Takaitacchunn qasidu

Musulinchi a Africa

admin August 23, 2020 عامة

Africa ta kasanche da sanin musulinchi tin farko farkonsa,yana daga chikin abubuwa da akafi so sabi sa samun chigaba,duk da haka wassu suna ganin kaman musulinchi abu sabo ne a Africa,shi yasa za kasamu chewa musulinchi baya samun kula yadda ya kamata a nahiyaryar.

Mahir Abdullahi:yen masu kallonmu,Sallama ta Allah a gareku,muna maraba da ku a wannan sabon shiri na (sharia ds rayuwa)

Musulinchi sohon abu a Nigeria dai dai da da farkon zuwan da'awan Annabi Muhammadu SAW kaman yadda takardun sira suke Chike da labarin yadda Annabi SAW ya yi tinanin chewa ba waje da za a iya kare musulinchi a chiki kaman wajen sarki Najashi a wanchan lokachi,duk da abkuwan wannan lamari wassu har yanzu suna ganin chewa musulinchi abu ne sabo a nahiyar kuma mutane tsiraru ne ke bin musulinchi.

Sabi da magana kan musulinchi a Africa bako na a wannan dare shine sheikh Ibrahim saleh Al-husaini mufti na kasar Nigeria ha ilaw shugaban majalasin malamai a kasar.

Sheikh Ibrahim saleh lale marhaban da kai a tashar Aljazeera a shirin sharia da rayuwa .

Ibrahim saleh:yauwwa sannunku

Mahir Abdullahi:me yasa kullum ake tinanin kaman addinin musulinchi abu ne sabo a wajenku duk da yake musulinchin abune da yade a nahiyar tin farkonsa,kuma ku kuka basa mafaka,a lokachin da ake ta bi biyansa d makirchi ?

Ibrahim saleh Alhussaini:Bismillahirrahmanirrahim Alhamdulillah Rabbil-aalamim,salatin Allah ta tabbata ga Annabi Muhammadu SAW mafifichi chikin Annabawa da aalayansa matsarkaku.lalla ko shakka babu chewa nahiyar Africa itache ta farko wajen baiwa musulinchi mafaka,kuma itache waje na farko da sabbai sukaje hijira,a kasar Habasha,wannan kuwa ya kasanche ne a farkon watan Rajab shekara ta biyar bayan bayyyanan Manzon Allah SAW wata shida  bayan bayyana da'awan musulinchi Annabi SAW Allah yabaiwa manzonsa izini da yabaiwa sahabbansa izin da suje waje da za suyi addininsu ba tare da andamesu ba ko antaba dukiyarsu ba,su dauku abu da za su iya dauka,sukaje habasha sabi da sarkinta baya yarda a chuchi ko a chan,wassu daga sabbai ko sunyi hijira cah basu koma ba sai da sugaji chewa yen makka sun musulunta, sai dai kash sun koma makkan amma maganan ba gaskiya bache sai suka koma izuwa Habasha,a wannan komawan kuwa sun sami Karin adadi sun kai tamanin,chikinsu kuwa da sayyidna Jafar bin Abi Talib,sun kasanche a Habasha kuwa shekara sha shida,a Wannan shekaru dewa chikin yen yankin sun musulunta,sai dai abin mamaki babu chikin abubuwa da aka adana chikin larabchi da yake magana kan wannan Hijiran.

Mahir Abdullahi (katsewa)shin Wannan itache kawai hanya da musulinchi yashigo nahiyar Africa ta shi,ko dai da kwai wassu hanyoyin?kuma idan har sun koma me suka bari bayansu,kuma wanne shabbai ne ?Ibrahim saleh Alhussain:kwarai kuwa sun bar sun bar musulinchi a nahiyar da al-umma musuluma,kuma lalle tabbatacchen labari ya nuna chewa sarki Najashi ya musulunta,dalili kuwa shine,Annabi SAW ya jagwarchi yimar sallan Jana'iza,kuma bazzayyu ache duk wannan lokachi da dama da srkinnan ya baiwa sahabbai sukasa tasiri akan mutanen nahiyar,kaman yaddda najashi ya nuna yardassa da aqidansu da chewa bata da babbanchi da abinda Annabwa sukazo da shi ba.

Mahir Abdullahi:Abdullahi marubuta tarihi na larabwa sun chuchi tarihin nahiyar Africa

Ibrahim saleh Alhussaini:a'a

Mahir Abdullahi:Abdullahi bawani bayani dalla-dalla kan abunda yafaru a nahiyar chikin wa'yennan shekaru sha shida,kuma yadda addinin musulinchi ya yadu a nahiyar,ko akwai wani bayani akai?

Ibrahim saleh Alhussaini:duba da yadda tarihin nahiyar Africa da kuma yadda musulinchi ya wanzu a nahiyar lalle yana da alaqa da wannan hijira izuwa Habasha,sabi da haka za kaga yawanchin mazauna nahiyar yen hijira ko sunyi hijiran daga Habsha ko da (alwa)daga Kasar sudan ko daga (danqalat Alajuz)ko (danqalatul qadima)ko daga wajen yen Nuba ko daga Sa'id Misra,duk wa'yennan baza muche sun dade da  shigowa nahiyar ba amma dai chikinsu da kwai sannan sun sami musulinchi ne daga wa'yennan sahabbai da sukayi hijirannan ne.

Mahir Abdullahi:Abdullahi sabo da Tinatarwa za ku iya bibiyanmu ta hanyar yanar gizo na Aljazeera wato www.aljazeera.net basu bi kowa ta akwatin television ga numbobin na waya,mabudin kasar qadar 9744888873 ga kuma wani numban 4888874 da numba na faks 48885999

Malam abi da mukafi Sani kan musulinchi a nahiyar Africa shine na nahira gabashi wato na larabwa,kaman su bude misra,sai kuma sai kuma na uqba bin nafi wanda ya so kewa nahiyar sai dai kaman tin wanna  lokachin tarihinta bai bayyana ba,ba muji wani magana akan nahiyar ba?

Ibrahim saleh Alhussaini:haqiqa Uqba bin Nafi ya shiga nahiyar Africa inda ya shigo Misra da Libiya ya kuma iso wajen da ake kira Fizzan,ya kyetara izuwa Kawar,Kawar kuwa wajene da aka sansa da gishiri a babban Sahara da take gabashin Kanin Borno da mukasani a yau.

