Takaitacchunn qasidu
kekkewar fahimta ga Addini
Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai
Tsira da aminchin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu SAW da aalayansa da
sahabbansa da wanda suka bisa
Gabatarwa
Ba a gushe ba bukukuwa na alheri sun zageyowa wanda a dalilinsu dogaro da
Allah da imani yake karfafuwa,sune kuma suka kare wannan addini mai girma.Allah
SW yana chewa (mu muka sauke wannan Alquraani kuma mu za mukiyayeshi)aya9 daga
suratul hijir
Du da irin wahala da wannan al-umma take gani daga aduwwanta na gaske da
kuma masu batarwa Sanye da rigan musulinchi da jahilai da suke mara musu baya
chikinsu har munafikai da gafalallu masu ba'a da addini,wannan alumma za ta
kasanche tana samin wanda zai jaddada mata addininta bayan tsoro da ake shiga
na ganin dashewan wannan addini,wanda zai karfafa mabiyan addinin yasa su
himmantu wajen yiwa addini hidima ta hanyoyi masu gamsarwa wanda za suyi da
niyya mai karfi,sai Allah ya basu daman yin hakan a sawwake.
Kaman yadda muka saba ya ku mabiya rubuche-rubuchen da mukeyi a sashen
Assiyada,muna masu farin chikin yada muku wannan kalima mai matukar muhimmanchi
wanda ko wani layi a chikinta ya kamata musulumi ya Sansa kuma ya kamantu da
shi,idan har shi mumini ne mai keutatawa mai karfin imani,mai kuma tinani,wanda
kuma yake aiki da himma da kuma zuchiya daya domin yada ilimi da sani ba tare
da ya chanza ba,yayi aiki da wannan kalima ba tare da ya tsawwala ba ko ya
Gaza,domin Rahama ta sauko,albarka kuma ta mamaye ko ina,adalchi da kuma yin
yakamata ya zama ya wanzu ko ina,zalinchi da nuna bambamchi ya gushe,har duk
dan adam yazama yan chikin walwala sabo da wannan addini wanda dukkanin
annabawa da manzanni suka yi bishara da shi,inda Allah ya ke chewa (فاقم وجهك للدين
حنيفافطرة الله التي فطر الناس عليها....الخ )
Wannan kalima duk da karanchinta ta kasanche da ma'ana mai girma wanda zai
budewa mai karantata wani babi na fahimta da kuma jaddada imani,muna kuma fatan
isar da wannan sako da inganchi,muna kuma fatan samin anfanuwa da tarihi da
jaddada niyya sabi da yin aiki mara gushewa tsakaninmu da Allah domin Mubada
nasara da wannan addini.
Muna kuma mika godiyammu ga yen uwa da suka jure wa wahalar balagaro sabo
da ziyaratar sheikh sahariff Ibrahim saleh
daga kasashensu masu nisa zuwa kairo a kasar misira,ba dan komai ba sai
sabi da Allah,sun kasanche sune dalilin wannan infanuwa da mukayi da wannan
kalima da kuma al umman musulumai baki daya da za su anfanu da wannan jawabi
mai matukar muhimmanchi Allah SW yana chewa (وما كان المؤمنون لينفرواكافة فلولانفر
من كل فرقة منهم طائفة ليتفقهوا في الدين ...)
Allah yasaka musu da alheri
Yen uwa wa'yenda sukayi ziran sune
1.sheikh sultan bin muhammad al-maskary daga nasarautan umman
2.malam Ahmad quraishi daga masarautan umman
3.malam Abdullahi assiyabi daga masarautan Umman
4.malam Ahmad yaqub daga masarautan umman
5.Dr mukhtar Ali daga UAE
6.Dr Amin Yusuf daga UAE
7.malam sharif Rashid Ahmad abdurrhaman alkharasani da UAE
8.malam Rahamatullahui Hindi daga Jahar jadda kasan Saudi
Muna rokon Allah da ya sawaita ran maulana shekh shariff ibrahim saleh,ya
karesa da iyalansa da almajitensa ya kuma sayasa chikin koshin lafiya,da basa
nasara ya biya masa dukkan burinsa,babban chikin burin nasa kuwa shine wannan
al-umma ta kasanche chikin hadin kai da nasara,rahama ta kasanche tsakanin
dukkanin mabiyanta duk yanda suke a kuma ko wani bangare,ya bamu zaman lafiya a
ko ina.wanda yake ba abu bane mai wiya
wajen Allah.
Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu
Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin dukkanin talikai
Tsira da aminchin Allah su tabbata ga mafifchi chikin Annabawa da halitta
chikamakin Annabawa da Alayansa da shabbansa tsarkakku.
Bayan haka :-
Wahala da sahbbai suka fiskanta a farkon musulinchi.
Sahabbai Allah yakara musu yarda sun baiwa wannan addini nasara sun kuma
kiyayeshi duk da sabanin ra'ayi da yake tsakaninsu,sabaninsu kuwa na bangaren
fahimta ne,musamman ma lokachin da annabi SAW ya amsa kiran ubangijinsa,sabani
ne wanda yake girmansa yafi wanda muke chiki a yanzu,sabi da me ? Mu Musami
wa'yennan sahabbai sun gama gina mana komai,sun tsara mana hanyar da za
mubi,sun ajiya mana duka wata irin alama da zu mufahimchi addini da ita. Abinda
yarageana kawai shine bin wannan hanyar tasu har mu iso inda muke so.
Amma su sun samu kasanche wanda take bukatar gini,duk wani wahala kuma
Allah ya jarabchesu da ita ya kuma gwada karfin imaninsu,da niyyarsu,in kaso
mai maita wannnan ginin to sai kabi alamunda sukabar maka daga abinda sukaji
suka haddache,suka fahimta daga Annabi SAW wanda yake chikamaki ne ga abinda
annabawa gabaninsa suka zo da shi,musamman abinda annabi Ibrahim yazo
dashi,sabi da yafi wahala a ko da yaushe tushen fara gini yafi wahala,wanda
yafi wanna wahala kuwa shine kiyaye wannan ginin da amana,sabida samin raguwa a
wannan addini wani lokachi yafi wahala,shi yasa wassu suke zaban wata hanya
daban ba ta sahabbai ba,suna kuma tinanin chewa hakan dai dai ne,suk yake
wannan da'awa che wanda bata da kamshin gaskiya.sai Bidia tafara,duk da bidia
abu ne wanda ya tabbata a musulinchi,wanda ta fara ne da Fitowan qadariyya da
murjiaa da mutazila. Da abubuwa da dama tin zamanin sahabbai.
