amsawa kirana Allah da Annabinsa idan ya kiraku ga abu da
zai anfaneku ..)
Lalle kuwa aluammar musulumai tin farkon wannan addini Allah yasa za su
gamu da bale'i iri iri wanda Allah kuma yasa za su iya jurewa kuma su ketaresu
saboda riko da sukeyi da alquraani da kuma sunnan Annabinta mai karamchi da
kuma bin umrnin magabata,shuwagabanni masu adalchi da kuma malamai masu tsarin
Allah masu aiki,har amanar wannan addini ta iso mana a sawwake a wannan zamani
a hannu malami da suka chika alkawari da suka dauka wa Allah,ba su Chaza ba ba
sukuma sawya wani abu ba,hakan yasa muka sami addinin yadda yake daga wajen
Manzon Allah SAW kuma yanda ya karbosa daga Allah.
Wani lokachin Allah yana yiwa bayinsa ajiyar abubuwa da suke bukata har zuwa lokachi da yakamata, mu kuwa lalle
muna wani zamani da yake chika da rabe raben kai da fama da masu tsatssauran
ra'ayi sai kwasam mukaji wannan kira na mai girma sarki sabi da kafa wannan
kungiya,wanda aka rada mata sunnan kungiyar sarki muhammad na shida na malaman
Africa. A wannan dare mai albarka a chikin wanna wata mai girma,a kuma wannan
waje mai tsarki,sabi da hadin kai tsakanin malaman kasar Morocco da sauran
malaman Africa sabida kira ga addinin musulinchi sabi da koyi da magabatanmmu
wa'yenda suka koyar da musulinchi a yanda yake
da kewunsa da tsabtarsa na kyewawan dabi'u wanda suke faantawa dukkan
dan adam rai a daukakin fadin Africa,kuma ne wanda yake da muhimmanchi da muyi
nuni da shi chewa alaqar kasar Morocco da kasashen Africa alaqa ce ta addini
kamin tazama ko wata irin alaqa sabi da abinda yake hada kasar da sauran
kasashe kaman alaqa ta Aqida da mazhaba da kuma manhaja ta sufanchi,sabida
dukkammu masu bin asha'riyya ne kuma dukkammu mazhabar malik muke bi da
manhajar junaid ta sufanchi,sabi da haka muke ganin chewa wannan kira ne da
yazo lokachin da yadache,wanda lalle mun kasa yin hakan a da duk da bukatarmu
ga hakan,sai gashi ya gudana daga wajen shi mai girma sarki wanda yake ba abun
Mamaki bane hakan.
Sabi da haka muna numa amsawarmu ga wannan kungiya da sunan dukkanin
malamai da suke nan da kuma wanda basu sami Halarta ba sabi da wassu dalilai,
kuma muna nuna goyon bayyammu ne sabi da wannan yana daga kira da annabi yayi
hakazalika Allah ya umurchemu da muyi,Allah ya kiramu da muhada kai kuma mubi
magabata,inda yache (ya ku wanda kukayi imani kuyi biyayya wa Allah da
Annabinsa da kuma majibinta lamarinku)
A karshe kuma muna
addua'a da Allah ya kiyaueku da abinda yakiyaye littafinsa mai tsarki da shi ya
kuma baku nisan kwana da nasara kuma ya kiyaye dukkan wanda suke wannan
masarauta,muna kuma Rokon Allah da yabawa wannan kungiya nasara karkashin
kulawanku ya kuma Bamu daman aiki tsakani da Allah.Allah kuma ya bawa wannan
kasa chi gaba wajen zaman lafiya .assalamu Alaikum wa warahmatullahi wa
Barakatuh.