Mahir Abdullahi:A Nigeria kenan

Ibrahim saleh Alhussaini:Alhussaini yana jamhuriyan chadi bayan rabe-rabe na mulkin mallaka ta kasanche dukkanin wajen nan a sansa da Kanim Borno ne,shi kuwa Uqba bin nafi ya ketare Fizzan da kawar har izuwa kudanchin nahiyar,ya kasanche wata shida achan,ya so ya kai har karshen sharan izuwa tabkin chadi,amma sabi da wahalan ketra ruwan da kuma irin dajin da yake wajen ya sassauta wa abokansa ya koma.daga wanchan lokachin dayewa a nahiyar suka karbi musulinchi a wajen Uqba bin nafi,wannan shine lokachi da musulinchi ya shigo nahiyar a shekara 56 ta hijira,a lokachin ne musulinchi ya shigo nahiyar kanim,wanda kudanchinta ya kasanche a chadi yammachinta kuwa shine inda akasansa da Borno a yau wanda ya kasanche a Nigeria yanzu. Musulinchi lalle ya shigo wannan nahiya ta hanyoyi dayewa wanda kuma dukkansu suna da Sila da juna.

Mahir Abdullahi.:(ya katse)amma ba asan kamin afuwa wa'yennan hanyoyi basu shahara ba a chan,shin sunyi wani tasiri?

Ibrahim saleh Alhussaini:musulinchi ya yadu a nahiyar ne musamman nahiyar kudanchin shara da tsakiyar nahiyar,ya yadu ne ba tare da yake yake ba,ya yadu ne ta hanyan masu zuwa yayon bude ido,daga bayin Allah da kuma masu tsoron Allah,sun kasanche suna yawo wajeje deyawa dauka da abubuwan alwala,da Alquraani,sunyi tasiri ne kan mutane da halayensu na kirki,da kuma yadda sune kamata halaye na musulinchi na kwarai,wannan yasa dayewa chikin attajirai larabawa da suka iso wannan wajeje kamasu kano,Katina,ta tsohon hanyan Sudan(sanar)da kuma Habasha,ta hanyoyinnan suka iso.

Da kwai wassu hanyoyi chikinsu babban shara ta Morocco ko kuma wanda aka sansa yanzu da shara ta Jazair (sidi Almasa) har izuwa (awdagsht) zuwa Gana ta da,da kuma Sinegal,Mali,har izuwa Borno da masarautun Hausa.

Mahir Abdullahi:mutanen nan da kamusu suna da attajirai da dukufa kan ibada anfi saninsu chikin takardun tarihi da sufaye

Sheikh Ibrahim saleh Alhussaini :eh

Mahir Abdullahi:dabia da aka fi sani kuwa daga wajen Africa shin wa'yennan sufaye sun taka rawa wajen yada addinin da darikunsu na sufaye ne ko kuwa kawai alokachin su ansansu ne da masu yawan bauta da zuhudu?

Ibrahim saleh Alhussaini: a'a lalle kuwa a lokachin sun shigo ne nahiyar kuma sun ahahara ne da yawan bauta bayannan darikunsu suka bayyana kuma sun taka rawa kwarai wajen yada addinin Musulinchi a lokchinda ake fama da mulkin mallakan turawa,shi yasa zakaga yawanchin mazauna africa ma'abota karatun alqura'ani ne da kuma kira izuwa zuhudu musamman idan ka karanta ayannan da take chewa (kusani chewa duniya wasa ne da kuma ado da Jiji da kai tsakaninku..)ayoyi dayawa a alqura'ani suna kira ne da anisanta da wasa a duniya kuma suna kira izuwa zuhudu. Musulumai na farko a Africa karatun alqura'ani ginshiki ne a rayuwansu kuma yana zukatansu shi yasa yawanchinsu sunzamo mabiya ga sufaye....sufanchinsu kuwa yana da alaqa da koyar da alquraani da koyar da fiqhu,a lokachin kuwa masu kira zuwa addini da alkalai da masu bada fatawa duk sune,shi yasa akasami addini a Africa ba tare da yaki ba,ansamesa ne ta hanyar yada al'adu na kirki,da gaskiya tare da Allah da bayin Allah.

Mahir Abdullahi:mu da muke nahiyar a gabashin kasashen larabawa munsan tarihin daulan abbasiyawa da daulan umawiyya da khalifanchi na usmaniyya,Africa ta hadu da wa'yennan irin khilafanchi wanda suke da daukaka kaman haka amma ba asan da su ba ,kadanne suka ji labarin daulan fulani,da Kanim Borno,da khilafanchi da Mali,da ta Gana,me yasa bakwa rubuta tarihinku,me yasa bakuyi haka ba dan muji tarihin abbasiyyanku da umawiyyanku ?

Ibrahim saleh Alhussaini:kaman yadda nache maka Africa ta damu ne farko da rubuta addininta da abubuwa na gaske da suka kasanche addinin musulinchi, kaman rubuta alqura'ani da fiqhu,sun dauki abubuwannan da muhimmanchi,dukkanin kartuttuka na alqura'ani suka iso ko ina,basu tsaya kawai kan karatun riwayar warsh ba,ko qaloon,kaman riwayar abu amr anayinta a wassu jahohin sudan,Amma a aqida kuwa dukkanin yammachi da ka kudanchinta suna bin Ahlu-ssunna wal-jama'a ne ta hanyan asha'ariyya da maturidiyya,da kwai kuwa masu ijtihadi chikin wanda suke kari kan wa'yennan kuma su zabi wassu abubuwa suyi rubuche-rubuche akai,da kwai wanda sukayi rubutun tarihi a nahiyar har da kwai wanda yake chewa:masarautu na musulumchi hudu ne ,sai ya anbachi masarautan abbasiyya a bagadaza,da Masarautu na kasar misra,da masarautan kanim Borno,da masarautan kasar Mali,Wato wannan takarda ya dache ya che manyan biranen kasashen musulinchi hudu ne :Bagadaza,qahira,Kanim Borno da Tumbuktu.da su akasan musulinchi,har marubuchi sa'adi yache a takardansa tarihin Sudan:Tumbuktu itache birnin musulinchi kadai da ba ataba bautawa wanin Allah a chikinta  ba,ta kuma dawwama ne shekara 400 idan kuwa ka duba litattafan tarihi na kasar na mawallafa kamansu Ahmad Babah attumbukti da sauransu za kasan chewa malamansu sunkai malamai na kwarai a dukkanin fadin kasashen musulinchi a wanchan lokachi,a wajen mu mun daukesa hujja a mazhaba ta malikiyya,shi yasa ni make chewa tarihin nahiyar a rubuche yake,kamsu takardan tarihi na (fattash)da tarihin sudan na imam assa'adi,da takardan ima m Ahmad furto,da tarihin Idris da yake-yakensa da dai takardu masu yawa.