Lokachi na Farko da akafara samin Rabe-rabe a musulinchi
Bayana haka alumma ta kasu zuwa bangare bangare masu yawa .
Haskiya ne chewa annabi a yakin da sayyidna Khalid yayi inda annabi ya aiki
sayyidna Ali da yata ganima ya kawo khumusi wajen Annabi SAW,da kwai kuma wani
sahabi da ya tsani sayyidna Ali,ya kasanche kuma sayyidna Ali ya dau wani abu
bayan khumusi da ya chirawa alayen Annabi SAW,SAW,wannan sahabi da yazo wajen
Manzon Allah sai ya tambayesa shi kai ka tsani Ali?ya che eeh ya Manzon
Allah,sai Annabi yache mar kada ka tsanesa,sabida Ali yana da kaso fiye da
wanda yadauka da khumusinnan,kuma Ali zai kasanche jagora gareka bayanni,du
kuma wanda nake jagora garesa to Ali ma jagoransa ne, ko kuwa magana dai mai
kama da haka.
Hadisin Buraida kuwa yazo ta hanyoyi daban daban ya kamata kuma mukawosa
sabi da muhimmanchinsa
Buraida yana chewa -Annabi yache:shin la tsani Ali tsani wanda ba wanda ka
tsana Kamansa ka kuna so wani baqurayshe kawai sabi da ya tsani Ali Allah ya
kara masa yarda.
Sai nabi wannan mutumin zuwa yaki muka sami ganiman mata sai na tura wajen
Annabi,kan ya turo mana wanda zai dau khumusi ,sai ya turo mana Ali Allah ya
kara masa yarda,da kwai kuma chikinsu wanda tafi dukkamsu kew.
Sai yache musu na dau khumusin kuma daga khumusin ita na dauka.sai mutumin
ya rubutawa Annabi,nache mar katurani na gaskataka,yache sai naje ina karanta wa Annabi kuma ina chewa
gaskiyarsa,sai annabi ya kama hannuna da abinda nake karantawa,yache min,shin
la tsani Ali,nache mar eeh,yache min kada ka tsanesa in kuma kana kaunarsa to
ka kara kaunar, ina ransuwa da wanda ya aikoni rabon aalayen Ali achikin wannan
ganima yafi wannan mache da ya dauka.ya che bayan wannan magana ba wanda na
sasa kaman Ali.Ahmad ne ya rawaitosa
Buraida yache annabi ya aiki tawaga guda biyu zuwa kasar yaman,daya
sayyidna Ali ne ke jagorantarta dayar kuma Khalid binul waleed, yache idan kun
kasanche waje daya to Ali ya zamo jagora,Idan kun rabu kuwa kowa yazamo jagora
ga tawarsa,yache sai muka hadu da bani zaid daga mutanen yeman muka kashe wassu
muka kamasu wassu,sai Ali ya dau wata daga firsunonin wa kansa.Buraida yache
sai Khalid yaban wasika zuwa Manzon Allah SAW da nakai wasikar zuwa annabi ya
karantata,sai na ga tagayyara,sai nache ya Manzon Allah ka aikemu da
jagoranchinsa shi yasa na mar biyayya na kawo wasikar,sai Annabi yache min
(kada ka zargi Ali sabo da ni da shi tamkar daya muke,kuma shine jagoranku
bayana.
Tirmizi ne ya rawaito
A wani riwayan kuma Annabi yache (me yasa wassu chikin mutane suke wa Ali
kallo na raini duk wanda ya raina Ali ya rainani,duk wanda ya rabu dashi kuwa
ya rabu da ni,kusani chewa Ali da ni tamkar daya muke,an halicchesa da lakadda
aka haliccheni ni kuwa dada lakadda aka halicchi Annabi ibrahim aka
haliccheni,kuma na kasanche na fi Annabi ibrahim daraja,zurriyyache waninta
daga wani,Allah mai ji ne masani. Ya kai Buraida shin ba kasan Ali Hakkin da yake
dashi yafi wannan matan da ya dauka ba kuma shine jagkranku bayana ba,sai nache
ya Manzon Allah shin baza ka mika min hannu ba na ma mubaya'a sabuwa,banko rabu
dashi ba sai da nayi sabuwar mubaya'a.
Tabari ne ya rawaito
Haka kuma an rawaito daga Amr bin zi mur da sa'eed bin wahb,da kuma zaid
bin yasi'i sukache munji Ali yana chewa : na tambayi wani mutum da yaji Annabi
SAW ranan Qudair inda yatashi,sai mutane sha uku suka tashi,suka shaida chewa
annabi SAW yache:"shin bani nafi wa muminai fiya da rayukansu ba,sukache
hakane ya Manzon Allah,sai ya kama hannun Ali yache,duk wanda ne kasanche
jagora garesa to wannnan ma jagoransa ne. Ya Allah ya kiyaye duk wanda ya
kiyayeshi kuma kayi gaba sa duk wanda yayi gaba ashi, kaso duk wanda yasosa ka
kuma ki duk wanda ya kisa,ka baiwa duk wanda yabasa nasar,nasara,ka kuma tabe
Duk wanda yachi amanarsa"
Bazzar da wassu suka rawaitosa A sahihul bukhari .
Haka abi tufail yache :"na tara jama'a a wata farfajiya sai nache musu
:ina rokon duk waninku da yaji Annabi SAW lokachin qadeer Khamma me yache ,sai
mutane talatin suka tashi.
Abu na'im yache, mutane Adams suntashi suka shaida inda ya kama hannunsa
yache:shin kunsan nafi muminai fiya da rayukansu? shiKache eeh ya manzon
Allah,yache:duk wanda nazama jagoransa to wannan ma kagoransa ne,ya Allah ka
kiyaye duk wanda ya kiyayeshi ka kuma kulla gaba da duk wanda yayi gaba da shi.
Ya che sai nafito ina jin wani abu na shakka a raina,sai na hadu da zaid
ibn arqam,na che mar naji Ali yana fadin kaza da kaza,ya che min to me kake
inkari a chiki,nima naji Annabi SAW yana fadin hakan.
Sai wassu suka fahimchi wannan maganar da chewa sayyidna Ali shine magajin
Annabi SAW zayyu kuma wannan gadon na gadon zahiri da muka Sani ne tinda shin
dan baffanshi ne,kuma annabi SAW ya kasanche bai da da na miji da yabari,wannan
fa in har ya kasanche Annabawa ana gadansu kaman sauran mutane,in ma har hakan
ya kasanche ai ba shi kadai bane zai kajeshi akwai Al-Abbas da kuma sauran
Aalil baiti da suke mataki daya dasu Al-Abbas.
