Takaitacchunn qasidu
Mufti na kasar Nigeria :Jamiar Azhar tabada gudun mawa kwarai wajen dakile masu tinanin ta'adsanchi
Babban shehin ma Jami'an azhar Dr Ahmad Tayyib yayi lale marhaban da muftin
Nigeria sheikh ibrahim saleh a inda yake karban manyan Bakinsa a Jami'ar
Shehin Azhar din ya kuma yabawa kugiyoyin yammachin Africa kwarai wajen
gudunmawa da sukeyi wa addini da kuma kulawa da duk wani abu da ya shafi addini
kuma ya kara da chewa wannan abu ne da suka dade Sunayi a tarihi,kuma malaman
yanki kwarai sun bada gudun mawa mai muhimmanchi dan chi gaban musulinchi
wannan kuma yana da alaqa da yadda suke bi sannu a hankali wajen yin da'awarsu
wanda hankan yasa kungiyoyin nasu suka sami chi gaba a tarihi.
Yache kuma Jama'ar tana iya kokarinta wajen yakar wanda suke da ra'ayin
ta'addanchi da kechewa kan hanya da kuma ra'ayin da bashi da tushe a
addini,hakan kuma yana Samuwun wanzuwa ne ta hanya dalibansu da suke yayewa yau
da kullum a Africa da yada manufofin addini na kwarai.
A wani gefen kuma shi muftin na kasar Nigeria ya bayyana chewa wannan irin
koyarwa lalle kuwa anan Nigeria ita aka kama kwarai kuma ita che ta samar da
wanzuwa alaqa tsakanin alummun a Nigeria da kuma dukkanin kasashen Africa.
Ya kuma yaba wa Jami'ar kan gudun mawa da take bayarwa ta wajen koyarwa da kira
wa musulinchi a kasashen Africa wanda ya temaka kwarai wajen kawchewa masu
tsatssawran ra'ayi da kuma taimakawa da suke wajen samun zaman lafiya tsakanin
musulumai a Africa.
A karshen zaman kuma muftin kasan Nigria ya sallamawa babbabn shehin
jami'an azhar din bugun Alquraani da kungiyar bayar da fatawa ta Nigeria za ta
qaddamar da shi a karshen watan Aprilu wanda kungiyar ta nemi wassu daga
Jami'ar ta azhar da su halarchi bikin na qaddamar da Alquraanin.