Mahir Abdullahi:amma a manhaja ta Makarantu na kuma zabi masarautun saboda su suke gina samar da mutane banga wata nami'a ta larabwa ba da take koyar da tarihin musulinchi a nahiyar Africa ba

Ibrahim saleh Alhussaini:Africa wannan..

Mahir Abdullahi: idan munche kasashe da khilafanchi na musulinchi toh muna nufin Dimashq ne da Bagadaza ...

Ibrahim saleh Alhussaini: wannan haka ne kuma gazawa ne..Kaman yadda yafaru a wajen koyarwa na tarihin Africa da malamanta,haka akasami gazawa wajen rubuta tarihin lokachinda sahabbai suke nahiyar da tasiri da suka yi a wajen da suka rayu chiki wajen shekaru sha shida,kaga toh wannan ba laifin yen Africa kadai bane dan basu Gaza ba wajen rubutun tarihinsu kaman sheik da fodio wanda yake daya ne daga chikin jigogin malaman musulinchi kuma mujtahidi a wancha  lokachin daga chikin waye'nda sukayi tajdidi,wanda ta kafa daulan fulani,Kawarai yayi kokari yayi rubutu shida dan uwansa Abdullahi da Dansa muhammad Bello,sunyi rubuche-rubuche da suka kai darurruka chikinsu akwai takardan tafsiri (diya'uttaweel) Kashi hudu,bugu na farko an bugashi a misra,a zamanin sheikh Shaltut lokachin Ahmad sardauna

Mahir Abdullahi: shi shugaban kasa ne

Ibrahim saleh Alhussaini: ahmad Bello sardauna (shugaban ministochin Nigeria ne)da kwai rubuche-rubuche masu muhimmanchi da suka rubuta

Mahir Abdullahi: ka ambachi yake yake wato lokachin da khilafanchi ne kudu ya rushe da kwai wanda sukeyi kokarin maido da ita kaman mayakan suriya da na Sudan duk da yake ba a rubuta shi ba yana sukatan musulumai a Africa,shin yayi tasiri a kasashen musulumai

Ibrahim saleh Alhussaini: duk wa'yennan sun kasanche ne a Karni na sha takwas  izuwa tsakiyar sha tara a wannan lokachin kuwa Ansami manyan malamai na addinin musulinchi a Tumbuktu sabo da Tumbuktu ta Samu a shekara ta 610 na hijira ba a ruguzata ba sai a shekara ta 1002 ko 1000 amma sauran nahiyoyin African da kwai wassu wanda sukayi tajdidi kaman su sheikh Usman dan fodio kaman yadda mauka fada,da su sheik Muhammad na Sudan,da sheikh umar sa'id alfuti,a Mali,sun tashi kawari da gaske wajen yada musulinchi a inda suke da kuma koyar da larabchi da bude makarantun musulinchi wannan yana daga chikin ayyuka da sukayi.

Mahir Abdullahi: ina mika Uzuri zuwa yen uwa da suka kira numbarmu Kafin muje aji na Hutu muna musu alkawarin daga wayarsu,da farko dan uwa sabri daga kasar misra

Sabri maruf : salamu Alaikum warahmatullahi wa Barakatuh

Mahir Abdullahi:ka yafemu da rashin daukar wayanka a lokachi

Sabri maruf: ba komai

Mahir Abdullahi:bisimilla

Sabri maruf:ina mika gaisuwa wajenka da bakonka sheikh ibrahim.

Nahiyar Africa ta kasanche nahiya da tafi ko ina musulumai kaman kidanchin ta na larabawa dukkansu musulumai ne,

Ibrahim saleh Alhussaini:mungode Allah

Sabri maruf: Idan baza kadamu ba zan baka wassu kidaddaga na wassu kasashen kaman Nigeria 76% musulumai ne kasar Senegal 92%musulumai ne,Kasar Niger 80% musulumai ne,kasar Chadi 85%musulumai ne,kasar Tanzaniya 63%musulumai ne,Kasar  Mali 90% musulumai ne wannan yana nuni chewa musulumai suna masu yawa a nahiyar Africa,amma a karni na ashirin kiristochi la'anannu sukayi kokarin maida nahiyar zuwa addininsu har ma sukache,mu baza mumaida musulumai kiristochi ba da wannan girma ne a garesu amma za musasu Subar addininsu,zan iya baka kidaddaga chewa da kwai Makarantu 16671 da suke koyar da kiristanchi a nahiyar,amma abun takaichi muna ganin chewa yawanchi Anbada himma wajen kira ga addini zuwa kasashen turawa duk da Africa tana da asali na addini muna kira da a himmantu wajen tabbatar da addinin musulinchi a chikinta

Tambyar izuwa wajen babban bakone,Duk da Nigeria tana da musulumai 76% 20%kuwa krista ne kuma 4%wassu addinai ne duk da yara da sukeyi shine turanchi,ina rawan da musulumai suke takawa a siyasar kasan,saboda yawanchin kasashen Africa musulumai suna dayawa a chiki amma turawa ne Ka hukunchi a kasashen kuma su ke Jan ragamar kasashen kamansu Ethiopia,Djibouti, da sauran kasashen musulumai

Mahir Abdullahi: yana da kwai angane tambayarka,muna godiya,dan uwa Khalid yusuf ne a waya daga kasar Imarat,bisimillah

Dan uwa Khalid bisimillah.