Wassu kuma sun fahimchi wannan maganar ne da chewa Annabi SAW a ko da
yaushe damuwarsa ba da gado na zahiri da muka sani bane,damuwansa shine da
wanda zai chi gaba da yaada abinda yazo da shi,Wato wanda zai zama khalifansa a
annabta.
Duk mun sani chewa ba wani annabi da zai zo bayan Manzon Allah SAW sabo da
haka bazai ma zo kanmu ba chewa Ali zai zama Annabi bayan Annabi SAW.
Hakazalika mun sani chewa annabwa ba'a gadansu kaman sauran mutane,duk wani abu
da suka bari za bayar dashi ne sadaka kaman yadda sayyidna Abubakar yafada,amma
ana nufin sayyidna Alin zai zamo khalifansa ne kaman sayyidna Abukar da umar da
Usman,kuma suna Zaton chewa sayyidna Ali yazamo shine Khalifa ba tare da wani
jayayya ba sabo da wa'yennan hadisan da aka rawaito.
Da kuma hadisin Albarra bin Aazib,Annabi SAW ya che :"duk wanda nake
shugaba garesa to Ali ma shugabansa ne"Ahamd ne ya rawaito da kuma ibn
maja,Ahmad kuma ya rawaitosa ta wajen buraida da tirmizi da nasa'i
Da kwai kuma wani hadisin ibn ishaq yana chewa :da Annabi yazo fichewa sai
ya maye gurbinsa da sayyidna Ali. Munafikai kowa suka firgita sukache :bai
sashi yamaye gurbinsa ba sai dan bai dawkesa da muhimmanchi ba,sai Ali yadau
takwabinsa ya fita yaje inda Annabi
yake,yache masa ya Manzon Allah SAW ga abinda suke chewa game da maye gurbinka
da nayi.Annabi SAW yache mar kar suke,ni na barka ne sabi da abubuwa da na bari
a bayana sabi da haka kaje la wakilcheni chikin mutanena kuma mutanenka,shin
baza ka yarda kazamo min kaman yadda Haruna yazamo wa dan uwansa musa ba,sai
dai ba wani Annabi a bayana,sayyidna Ali sai ya koma. Hadisin yananan a bukhari
da Muslim, yana kuma takardan sira na ibn Hisham.
Chanchantar sayyidna Abubakar da ya zama Khalifa
Kasani chewa girma da kwarewa ta yau da kullum tana dai dai da ilimi,tana
kuma dai dai da wanda yake sani.shi ya sa sayyidna Abubakar yafi chanchatar da
ya jagwarchi mutane,sabi da me ? Sabi da an gwadashi da dukkanin alumma kuma ya
rinjayi dukkaninsu,shine kuma aboki na kut da kut na annabi da nassin
Alquraani,ya kuama halarchi zamanin jahiliyya,ya San duk wani makirchin da
akeyi a zamanin,da kuma yanda suke tinani. Ya kuma riski musulinchi tin
farkonsa,ya kuma riski duk wani yanayi da musulinchi ya shiga yana babba,yana
kuma da sanin Alheri da Sharri na duniya,ya San kewum halyen mutane da rashin
kewunsa,sabi da haka shi yafi chanchantar sanin masu Kirki da marasa
kirikinsu,da kuma gaskiyansu da rashin gaskiyansu,da hakunchi na kwarai da na
wofi tsakaninsu,da kuma adalchi a shawara da rashinsa.
Sayyidna Uamar Alfaruq da wa'yenda suke komitin nada khalifanchi ,bayan anfitar da sayyidna umar da Abu ubaida
sabi da azabi dayansu,amma sayyidna Umar sabi da kwarewa tasa ya Zabi sayyidna
Abubakar,dalili kuwa shine sayyidna Abubakar mutum ne da hada dukkanin siffofin
alheri na muhajirai,shi yasa yafadi kalimarsa da ta shahara inda yache "da
a fito dani a yanke min wuya ba tare da nayi lafi ba yafi min da na zamo
jagoran wassu da Abubakar ya ke chikinsu"
Wa'yennan abubuwa gaba daya suka zamo dalilai da Ali bai zamo Khalifa ba,
wannan kuwa ya jawa aka rabu kaman haka.akwai sayyidna imran bin husain,ammar
bin yasir,abu ayyub al-Ansari,Abu zarrin da sauransu da suke ganin chewa wannan
ta waye ne akayi wa sayyidna Ali,haka kuma irin wants ra'ayi ba mugushe mina
fama da shi har wannan zamani .
Abubuwa sunyi ta chi gaba bayan sayyidna Abubakar,da sayyidna Abubakar ya
kunsan chikawa kuma ya duba chewa al-umma a wanchan lokachin tana bukatan
mutuma mai zafi,ya Zabi sayyidna umar,shima sayyidna umar da yayi shahada sai
lamarin khilafa ya kasanche na shawara tsakanin mutane shida daga sahbban
Annabi SAW wanda yabar duniya yana mai yarda garesa,sai suka zabi sayyidna
usman,wassu kuma a wannan lokachin suna sukan banu umayya,wassu ko suna
sonsu,mun kuma san me yafaru a wanchan lokachin,mutane sun rarrabu wassu ma suna
ganin chewa khilafan anyita ne bisa son rai,ba da ra'ayin jama'a ba,kawai
anbawa wassu jama'a ne,wanda dune banu umayya,sayyidna usamn kuwa ya sassawchi
sosai,aka chi gaba da haka har wassu masu tada kayar baya suka shigo daga kasar
misra,abubuwa dayawa suka faru da sayyidna usman Khalifa mai adalchi Allah
yakara masa yarda. Chikin wannan lokachi wassu daga sahbban Annabi sun zauna ne
chikin gidajensu ba ruwansu da abinda yake gudana,wassu kuwa sun bar chikin
madina,wassu kuwa sunyi kokarin yin sulhu tsakanin mutane.