Khalid Yusuf: Assalamu Alaikum wa warahmatullahi wa barakatuhu

Mahir Abdullahi:wa Alaikumusslam

Khalid Yusuf:Annabi SAW yana chewa yahudawa sun kasu Kashi saba'in da daya,Nasar ko sun kasu Kashi saba'in da biyu,Al-ummata Kuwa za ta kasu kashi saba'in da uku,dukkansu suna wuta sai kashi daya,wani Kashi ne wannan ya Manzon Allah?shine wa'yenda suke kan abinda nake kai sa sahabbaina ko kuma jama'a suke kai. Mun kuma ji sheikh Qardawi yana chewa hadisinnan ba sahihi bane ko dai wani abu kaman haka,Allah kuwa yafi kowa sani.

Mahir Abdullahi: ni naji wata qissa mai dadi daga wajen shehi kuma zan nemeshi da yamai maita mana ita amma bayan wannan kira da zan ansa na karshe,dan uwa sidi amin inyas daga Kasar Senegal bisimmillah.

Sidi Amin inyas:(shugaban jaridar Al-fajr)na gode dan uwa mahir,Assalamu Alaikum wa warahmatullahi wa barakatuhu

Mahir Abdullahi: muna maraba da kai

Sidi Amin: ina mika gaisuwa gareka da kuma bakonka dan uwana ibrahim saleh wanda mukasansa kwarai,kuma shi yana daya daga yen makka dan yasan Africa sosai,kuma yabata gudun mawa kwarai,ya bayyana dayewa kan yadda musulinchi ya shigo Nahiyar Africa kuma ya yadu chikinta,da kwai wani bangare da yakamata ayi magana akai shine magananku kan rubuche-rubuche da akayi kuma ta yaya sukayi,musulinchi ba dole bane ache yana da waje na musamman har ma idan wani balarabe yaga dan Africa yana wanna yare na larabchi sosai sai yayi ta mamaki,idan yaga shi baki ne ko yafito daga nahiyar sai yafara tinanin ta ya wannan yake larabchi haka,musulinchi ya iso kuma an yada larabchi chikinta duk da ta sha wahala wajen yen mulkin mallaka,sabo da yen mulkin mallaka sunzo ne da 'yebe Alherin da ke nahiyar,kuma yazo da wani tsarin chanza masallatai izuwa majami'ar kiristochi, toh wa'yennan da suke  magana da wannan yare suna yada shi da addini ana foskantarsu da kiyayya dawwamammoya,ta wata nahiyar kuwa, wanda tafi Muni itache yadda wassu larabawa ke kafirtar da wassu,san suche wannan sufi ne,wanna darika ita ta kare musulinchi, shehi ya ambachi sheikh umar alfuti wanda yake daukar charbi a wannan hannu takwabi kuwa a daya hannun,cherbi domin tabbatar da addini da zikiri a zukata,(lalle da zikirin Allah zukata ke samun nitsuwa)har she sheikh muhamad alhafiz da sheikh Ibrahim saleh ya sansa kwarai ya rubutawa daukar tumbuktu wasika daga Dakkar wa'yennan rubuche-rubuche duk suna da muhimmanchi kwarai,amma larabawa kaman basudamu da duk wa'yennan ayyuka ba sai dai su ambachi chewa su sufaye ne su kafirai ne,shin zikirin Allah shine fita daga Addini, ko dai daukaka manzon Allah ne fita daga Addini, da kwai wata magana mai kew da sheikh Hasan Annadawi ya fada : "ya ku masu bautawa banaye kutausayawa masu bauta wa kabura," wato su suna zargin wassu suna bautawa kabura su ko suna bautawa banaye,a Karshe za ambachi wata maganan shekh Ibrahim wanda sheikh Ibrahim saleh ya sansa yana chewa "wannan addini zai tabbata da larabchi da kuma wanda ba balarabe ba zai karfafa"lalle mun fahimchi wa'yennan abubuwa to wannan addini zai yadu kuma zai karfafa insha Allahu.

Mahir Abdullahi:dan Uwa mun gode

Sidi Amin: zan dakata anan sabi da kuna tare da wanda yasan wannan sosai kuma shi jarimi ne a fannin

Mahir Abdullahi: mungode sosai dan uwa sidi,ina neman tinda kana mana magana aaga Senegal ne kamana magana da sheikh Ibrahim Job da yazama bakonmu a wannan shiri sabi da anche yana daya daga masu kwarewa wajen magana da larabchi.

Ibrahim saleh Alhussaini: yayi keu

Mahir Abdullahi: Kabani Dama na danyi tsokachi wa dan uwa Khalid kamin kabada ansa kan maganan da yayi kan sheikh Yusuf qardawi bai taba kiara kan hadewar addinai ko wani abu mai kama da haka a wannan shiri ko wani shirin,shi yana kira ne izuwa muhawara tsakanin addinai,kuma lalle da kwai banbanchi tsakanin wa'yennan abubuwa biyu,duk kuma wanda bazai iya ban banche tsakanin abubuwa biyunnan to kamata yayi shuru kada yayiwa malamai shisshjgi. Akramakallahu kabadi labari mai ban mamaki kan wani malamin krista  da yake iqrari chewa ai sunfi musulumai yawa a Nigeria,ba kaman yadda sibri ya fada ba daga kasar misra,to me yake nufi da wannan,yayinda yayi anfani da damar chewa musulumai suna jayayya suna chire wassu bangare daga musulinchi a nahiyar Africa,

Ibrahim saleh Alhussaini: kwarai da gaske maganan dan uwa sibri yana da muhimmanchi kwarai, chewa musulumai sunfi yawa a Nigeria amma wani rawa suka taka a hukumanche,in akwai lokachi zanyi bayani akai.

Kaman yadda kache musulinchi yashigo nahiyar Africa ta hannun amintattun mutane.

Mahir Abdullahi: ina son ka bayyyana mana labarin malamin kiristanan

Ibrahim saleh Alhussaini: zanyi magana akai,ina maganan yadda musulinchi yashigo ta hannun amintattun mutane da salama da yafiya,da fahimtar juna,da muhawara ta anfani da hankali,ya kamata ache yen nahiyar sun dukufa wajen yada irin wannan Kira izuwa musulinchi sai dai kash! A zamani ma karshennan musulumai sun raba kansu,suna Tuhuman junansu,suna kafirtar da juna,a matsaloli da basu taka kara sun karya ba,wanda ba farillu bane a musulinchi, shi yasa abubuwa na ban dariya suka faru a Nigeria,Kaman yadda dan uwa yache 76% musulumai ne,muma kuwa muna chewa adadin Yakai haka ko ma yafi,ko ma a kudanchi,sabi da ba ataba yin kirista hakimi ba a Lagos,sai dai musulumi,hakama Kasar Jos,hakama babban birnin kasar duk da yana tsakiyar kasar wanda yake zama hakimi chiki wato Governor musulumi ne. Wannan kuwa dalili ne na chewa musulumai sunfi yawa a kasar.

Wataran da kawai wani malamin kirista da yazo Jami'ar Jos,sunansa Sabiya,yache shi yana son ya tabbatar wa mutane su waye suka fi yawa a Nigeria,shin musulumai ne ko kiristochi?sai yache kiristochi ne sukafi yawa,mutane sunyi mamaki kwarai, ya zai che haka!

Yache yanzu anan Jos, daman ita Jos kuwa da kwai malamai masu kira izuwa addinin musulinchi da kirannansu yasha banban da na sauran malamai a kasar,sai yache masu sifa kaza daga musulumai suna chewa yen mazhabar malikiyya sufaye kafirai ne,kuma naji suna chewa annabinsu yache duk wanda yache wa dan uwansa kafiri to dole dayansu yafita daga addini,to kaga wa'yennan da suka kafirtar da wa'yenchan sun zama kafirai,wa'yennan kuwa sun zama kafirai kaman yadda annabinsu ya fada,toh kaga munche musulumai 37% ne a ra'ayinsa fa,za musamu adadin masu kafirtarwa 4%,kuma za mudauki adadin wanda aka kafirtar chiki musulumai  wanda yakai 27% zuwa 30% idan muka hada 27% muka kara mar 4% da kuma 31%

Ibrahim saleh Alhussaini: 31% da 37%

Mahir Abdullahi: musulumai za suzama sunfi yawa

Ibrahim saleh Alhussaini: kiristochi za sufi yawa, yache shi da wannan zayyi hukunchi chewa ni zanyi wa wa'yennan da suka kasa gane addininsu da chewa kiristochi sufi yawa.

Dan uwana kaga wannan abu yana da ban haushi,lalle wannan rabe-rabe da sabani kan abubuwa da basu taka kara sun karya ba yana da tasiri a zukata,da siyasa,harma da tattalin arziki,da nahiyar zamantakewa,yanama da tasiri a ibada,amma munayi wa Allah godiya chewa abubuwa suna gyeruwa fatanmu kuma akoma kaman yadda ake da,Munkai ga idan abokin gaba ya shigo yana fada da wani bangare daya bangaren bazai taimakawa dan uwansa ba,da haka kuwa zai iya gamawa da dukkanin musulumai,da wannan zan iya chewa kaman yadda dan uwa sibri yafada chesa musulumai sune masu yawa a Nigeria ,sai dai wani rawa suka tana a hukumanche?

Zan iya chewa tsarin da yake tafiya a Nigerian kai kasani,ba kuam a Nigeria kadai ba,za mu iya chewa yen mulkin mallaka da suka shigo ba wanda sauka yaka sai mabiya addini,Kuma sunyi kokarin sharesu,ta yanda baza su iya chanzawa yen kasa ra'ayinsu ba,ya kuama sa shamaki tsakaninsu da hakimai musulumai,

Mahir Abdullahi: ina neman afuwanka,kache hakimin Jos ko da yaushe musulumi ne ake zaba,wannan dalili ne na chewa musulumai sunfi yawa amma shugaban kasan fa.

Ibrahim saleh Alhussaini: shugaban kasa ba ko da yaushe ake zaban kirista ba,sabi da ta hanyar Zabe ba wani kirista da ya taba zama ahiganban kasan,sai a wannan lokachi,Wannan lakochi kuwa bazan iya chema taya ya kasanche ba,sabi da wata irin hanya che ta yakan musulumai daga kasashen yamma, Amrica da kasar ingla da sauran kasashen turawa,suna ganin chewa yen arewa suna chutan yen kudu,kuma suna ganin chewa tin bayan mulkin mallaka da yen arewa suke ta mulki ba su tabka komai wa yen kudu ba,shi yasa yen arewa ba da sunan musulinchi ba da sunan chewa yen arewa sukaga bari mubasu suyi mulkin shekara hudu.

Mahir Abdullahi: kenan yarjejeniya akayi

Ibrahim saleh Alhussaini: haka ne amma har yanzu musulumai sunfi yawa a mulkin muna kuma fatan Allah yasany suyi gyera a gaba.

Mahir Abdullahi: toh man yasa idan misali mun koma wa tambayar dan uwa sibri muka mata gyera, me yasa larabchi bazai zama shine yare da akeyi a hukumanche a kasar ba,ko kuma muche yaren Hausa tinda shi larabchin ma shigowa kasar yayi

Ibrahim saleh Alhussaini: eeh larabchin dai ya yadu a kasar

Mahir Abdullahi: me yasa ba tazamo itache ba

Ibrahim saleh Alhussaini: a Nigeria yaren larabchi ya yadu sosai tsakanin musulumai,amma a yanzu yaruka da suke yaruka na kasar wanda akafi sani su hudu ne,ko wanne anfi yinta a nahiyar mutanenta,sai dai Hausa shine yare da yake karbabbe bayan yaren turanchi a Nigeria, yaruka hudun kuwa sune ;yaren Hausa a kasashen Hausa,kanuri a  Borno,sai yorobanchi a yammachi,da yaren igbo a nahiyar kudanchin kasar,sai dai turanchi shine yare da ke hada yen wurare daban-daban a kasar,kuma lalle wannan kuskure,Allah kuma yakawo lokachinda za muga Africa za ta samu inchinta baki daya ta koma zuwa yaren da take da shi.kasar Nigeria da take da yaruka da suka kai 250 a al-ummu daban daban,ba wani jama'a da za kasamu basa yin yaren larabchi,turanchi kuwa ya zamo yare na kowa duk da chewa mun san yare ne na mulkin mallaka da shi ake aiki,sai dai dan uwa sibri idan ka duba duk kasashen Africa kasashen yamma sun mallakesu kuma sun lalatasu,sun Janza musu yanayi,har a nahiyar siyasa ta ajiyesu kan wani gada da zai kare da su a tsakiyar Kogi, ina ma zai tsaya da su a tsakiya ne,kaga yadda kasashen mu suke kwaikayansu ta nahiyar tattalin arziki abunda ya jawo mu izuwa halaka, hakama a dukkanin abu buwanmu, sabo da haka afrika baza muche ta kure ba waje  ginin nahiyar,muna dai fatan ta tsaya da kafafunta a gaba da yardar Allah a Nigeria da dukkanin kasahe da aka karbe musu inchi.