Bayan rasuwan sayyidna Usman sahabai suka hade da a ba sayyidna Ali
Khalifa,a khilafan sayyidna Ali kuwa anchi gaba da rabe rabe wa'yenda da chan
suke gaba da shi basugushe ba sai da suka raba kan al-ummah,suka bukachi
sayyidna Ali da ya kashe wa'yenda suka kashe sayyidna usman,duk da yake
wa'yenda sukakashehsa jamaa ne masu yawa,sunyi hakanne ba daya chikinsu da za
kache yana ji ko yana gani,baza kuma iya chewa wane ne yayi hakan ba,dan yana
bukatan shaidu da atabbatar da hakan,kuma ba subaiwa sayyidna Alin lokachi ba
dan ya bi lamarin chikin hikima da sannu,har ya tabbatar da gaskiyan lamarin ya
kuma hukumtasu hukumchin kisa ga Khalifa maiAdalchi sayyidna usman Allah ya
kara masa yarda.
Sai dai kuma su ba hukumtasu da zayyi suke so ba,so suke idan har ya yarda
zayyi mus haddin kisa shima sai a kashesa Kamar yadda aka kashe sayyidna
Usaman,sai daular musulamai takasanche batada Khalifa kowa yayi abinda
yakeso,wannan kuwa shine masu sassauran ra'ayi chikin banu umayya ma suke
so,har maganan tufan sayyidna usman ma ya taso,kamar kuma sayyada Aisha da aka
kawo mata labarin rasuwan Sayyidna usman ba ta damu ba,amma da akache sayyidna
Ali ne yazama Khalifa sai tache ayyaa Usman ta kuma nemi akashe wa'yenda suka
kashesa,wannan duk ya kasanche kuma munsan maysayin sayyidna Ali a qissar ifk
game da sayyada Aish,matsayinsa game da sayyada Aisha a wannan qissa ba abi
bane ma sauki ba,haka kuma lamarin zai kasanche ga kowa idan da ache shine a
wannan matsayi na kage da akyi game da ita.
A Khalifanchin sayyidna Alhassan Allah ya kara masa yarda aka sami
Ahlu-ssunna wal jama'a da kuma shi'amchi. Duka da haka godiya ta tabbata ga
Allah,bayan sayyidna Ali da zuwa sayyidna Al-Hassan wannan qissa ta gushe. Anan
idan muche khalifofi to su hudu ne,idan kuma mun mayarsu biyar to sayyidna umar
bin Abdul-Aziz shine na biyar din,khalifanchin sayyidna Alhassan ba anbatanta
kuma anfima anabatan sayyidna Azzubai akansa,kaman ma bai zamo Khalifa ba,wanan
kuma abu ne da yafaru,sai dai marubuta tarihi ba suyi barshi ya gushe haka
kawai ba.
Al-umma ta sami wannan suna na Ahlu-ssunna wal jama'a da wannan suna yasamu
,sai wani lamari ya taso da yake binne,sabi da lamari yakasanche wajen banu
umayya kadai,mutanen da sukasanche basu
da yarda da banu umayya sai suka bayyanar da aqidarsu ta shi'anchi sun kuma yi
sauri wajen yin hakan.
Wannan shi'anchi ya kasanche a zamanin sayyidna Ali Sharma kuama kafinshi a
zamani n sayyidna Abubakar da Umar. Masoyan sayyidna Ali da Aalayen Annabi
sunanan amma ba tare da tsassauran ra'ayi haka ba. Bayan kuma sayyidna Alhssan
ya sallamar da khlaifanchi zuwa mua'awiya ne sunan Ahlu-ssunna wal jama'a ya zo
kuma shi'anchi ma ya bayyana a daya bangaren.sunan Ahannunsa wal-jama'a ya chi
gaba aka chi sa'a kuma dukkanin mazahabobin malamai hudunnan dama sauran da
suka gushe kaman mazahaban zahiriyya da abi saur da sauransu,duk suna tare da
wannan mazahaba ta Ahlu-ssunna wal-jama'a sai suka zamo suna tushen na
mazhahbobi da wannan al umma take bi.
Sai Lokachi da kasashen yamma suka yaki musulumai suka 'yebe duk wani
alhwri da suke da shi,suka kuma tawarsa hadin kai tsakanin musulumai, ba a
gushe ba kuma na ta fama da wannan rabe raben kai da aka haddasashi,aka sami
mabiya wassu aqidoji da rassansu wanda ya kawo har Karin na sha daya bayan
hijira,a lokachin da kasashe Engla,fransa da potigal lamarinsu ya bunkasa wajen
yin mulkin Mallaka wa kasashen mutane da kuma 'yebe musu alherin kasashensu.
Musulinchi kuwa tinda yazo bai taba bawtar da mutane ba,su kuwa wa'yennan
kasashe sunzo wai za su wayar da mutane,wayarwan kuwa itache suna sasu sujuyewa
wa addininsu baya ba tare da sonsu ba,wannan kuwa ya jawo wassu sunyi ridda da kuma gushewa ta
khalifanchi a musulinchi har musulumai suka kasa tsare kansu balle kuma kare
wassu,wannan bautar da kasashe kuwa har yanzu anan anayinsa,kullum suna tinanin
ya za su sache man fetur sa kuma sauren albarkatun da suke kasahennan na
musulumai da suke tasowa,kuma suna tayin kokarin ya za su raba kawunansu,wannan
kuma lamari ne da ya ke tabbatacche.
Abubuwa da dama sun faru,wanda Suke sabi ne,malamai kuwa sun Sami sabani
kwarai wajen warwaresu,ko wani daya da yake tinanin shi malami ne idan bai sami
karbuwa ba sai ya kawo wata mazhabansa kawai dan yasami shahara,har muka Sami
kanmu wassu na chire wassu daga musulinchi sabo da sabanin ra'ayi kawai,wannan
bidia ta yadu chikin jamaa,idan kuwa ka karanta sofin littatafai za kaga chewa
yen uwanmu dake mazhabar hambali Allah ya ya shiryesu kuma ya jikansu suna
kafirtar da imam ibi hanifa,Imam shafi'i da kuma duk wani da ya saba wa
ra'ayinsu,sukayi nisa har suka kai ga suna jayayya kan chewa zayyu a aure mache
dake bin mazhabar imam shaf'i ko bazayyu ba,me laifinta?kawai dan tana bi shafi'i,karya dai iri iri ta bayyana,idan ma
kakaranta takardan Abdullahi bin imam Hamad da ibn mandah da sauransu za kasamu
suna chewa bayahude ma yafi imam Aba hanifa,da kwai ma wani chikinsu da yake
chewa "akwai wani mai suna muhammad bin Idris da za bayyana,yafi iblis
shari ga wannan al-umma"
Muhammad bin Idris kuwa shine imam shaf'i Allah yakara masa yarda babban
malamin qurayshawa.