Mahir Abdullahi:da kawai yer uwa Aata yare da ni bisimillah

Mahir Abdullahi: walaikummussalam yet uwa Aata

Aata Ibrahim: Iran za Kubani dama ina da tambya zuwa shehi

Aata Ibrahim : mafi yawa chikin yen Africa suna damuwa da maulidi me dalilin?

Ibrahim saleh Alhussaini: suna bikin murna

Aata Ibrahim: suna bashi himma,suna kuma murna,ina son dalili me yasa suke haka?

Ibrahim saleh Alhussaini: tambaya ta biyu

Aata ibrahim: musulinchi a nahiyar Africa duk daya ne ko akwai banbanchi chiki?

Ibrahim saleh Alhussaini: yayi kew

Mahir Abdullahi: Tare dani dan uwa salah Muhammad daga Kasar ingila

Salah Muhammad: alo Assalamu Alaikum

Mahir Abdullahi: wa Alaikumusslam

Salah Muhammad: ni marubuchi ne daga kasar libiya,nayi rubutu kan manyan malaman malikiyya a libiya

Ibrahim saleh Alhussaini: yana da kew

Salah Muhammad:a wannan takarda nayi magana kan rawa da wa'yennan malamai suka taka wajen yada musulinchi a nahiyar Africa,ina gaida mahir ina kuma mamakin yadda shehi bayyi magana kan malamanan da kokarin da sanusiyya tayi

Mahir Abdullahi:  ina tare da dan uwa mahmud Ahmad daga kasar saudiyya

Muhamud ahmad: Assalamu Alaikum

Mahir Abdullahi: wa Alaikumussalam,bisimillah

Mahmud ahmad: ina maka fatan alheri a wannan shiri da kakeyi tare da baki da kake gayyata

Mahir Abdullahi: Allah ya saka maka dan uwa

Mahmud ahmad: a gaskiya ni tsokachi zanyi ,kan sarakunan Africa, na kasanche ina binchike kuma ina yawan yafiye-tafiye Zuwa kasashen musulumai a fadin duniya,chikinsu naje tumbuktu, a shekara 66,na kuma na je chibiyar ta Ahmad Baba kuma ya kasanche a sifar Daki ne mai tsayi, abinda na gani shine rubutattun takardu da hannu wanda yakai shekara dubu da rubutun tsarin husain,Wato Harafin fa ba tare da digo ba da kuma harafin qaafun da digo daya a sama,kaman yadda kukasani,yana da wuya kaman mu na nahiyan larabawa mukarantashi,ina kuma sami rubutun hannu na sahihul bukhari,na kuma sami takardu masu yawa,na sami kuma masallachi da aka gina shekara 700,abinda yabani mamaki sarkin lokachin sunansa (musa turawi)da yasu yin hajji sai ya tura wassu su gina masallachi da zayyi jummaa a chiki kafin ya iso wajen,kuma ya na tafe da rakuma dubu ma su daukan gwala gwalai dan chiyar da mahajjata sabo da Allah,kaga irin wannan masarauta da irin tattalin arzikinta babu irinsa bangansa a ko ina ba ko a kasashen larabawa,kuma zan fada tsakanina da Allah na sami mutanennan sunfi kowa sanin addini a duniya da ladabi,da Managartan ala'adu,da tausayawa,zan takaita mu muana da ginshiki amma munsakeshi,ina mu ina tumbuktu,da kuma zuwa wurin dan anfanuwa da ilimin da ke chikinta,da ma sauran gurare a Africa

Mahir Abdullahi: mungode dan uwa mahmud

Mahmud Muhammad: ina da abu daya da nake so nakara

Mahir Abdullahi: bisimillah

Mahmud Ahmad: Allah ya saka muku,kun kasanche tare da hakika masu yawa chikinsu shekh Yusuf alqardawi kunyi magana kan bikin maulidi,ni bana kiransa bikin maulidi ina kiransa na bikin yin bishara da Haske da Allah ya aiko ya zamo abun jin kai ga Al-umma, Allah yache (mai jin Kai da tausayi ga muminai)abu mai muhimmanchi shine chewa Annabi SAW shine yafara yin wannan biki,idan kuma nayi kuskure shehi ya min gyera

Mahir Abdullahi: mun gode kwarai

Mahmud Ahmad: sahabbai sun tambayesa munga kana azimin ranan litinin me yasa ? Ya che :rana che da aka aifeni chiki,kaga shi bikinsa shine Ibadan azimin

Mahir Abdullahi: mungode kwarai

Mahmud ahmad: rana che da a chiki a ka aiko ni,kuma chiki zan koma wa Allah,kuma chiki aka sauko min da alquraani

Mahir Abdullahi: mungode za kaji bayani daga shehi

Akwai abu na ban al-ajabi da ya faru a jahar Kaduna inda wani daga chikin irin wa'yenda basa ganin girman musulinchi da Haibarsa ana chikin sallan Jumma'a ya rinks shiga tsakanin Sahun masallata da takalmansa yana taka sallayarsu da tabarmansu da suke salla akai,wassu matasa ko suka Fusata suka tada kayar baya wanda tajawo ga mutuwar wannan mutumin. Kaga bamusan ire-iren wa'yennan fitunu ba,ada sun kasanche suna girmamamu,amma bayan musulumai sun fara kafirtar da Junansu sai haibarsu da na musulinchin ta gushe.

Mahir Abdullahi: yayinda musulumai suka fara zargin junansu sai su ma wa'yenda ba musulumai ba suka abka musu

Ibrahim saleh Alhussaini: kwarai sun bude musu hanya izuwa..

Mahir Abdullahi: akramakallahu za mukoma wa tambayoyi da akayi ta waya amma kafinnan ina da tambaya sabi da mu takarkare maudu'in,muyi maganar yadda musulinchi ya yadu a tsakiyar nahiyar Africa da yammachinta,dan uwa Ballishi yana tambayan yadda musulinchi ya shigo ta hanyan attajirai,kada kuma mumanta taka rawa da yen Kasar ta Umman sukayi,wanda suka tashi tsaye wajen yada addinin musulinchi a lokachin Daular  Umman da take Gabashin Nahiyar,haka munyi magana kan Tumbuktu da (Kalwa) a (zinjibar)shin da Daular umman din tataka rawa kwarai wajen yada addinin musulinchi a nahiyar Afrika?

Ibrahim saleh Alhussaini: lalle ba shakka Daular Umman tayi kokari kwarai wajen yada addinin musulinchi, dangane da Kaula kaula kuwa da kwai wata tawaga daga Zaidawa da suke iso daga chan zuwa nahiyar Afrikan a shekara ta 122 ta Hijira,tin wannan lokachin kuwa musulinchi ya ya kafu kuma yayi karfi a nahiyar, Daular Umman kokari da tayi ba tsabani akai,su suka yada musulinchi kuma suka kafa kasashe kaman su Magadishu,(Marka),(Barawa)da sauransu,da kwai kuma wani da ya ahahara a wa'yennan kasashe da ake kira (Muniri wabara) daya daga chikin yen Umman ne da ya zauna a Nahiyar  yayi kokari kwarai da bai baigaza da kokarin da yen Daular Morrocco sukayi ba a yammachin Afrika ba,ko kuma kokari da Daular Tumbuktu tayi a wajen yada ilimi a nahiyar,lalle musulinchi a dukkanin wa'yennan wurare ....kokari ne yen Daular Umman sukayi ta wani gefen,kulawansu da Malamai abu ne da ke misali da shi,dan malamai a wanchan nahiyar har yanzu suna kulawa da wannan abu da suka gada daga yen Umman,haka kuma wannan abu yayadu izuwa kasar Yamen,da kuma kasar Adin,da Habasha,da Iritirya,har ma wassu sassan kasan Sudan,duk Wannan kokari da sukayi kwarai ba amanta sa shi ba kuma yananan rubuche.

Mahir Abdullahi: da kwai tamabayoyi uku,zuwa Hudu da aka turo ta....

Ibrahim saleh Alhussaini:  Bisimillah mana

Rawan da malamai suka taka a nahiyar Afrika

Mahir Abdullahi:kan kokari da yammachi da gabashin nahiyar na larabawa wajen yada musulinchi ina son takaitacchen bayani sabi da muna kan gaba....

Ibrahim saleh Alhussaini: wallahi a takaiche malamai a nahiyar afrika ko kuma yammachi da kudanchi na nahiyar sun taka rawa kwarai,mu munsani chewa Alkura'ani ya shigo nahiyar ne ta wajen wa'yennan masu kira izuwa Addini,da karatun warsh na Nafiu,da riwayar Qaloon ita ma ta Nafiu,da riwayar Duri ta Amru,Wannan karatuttuka sun yadu ne a nahiyar ta kokarin malamannan wand suke sunzo ne daga Kasar Libiya,Tunis,da Morrocco,hakama ilimin Fiqhu,da mazhaba ta imam Malik,kaman yadda kasani dukkanin nahiyar Africa mazahabar malik suke bi,wanda ya iso ta hanyar malamai daga kasar Morocco kuma suka yadashi ta hanya ingantacchiya,har yanzu bayan da kasashen musulumai suka zamo suna tare ba wani ban banchi tsakanin malamin Mazahabar da yake nahiyar da wanda yake jamai'ar Azhar ko wanda yake Jami'ar zaituna ko jama'ar karaween,toh gaskiya gabashin nahiyar na Larabawa da dukkaninn kasashensa daga Libiya,Tunis,Jazaiyir,da kuma kasar Morocco da wassu chikin yen Muritaniya ga kasashe da suke makwabtaka da su kaman Kasar Senegal da Mali. Amma kaman Nahiyar Borno da Kanim da kuma masarautun Hausawa to lalle da kwai malamai da suka iso wajen da ga Tunis,da Morocco kaman Sheik Ilmy, da shehi Fantur,da sauran sanannun malamai da suka yada mazahabar ta malikiyya a wa'yennan kasashe.

Mahir Abdullahi: da uwa Muhammad yusuf idris yache yana ganin chewa hira ta kwashemu da ma su masu saurarammu Baki daya izuwa Gabashin Afrika,yache Yanason ya maidamu zuwa Ethiopia wanda harin turawan yamma yafi karfi a wajen ..wanda da yadache a Kirata da masarautar musulinchi.

Ibrahim saleh Alhussaini: Ethiopia

Mahir Abdullahi: yana nufi  mun anbachi sarki Najashi amma kuma sai ba inda hari yayi muni kaman wajen ya fi ko...

Ibrahim saleh Alhussaini: kwarai Ethiopia musulinchi ya shiga Afrika kafin ko wani waje sai da Ata da kasar Makka take chikinta,Afrika ko muche Ethiopia ta maraba da musulinchi kafin dukkanin kasashe sai sai kasar larabawa,kuma musulumai na Farko, sabban Annabi SAW sun kasanche a Ethiopia lokachi mai tsawo,kuma sunyi tasiri kwarai,sai dai lokachinda musulinchi yafara yaduwa zuwa sauran kasashen Afrika ba ma shakka chewa da kawai adadi mai yawa da yakarbi musulinchi a Ethiopia,suna ma daga chikin wa'yenda suka shigo tare da mayaka da malamai kaman nahiyar Kanim da (waradi),chadi,Nigeria wajajen (Kano)(Kaduna)da su (sofito)da ..

Mahir Abdullahi: dan uwa Yusuf yana tambaya ne chewa shin za ka iya tino takardu da suke magana kan musulinchi a nahiyar Habasha?