Bayyanan fitintinu a addini
Way'ennan fitintunu suna da yawa kum sun kasu iri iri,da kwai fitinan
da'jfiyya wanda ta munana kwarai,da fitinan bangarewa da kuma tsananchi,da
fitinan Haraj da maraj,da fitinan leken asiri,da fitinan kin salihai bayin
Allah da waliyyayai da kiyayya riko wa bayin Allah ba tare da wani dalili ba
sai dai kawai dan son mulki da daniyya,da kuma zubda jini ba tare da wata
gaskiya ba,wanda ya haddasa abubuwa da yawa way'enda Muke fama da su har izuwa
yau,wanda kuma yafi chutar damu shin bin tafarkin dasa wa wassu kiyayya ga
wasu,kuma yawanchinsu sunayin haka daduk wani bangare da yake da babbanchin
ra'ayi da su kaman yadda khaqarijawa sukayi da sayyidna Ali,kuma sun kasanche
suna kafirtar da Ahlu-ssunna wal-jama'a da Asha'ira da maturidiyya duk da yake
wa'yenda suna bangare mafi yawa a musulinchi,Hakazalika suns kafirtar da sufaye
ba tare da wata hujja ba ko dalili kawai dai dan makiya musulinchi sun dasa
wata kiyayya a zukatansu gami da adalchin musulumchi da algerians.
A lokachin da Muhammad bin Abdul-wahhab ya bayyana Alumma ta kasanche ta
chikin rudani yana kama da yadda al-umma take rayuwa a you,kuma da'awansa da
kira da yayi izuwa tauhidi a kasar larabawa abune da duk wani wanda yake da
adalchi zai yaba masa akai,sai dai chewarsa dukkan al-umma bata kana tauhidi na
gaske magana che da baza a karanta
ba,idan kuma munma yarda da hakan to dama chewa yayi suna tabka bidia'a ba tare
da ya kafirta alumma ba da abin zayyi sauki ta inda za aiya yin gyera ba tare
da an rushes hadin kai da al-umma take da shi ba,amma yayi tsanani kwarai kuma
shi da mabiyansa musu tsanani da suke kan wannan tafarki na kafirtar da al-umma
abu ne da ayi tir da shi. Duk da yake ba dukkansu suke kan wannan ra'ayi ba
amma da deyawa chikinsu suna ganin chewa duk wanda yake da wani ra'ayi sabanin
nasu to kafiri ne duk yanda yakai a alimi da sanin addini da ibada,duk da yake
bai taba yin wata da'awa ba in ba ta tauhidi ba sai dai kash!da'awar tasa
tamkar dafi ne a chikin Zuma a ganin wayanchin malaman musulinchi sabi da
abubuwa da suka daukesu kafirschi ne da fita a addini ba wassu abubuwa bane
fache abubuwanda suke da tushe a musulinchi da imani kaman son waliyyayai da
slihan bayin Allah,da neman albarkansu da kuma son Annabi SAW da tabarruki da
shi,da ziyrar raudanshi,har takai da zakaga musulumi bazai iya fadin chewa na
ziyarchi Annabi ba sai dai wai yache na ziyarchi masallachin Annabi SAW, kuma
wa'yennan duka abubuwa ne da suke rassa ne a addini wa'yenda Annabi SAW yayi
nuni musulumi zai iya yinsu.
Mu muna ganin chewa Annabi SAW mutane sunyi tabarruki da shi,sunyi
tabarruki da yawunshi,sunyi da majinanshi,sunyi da gashinshi,sunyi da abubuwa
da yabari,abubuwa da yewa gasunan a bayyane duk kunsansu,kuma ba wanda yache
wanda sukayi tabarrukinnan mushrikai ne.Annabi SAW da kansa ya baiwa khalid
binul-Walid wani yankin hashinsa,ya kuma raba gashin kansa wa aba musa sa wassu
sahhabbai,duk mun San wannan,kuma kissar tazo a sahihul-bukhari da takardun
sira,suna chewa:
Lokachinda Annanbi SAW yayi layya sai ya kira mai aski ya aske kansa,sai
yache wa mai askin wanda shine m'ammar bin fahlaq bin Nadla bin Abdul-Aziz bin
Harsan bin auf,sai musulumai suka hallara suna bukatan abasu hashin,syayinda
shi mai askin yana kan yi masa aski,sai ya kallesa tache:ya kai m'amar Annabi
Allah yabaka amanan kansa yayinda aska ke hannunka,sai m'amar yache ya Annabin
Allah lalle kuwa wannan babban falala che a gardeni,sai yache dashi chi gaba,a
yayinda yake aske bangaren na dama,da ya gama,ya rarraba gashin ga wanda suke kusa
ashi,sai yayi nuni ga mai askin da ya aske bangaren Hagu,sai yache wa abu dalha
amshi.
Ibn sa'ad yache:ya aske kansa ya kuma rage gashin bakinsa,da sajensa,ya
kuma yanke farachensa,sai yache abinnne gashin da kuma farchen.
Bukhari ya rawaito ta wajen ibn sirin,Anas Allah ya kara masa yarda,yache
Annabi SAW da ya aske kansa abu dalha shine na farko da ya dauka daga
gashin,yache Wannan kuwa baya karau da riwayar Muslim,sabi sa yiwar chewa zan
iya yiwa Aba dalhan ya kebe ne da gashin gafe na dama,kaman yadda wassu suka
sami na gefen hagu.wannan gashi da Annabi ya raba wa sahabbansa kuma sun
kewayeshi dan su samu ba dan komai bane sai dai kawai dan tabarruki,to shin za
muche Annabi SAW ya na kira zuwa shirka ne ko kafirchi,kawai dai idan mutum ya
biye wa son rai zai iya fadan abinda yafi haka ma,tsanani yakai ga wassu suna
ganin duk wanda ya saba ra'ayinsu to ya kafirta,wassunsu kuwa yakai ga suna
chewa idan harma kayarda da kafirtaka sa sukayi ma shima wani kafirchinne,wassu
kuwa suka zo suna kafirtar da duk wani wanda ya zamo jagoran mutane dama wanda
suka yabasa suka yarda dashi,har sayyid qudb Allah ya rahimchesa yazo yayi
rubuche-rubuche masu irin wannan ra'ayi. Idan kahadashi da irin ra'ayin
Muhammad bin Abdul-wahhab za ka gane yadda Alummannan ta shiga chikin
rudani,kuma wannan shi ya haifar da abinda ake kira salafiyya a yau,wannan
abinda ta haifar suka tashi da wani
ra'ayi na chire duk wani musulumi daga musulinchi sai dai idan yana tare
damu,da kwai kuma wassu malamai da suka yi kokari kwarai wanda jagora mai
hukumchi za iya komawa ga ra'ayinsu amma an gushar dasu,suna nan amma da yake
antake afani dasu sun zamo tamkar ba sanan.
Turawa Mallaka kuwa sun taimaka kwarai sabi da wanda suka zo baya bayanan
baza su iya bin ra,ayin wanda suka gabata ba daga malama fiqhu,sabi da yana saba wa ra'ayinsu,sabi da
su malaman fiqhu da suka gabata duk wani ra'ayi da za sufada sai sun tabbatar
da shi da ayar alqura'ani ko kuwa hadisi,su kuwa wa'yennan sabin basu yarada da
hakan ba,sai muka kasanche a wani yanayi da mara ilimi yaka bada fatawa ba tare
da sami ba,wannan kuwa ya jawo bala'i mai yawa.
Shiri da makiyin musulinchi yayi dan ya gama da musulumi yayinda yake
gidansa
A lokachinda Kasa amarika taso rage wa duk wata kasa da take da karfin
musulinchi sabi da rage karfin musulinchi sai tayi anfani da yaran musulumai da
Suyaki tsarin Soviet na kasar Afganistan sai mutane suka ruga zuwa Afganistan
Amarikan tayi anfani da yaran musulumai da suje su yaki wannan tasari,bayan
wa'yennan matasan sunje suka koyi dabarun yaki da yadda ake anfani da makamai
da basa hannun mutanen da suke garin larabawa,har suka fara kashe-kashe
tsakaninsu ya kai da aka kashe shehi Abdullahi Azaam da yaransa,idan waninsu
yage wani yana anfani da wassu ayoyi dan ya kare kansa ma sai yache mar kai
mushiriki ne har dai wata kungiya ta
malamai ta tashi da kokarin sulhu da hada kan jama'a munayi Allah godiya wani
da yake da alaqa da lamarin yabani labari chewa ana chin nasara,sai yen Taliban
suka tashi da wani aiki wanda yake yawanchin ra'ayinnasu tana tafiya dai dai da
mazhabar hanafiyya sai dai sun kauche mar ta wajen tsaurin ra'ayi kan abinda
yake ba ginshiki bane a addini ba,abubuwa masu muhimmanchi da yakamata musulumi
ya damu da su kaman karfafa kanmu ta hukunche-hukunche da addini ya shirya mana
sai aka koma ana ta matsawa kan hijabi da kuma hana mache tayi karatun zamani
sai dai wai tayi ta zama a gida tayi wanki ta dafa abinchi da sauransu..ba
adamu da ra'ayinta ba bata da hakkin
taimakawa wurinda ta rayu chiki.
Su buza da kabil da banj shik da Nad da firauna da Haman da qaruna da wanda
suka bijire da ache suna da rabo da sun musulunta amma musulinchin sai Allah ya
qaddara ya so za kasamsa,wa'yennan mutane sun kasa samin hujaa sai chewa wai
musulumai sun kafirta suka rusa gunkunannan wanda hakan yasa turawa mallaka
suka sami daman kuntata wa musulumai da suke Amrika aka sa mutane su gujesu,
abin tsoro ne su,wannan kuwa abune da aka tsarashi tin tini.
Hakan ya sake tarwatsa musulumai wanda ya dache ache Amrika sojojinta suka
tura zuwa wannan yakin na Soviet, sabi da dokar musulinchi tazo ne dan saukake
hanya idan ka duba fadin Allah (kuyi temakekeniya kan Alheri da tsoron Allah
...)surar Almaida aya to 2
Musulinchi ya karrama mutum da musulinchi da tauhidi da ibada dai dai
gargado,Allah ya che (Allah baya daura wa wata rai wani aiki sai dai dai iyawanta ..)Baqara aya ta 286
A mua'amala Allah ya shar'anta son Alheri hakazalika yin Alheri wa dukkanin
dan Adam,da kuma kiyaye dan Adam da duk wani abu da zai chutar dashi.Allah ya
shar'anta duk halaye na Kirki da tsarkakken zuchiya,ya kuma nememu da mu
girmama kowa wajen bayarwa da karba,ya nememu da muzama tsarkakku domin
mukiyaye duk wani aibi domin muzamo karbabbo wajen Wanda ke arzutamu,ya kuma
nememu da yafiya da tausayawa a komai da baiwa ko wani mai hakki Hakkinsa.
Komawa ga maganan da mukeyi kan yadda Amrika tayi anfani da 'yayen
musulumai wajen yakar tsarin Soviet ina ma kuwa sabi da Allah sukayi
haka,yayinda suka rasa wa'yennan yara bayan sun koma Afghanistan sun rasa
mafaka daga yen Afganistan din sai suka koma Amrika da kasashen turai wanda
suke bin tsarin dimukradiyya,suka zamo mazauna a chan yayinda dewa daga chikin
wanda suke da ra'ayin siyasar musulumnchi suke chan tin da chan,sai Amrika
tafara tinanin fa wa'yennan da suka zamo mazauman kasarsu za su iya zama
barazana a garesu hakama Fransa,kama yadda akache Sarkozy ya taba chewa :bayan
shekara ashirin da biyar wato shekara ta 2025 za a iya samon shugaban kasa
musulumi a kasan,ko dai wata magana mai kama da haka,hakama Biritaniya taji irin
wannan tsoro,hakama Almaniya,da kasar Italiya,duk wa'yennan kasashen sun
tsorachi musulumai da musulinchi,tana kuma tsoron samin karuwar haifuwa da
akeyi a kasashen musulumai,ina kuma da wa'yenda sukayi hijira garesu,tana kuma
tsoron mallakan kasashen na ga albarkatun kasa kaman man fetur da sauransu da
kuama yaduwar musulinchi a ko ina.
Maysayin sufaya kan wa'yennan abubuwa
Munche maysayin malaman fiqhu da yake da tasiri kan Alumma kusan ya gushe
hakama sufaye,hakan kuma baya nufin chewa basanan kaman su sufaye kan za mu iya
chewa a yanzu sunfi ko wani bangare yawa a duniya sai dai rashin yunkurinsu
chikin Harkokin yau da kullum har yasa ana musu ganin basu taka kara sun karya
ba.