Ibrahim saleh Alhussaini: wallahi da kwai da dama,dukkansu takardu ne da ba asansu ba,ba kuma takardun musulumai bane,akwai takardun dan uwa Aatif Annawawi wanda yake magana kan musulinchi a nahiyar Afrika,hakama Talmanjam,ya rubuta takardu masu yawa kan musulinchi a gabashin nahiyar Afrika,da kwai kuma shehi Abdurrhaman zaky,shima kan gabashin Afrika inda yake tabo Habasha,da kwai kuma wanda yen kasar Habashanne suka rubuta bana iya tina sunayensu amma na karantasu,..kuma ana samunsu

Mahir Abdullahi: kaman yadda kasani shi dan uwa Yusuf yana kuma tambaya ne shin za asami wani shafi a yanar gizo da yake magana kan nahiyar Afrika?

Ibrahim saleh Alhussaini: wallahi akwai dai daikeku da suke da shafuka wanda bana iya Tina su a yanzu,akwai kuma chibiyoyi da suke shafuffukan yanar gizo,amma su ba kan musulinchi a nahiyar bane suna dai magana ne kan Nahiyar kuma ba musulumi bane suka rubutasu ba to kaga ba za mu dogara da su ba.

Mahir Abdullahi: dan uwa Hazim Ahmad quraab yana Tambaya kan yanayin yadda hari ne gabashi da na kiristanch a Nigeria?kuma shin kuma kuma iya Tina yadda kori malaminnan Ahmad Qurab daga kano?kuma hakika da kwai tambaya da dan uwa Habi Hasan Nasir yayi kan shigowan kiristanchi nahiyar Afrika,shin kasar Israila tana wani karfin iko a nahiyar ?kuma shin da kwai wani takura da akeyiwa kasar Nigeria na musamman?

Ibrahim saleh Alhussaini: wallahi ita Afrika...Israila tana da karfin iko a wassu wuraren,amma na samuwanta a wajen na kasuwanchi ne,hakazalika da kwai lokachi da ta kasanche bata kasar ta Nigeria, bayan Alakanta da kasar ya yanke suka fita daga kasar bayan wani lokachi kuwa alakan ta koma sai suka zo a attajirai,da sunan wassu kanfanoni wanin kuwa abu ne da ba wanda zai musa shi,amma abu da nakeso na kwantar wa yen uwa masu saurarammu hankali dashi shine su sani chewa yen uwan musulumai a kasar sun san duk wani irin makirchi da Israila take shiryawa ga Afrika musamman ma Kasar Nigeria,kuma kan maganan dan uwa Quraan bansan dalilin ba amma naji labarin,naji magana dewa kansa,amma  bansan dalilin me aka Koresa daga Nigeria ba.

Mahir Abdullahi: ina nema a takaiche sabi da saura min mintina da basu kai uku ba da na karkare

Ibrahim saleh Alhussaini: yayi keu

Mahir Abdullahi: my munji labarin yin aiki da shara'ar musulinchi a Nigeria, antada hankali ds kone-kone a wassu jahohin, shin abunda yake faruwa a kasar a matsayinka na wanda yake kusa da masu mulki a Nigeria, shin abunda yake faruwa a kasar a sabbain Shara'ar musulinchi a kwai Kari chiki ko kuma wani abu ne da kiristanchi suka tashi da shi,ko dai lamari ne na wanda suka kauche hanya kaman yadda muke gani a wassu wuraren?

Ibrahim saleh Alhussaini: wallahi hakikanin lamari mu a Nigeria mun rayu lokachi ma yawa da ba'a aiki chiki da sha'rar musulinchi, shi yasa muke fatan muga ankoma aiki da ita,wannan fatannamu kuwa yawanchin yen Nigeria suna da ita,yawanchi Yanason yaga hakan ya wakana ne ba dan siyasa ba ko wani abu,Wannan kuma yau a Abuja ana ta anfani da shi,yen siyasa da sukaga anason hakan sai sukayi anfani dashi da susamu abinda suke so,amma hakika lamarin aiki da shara'ar musulinchi da yafaru a jahar zanfara, kano da Borno,da wassu jahohin yana da gaskiya na wajen ganin hakan yafaru ga al-umma musulumai, sabi da bayan barin mu ga Shara'a abubuwa da dama sun faru har za kaga rayuwa musulumi da na wanda ba musulumi bata da wani banbanchi, Shara'a kuwa ita che za takawo konchiyan hankali da zaman lafiya da gaskiya a siyasa tsakanin musulumai, shi yasa musulumai a Nigeria suke fatan suga hakan yafaru.

Mahir Abdullahi: to kasanchewarka kusa da masu mulkin ko zan iya chewa daya daga masu mulkin....a saninka daga shugaban kasan shin da kwai wani tsoro tattare da yiwar hakan ga kasan ko ga mahukuntan kasar?

Ibrahim saleh Alhussaini: a'a kasar bata tsorata ba kuma wannan tarzoma da wassu sukayi daga yen uaanmmu a kudanchin kasar wassu ne daga wajen kasar suke zugasu,ai Shara'a ratuwar musulumi dukkanta Shara'a che,aiki da Shara'a ba abu ne da zai baiwa kirista tsoro ba,gaskiya ne da kwai wa'yenda suke baiwa kiristochi tsoro,suna basu tsoro da wassu maganganu da suke fadi,amma a hakikanin gaskiya Shara'a tana kare kirista kaman yadda take kare musulumi,shi yasa baza muche hukuma tana tsoron hakan ba,amma da kwai kungiyoyi da suka sa kiristochin da sununa rashin yardarsu sabo da wani ra'ayi nasu na siyasa.

Mahir Abdullahi: Akramakallahu muna godiya kwarai,kuma zan so na kwantarwa wassu yen rai kaman su dan uwa Abussanud wa'enda Suke son suganka chikin tufa ta Nigeria inche musu kasar wanna abaya ta larabwa da kwai tufa ta Afrika.

Ibrahim saleh Alhussaini: tufa ta Afrika kuwa kwarai gatanana.

Mahir Abdullahi: muna rokon yen uwa da ba musamu mun basu daman tsokachi ba ko ta hanyar faks,ko yanar gizo,a madadinku baki daya zan mika godiya ga mai girma sheikh Ibrahim saleh Alhussaini wanda yake daya daga zuriyar Annabi SAW a tarihi kuma..

Ibrahim saleh Alhussaini: wallahi kabar wannan dai...

Mahir Abdullahi: muna muku godiya da bibiyarmu da kukayi,sai min hadu a wani shirin na sati mai zuwa,aminchin Allah ya tabbata gareku.