Idan muka duba sufanchi da ma"anansa na hakika za muga chewa sunfi
kowa yawa sabi da dukkanin masu hadisi daga mazhabobi hudunnan duk sufaye ne
suna kula da abinda wannan addinin ya kunsa chan chiki,hakama malaman fiqhu da
masu tafsiri,da dai dukkan malaman addini. Har ibnu taimiya da almajiransa
kaman ibnul qayyim da ibnu Rajab dakkanin malamansu sufaye ne kaman su ibnu
qudama da sauransu,takardunsu kuwa shaida ne kan abinda muke fadi,har ma wanda
yafara kafa tsarin na yen uwa musulumai ai bai da gaba da sufanchi ko sufaye
kaman yadda akasan da'awarsa chewa (da'awa che ta salaf ,sunna ,hakiakan
sufanchi,tsari na siyasa,tsari na motsa jiki,tsari na wayewa ta karatu,tsarin
kasuwanchi kuma tinani da jama'a za suyi).
Kawchewar wassu mabiyansu bazai chanza wannan maqasudin ba kaman yadda na
hadu da almajirinsa malam sa'id hawa a madina na yaba mar kwarai wajen bani
sura ta gaskiyar tafiyarsu Allah ya jikansa,wannan kuma yana tabbatar da chewa
wanda ya kafa wannan kungiya bai da wani adawa da sufaye idan ka karanta
abubuwa da suka wakana tsakaninsa da shehimmu malamin hadisi Muhammad Alhafiz
Attijjani a isma'iliyya za kasamu kissar a Wasikoki na sheik Albanna.
Zai tabbbatar da wannan rubutu da akayi a shekarun kafin Tawaye suka che
:Ba asan wani Abu kan yen uwa musulumai ba a shekara 1928 inda yayi rajistanta
a matsayin kungiya ta alheri dai dai suke da kugiyoyi na alheri na sufaye da
akasansu a wanchan lokachi,sai dai shi shugaban a ganinsa ya dache a che sufaye
ana dama duk wata harka ta yau da kullum da su.
Kuma shi Albanna ya kasanche a tasowarsa ya bin tafarki na Hassafiyya
shaziliyya na sufanchi,har ya kai da ya wajabta wa mabiyansa wazifa karama da
babbab ya kuma Sanya shi doka a kungiyar,a farkon ma kafuwanta,da kuma koyar da
takardun sufanchi akaman takardan hikimomi na ibn ad'illah da wasika ta
mustarshidin na Alharis Almuhasibi da mawahib Alladunniyya na qasdalani,da
al-Anwar almuhammadiyya na Annabahani,da Alrriisala Alqushairiyya da ihyaa
ulumuddeen da imam qazali da mukhtasar minhajul qasideeen na inb qudama
Almaqdasi,ya kuma kula sosai da yin bikin maulidi wanda yake tara jama'a kwarai
da tsari,yana kuma kula kwarai da nahiyar kulawa da azimi da juriya da hakuri
da yin bulala da yin sallan dare da hada yen uwantaka da tafi ta jini wannan
kuwa duk yasameshi ne daga sufanchi.
Da kunchin mulkin mallaka da harka ta siyasa ta bijiro a misra sai ya
mayadda mabiyansa zuwa tsarin na salafanchi wanda yafi damuwa da aqida da kuma
wassu abubuwa da suke sabawa da tsarinsa na farko wannan salon sabon ra'ayi
nasa yana tsabawa fadin Allah da sunna.
Sufaye a hakiaka suna da yawa da gaske idan ka ga sufaye mabiya darikar
fullaniyya Sunkai miliyan sittin,haka tijjaniyya da kadiriyya a Nigeria sun kai
miliyan sittin!miliyan sittin amma sai dai tasirinsu bai da karfi sabi da kalu
bale da suke fiskanta da ga makiyansu.
Hujjan wassu kuwa shine sufaye bai kamata ache suna tunani kan duniya ba da
ma mutane kai bai ma kamata su kula da yadda za sukiyaye addininsu da kansu,ya
bar mutane da abinda suke chiki shi dai kawai in wani ya rasu yazo ya
sallachesa bayan kuma Allah yana chewa (ya ku wanda kukayi imani kuyi hakuri
kuma ku jure kuji tsoron Allah saboda kusamu rabotuwa ) Ali-imran 200
Yache kuma (ku jajirche sabi da Allah shi ya zabeku ...)Anbiya 78
A wani ayan yache (Anyi wanda ake yakansu izini da chewa anchuchesu ..)Hajj
39-41
A wata ayan yache (ya ku wanda kukayi imani kuyi wa Allah da Annabinsa
biyayya kada kubijire masa Kuna masu ji ..)Anfal 20-21
A wani ayan yache (ya ku wanda kukayi imani kuzamo masu amsawa ga Allah da
Annabinsa idan har suka kiraku ga abinda zai anfaneku ....)Anfal 24-25
A wani ayan yache (ku shirya musu da abinda kuke da shi na karfi da dawakai
....)Anfal 60-61
A wani ayan yache (kada kuzamo chikin wanda suka manta da Allah sai
yamantar da su kawunansun ....)Hashr 19-20
Wannan ayoyi da hadisan manzon Allah da suke kira da jihadi da yin niyya da
mubaya'a Allah yana magana wa dukkanin muminai,tin da chan har gobe,bai kuma
kebe sufaye ba ko wassu daga duk wani bangare na musulumai,wannan kuma abu ne
da mukayi wasa da shi har muka sami kammu idan muke yanzu,ba wanta kasa daya na
musulumai da za kasamesu kansu hade
bayan kuma Allah ya hanemu da muguji hakan inda yache (kada kuyi jayayya
za ku rarrabu kuma za Kursa karfinku kuma kuyi hakuri..)Anfak 46
Allah ya ymarchemu da chewa duk inda muke yazamo chikknmu akwai masu yin
umrni da tin Alheri masu kuma hani daga sharri suna kira yazuww imani Allah
yana chewa (ya zamo daga chikinsu wata al-umma masu kira zuwa alheri suna kuma
hani daga yin sharri ..)Ali-imran 104-105
A wani ayan yache (kun kasanche mafi Alherin Alummu sabo da umurta da
alheri da hani daga sharri )Ali-imran 110
Allah ya umarchemu da takawa,kuma kada mumutu fache muna musulumai, ya kuma
nememu da mu hada kai ya hanemu kuma daga rarrabuwa,inda yache (ya ku wanda
kukayi imani kuji tsoron Allah tsoro na gaske kada kuma kumatu fache kuna
musulumai,kurriki igar Allah baki dayanku wajen hada kai kada kurarrabu ...)Ali
imran 102-103
Ya sake chewa (ya ku wa'yenda kukayi imani idan kukahadu da abokan gaba to
ku tabbata kukum yawaita zikiri sabo da kurabauta,kubi umurnin Allah da
Annabinsa kada kuma kuyi jayayya saboda za kuyi rashin dache sannan kurasa
karfi ...)Anfal aya ta 46-46
Lalle jayayya ta faru,to me muke Kira,sai rashin karfi da rashin
Daula,wannan shine abinda yake faruwa a dukkanin kasashenmu.
Shi yasa ya wajaba baki dayyammu da mukula,muyi aiki chikin nutsuwa a duk
inda muke sabo da addininmu ya samu nasara,muyi kokari mutuka wajen hadin
kai,ba babbanchi chikin wannan wajen kai Sufi ko wani abu daban,bai kuma kamata
musulumi ya raina kansa yache ni bazan iya wannan ba chikin wannan rudani mai
kama da ambaliya mai dauka mutane .
Lalle za ka iya ko da kalima mai kew da za kayi kuma tayi tasiri da
wani,duk inda kasami Kanka a waje sa ya kamata da mutane masu sanin ya kamata to kayi kokarin yin da'awa,da
hakan Allah zai bada muwafaqan fahimtan addini na kwarai,da zaban me ya kamata,
za kakuma yin dache da isar da imani wa wassu,musulinchi kuwa zai samu zama a
zukatan wassu,har sugane matuka wanda yake son musu alheri da wanda baya son
haka garesu.
Karuwa hatsarinda yanayin musulinchi yashiga bayan tawaye da akayi a
kasashen larabawa
Lalle gaskiya kuwa muna chikin hatsari Alumman musulumai sun chikin
hatsari,dubi yadda kasashen larabawa suka tabarbare a dalilin wannan tarzoma da
sunan neman inchi,Libiya,Misra,toh me dalilin wannan?shin da gaske ne sabo da
neman maye gurbin Masu hukunchi da zalinchi ne,to me dalilin kisan kai?idan har
ina da niyyan gina kasashen ne ?me ya kawo wannan kashe kashe ?me yasa za ayi
ta zubda jinin musulumai ba tare da dalili ba ?
Duk wannan zai ishi mutum tunani chewa da kwai wata badakala da aka shirya
don tarwatsa mu,idan har kana wani bangare a wannan irin yafiya to ba abinda za
ka iya yi,amma idan har baka chiki kuma kana bangare na tafarkin kira na Annabi
SAW to da ikon Allah za ka iya yin abu deyawa kuma Allah zai baka nasara mai
karfi.
Muna rakon Allah ya bamu dachewa baki dayyammu,kuma ina maraba da ku ,kuma
da ikon Allah chikin fahimta na kwarai dukkanin matsalolo da ke fuskantar
musulumai za su gushe,lalle kuwa hanyoyin kekkewan fahimta yana da yawa kwarai
a rasuwanmu ta yau,kada kuma kayi tinanin yau idan ka fadi magana kowa zai
karbeta daga gareka, yau ko Alqura'ani kake karanta wa baza a ji daga gareka
ba,ko a fahimta ba,ko wani daya yana da nasa ra'ayi,sabi da haka kai kayi nasihanka
ba tare da bachin rai ba,ka zamo mai karban kowa,haka ma kazamo mai hikima
wajen sauraran kowa har ka kai ga inda kakeso,ya na kuma daga hikiman Allah da
yasanya zukata a karkashin ikonsa ba karkashin ikon mutum ba duk yanda
yake,wanda kuma yake waswasi a chikinta shaidan ne,kai kuma za ka iya koransa
sa zikirin Allah,Allah SW yana chewa (wanda sukayi imani zukatansu na tabbache
da zikirin Allah lallae kuwa da zikirin Allah zukata ke tabbata)Ra,ad aya ta 28
Allah yasa mudache
Rufewa
Ya wajaba kanmu da muyi tinani kwarai kan Halin da al-umma tashiga,musamman
muhimmantu da wannan sabida makiyan Allah suna neman yiwa musulinchi fitina
babba,da sharri ma yawa kuma halinda Nigeria ta shiga na tabarbarewa!!!
Sunga yanda musulinchi ya bunkasa a Nigeria sai suka zabi Borno,itache Jaha
da muka fito daga ita,sabo sa tazama waje da za ayi wannan aiki a chiki,its che
kasa mai tsohon tarihin musulinchi,tana da masarauta mai girma ta
musulinchi,sun dade suna tinani akai sunyi ta kokari iri-iri,sabi da sun sha ziyartar
jahan suna muqabala da wassu shararru sai daga baya muka gane manufansu.
Makamai suna shigowa Nigeria ta ko ina da kuma yawa,mai dalilin hakan?bai
da wani ma'ana in ba yakar musulinchi ba,garuwan wannan da rashin tsaro a kasa
mai yawan Albarka kaman haka zai Sakata dole ta shiga hannun abokan gaba da
machuta,a yanzu kuwa Allah ya bayyanasu da bayyyanan wa'yennan rabe-raben kai
da muke gani a kasar.
Lalle kuwa tin Faruwan wannan abu basu abka mana mu sufaya masu bin
tafarkin salaf ko amatsayinmu na masu kira a zuwa addini,har ma wani lokachin
suna zuwa su mana bayani chewa su ba makiya addini musulinchi bane,kuma kar muyarda da abinda
wassu ke fada kansu amma lallai kuwa abu yanzu a fita daga hannun wa'yenda suka
san yakamata lalle kuwa ya dache muyi shiri.
Da kwai yen kwnata-kwanta da ke anfani da makamai da ake kira Boko haram,da
kwai yen siyasa da ke neman kauda abokan gabansu da wannan suna,hakama wassu
kristochi,haka kuma su ainihin yen Boko haram din,to kaga matsaloli za suyi
yawa .
Ma'ana Boko Haram
Ma'ananshi koyarwa da akeyi daga shekara ta farko zuwa shekara ta bakwai
wata matsayin primary,harma kuma koyarwa ta shekara bakwai a takaiche da suna
nufin koyarwa ta tsarin bature haramunne .
Wannan tsari kuwa yana kira ne zuwa tauhidi da jihadi,duk da irin
tsarinnasu yana da alaqa sa kasar jazayir,kaman su ansarudden,a Kasar Mali,da
ansarusshari'a wal islam a libiya,kaman na su kasar Sumali da yaman da wassu
kasashe,duk da suna da san babbanchi Allah dai shi ne da hukunchi,Allah ya
karemu daga dukkanin fitintinu wanda suka bayyana da Wanda basu bayyana ba.
Alhamdulillah
Tabarakallah