Takaitacchunn qasidu
Tsarin karatun tattalin arzikin Islama ya cimma burin mutane: Sheikh Ibrahim Salih - Mufti na Najeriya
Hadin kai A ala'adanche
Shin hadinkan masana da shuwagabanni yana baiwa musulumai dama na fiskantar
abubuwa da suke daminsu wa'yenda za su bata zamansu na lafiya a tsakaninsu?
Abun takaichi wannan hadin kai yana da wahalan samuwa a yanzu sai a wurare
kalilan,a yau muna fiskantar matsaloli na ala'adu na wani irin tinani na masu
tsaurin ra'ayi wanda suka mamaye wurare da dama a kasashen larabawa da wassu
kasashen musulinchi,kuma samuwan masu irin wannan ra'ayi kwarai yana bukatan
asamu hadin kai sabi da yawantan masu irin wannan ra'ayi ba karamin barazana
bache wa zaman lafiyammu da kasuwanchinmmu. Kwarai muna neman masu zirfin
tinani da su tsaya kwarai wajen samin zaman lafiya.
Musulumai suna samun karfi ta wajen basu fatwowi,to taya kake ganin musulumai
za su samu karfi a wannan duniya?
Musulumai za su iya samun karfi a dukkanin sassan duniya idan suka hada kai
sukayi aiki tare,za su samu karfi a kasuwanchinsu,hakama a fasahan kimiya, da
kuma karfi a zamantakewansu da chi gaba a komai,haka kuma karfi na suji wanda
zai tsoratar da abokan gaba Wanda suke kwadai mamaye kasashenmmu da alheri da
ke chiki.
Kuma sunnan Allah che a kasa chewa zai baida karfi ga wanda yayi aiki da
zai baiwa dalilan karfinnan, Wato hadin kai,amma Idan basuyi wannan ba to ba wani
chanji da zai faru,ya kamata mutashi tsaye wajen aiki da kuma yin karatu mai
zirfi sabo da samin chi gaba a fasaharmu na kimiya aiki na kwarai wanda yadache
da shi,kuma mukarfafa duk wanda zai aiki dan samun chi gaba,abin bakinchiki ne
samun marasa abun yi masu yawa a tsakanin musulumai ba'a kuma wani aiki a kai
sabi a kawadda wannan rashin aiki da zaman banza.
Musulinchi a addinine mai farfadowa da alummu da kuma samun chi gaba.
Me yasa musulumai kullum suke kukan talauchi,jahilchi,da kuma matsaloli na
rashin aiki a duk wurarensu na zama?
Kuma me yasa yawanchin kasashen musulumai suke fama da koma baya a chi
gaba?me kuma martani da za kayi wa masu hada wannan da koyarwa na musulinchi?
Hada wannan abubuwa da koyarwan musulinchi jahilchi ne,sabi da kana magana
ne akan abu da yake da alaqa da yanayin zamantakewa kasan kuma addinnmmu addini
ne mai farfado da al-umma da saman mata chi gaba sa wayewa,kuma chewan
musulumai suna chikin yanayi na rashin karfi bai da alaka na kusa ko na nisa da
addinin musulinchi, abinda yake samun musulumai na rashin karfi da chi gaba an
tabbatar da chewa duk rashin bin ka'idojin musulinchi ne yanda yake,sun bar
hanya madaidaichiya da ak shirya musu sabi da za ta basu karfin nasara sunje
suna neman warware matsalamsu a wajen wassu.
Neman mafita
Kayi maganan hanya da za abi wajen neman Mafitan matsaloli da ake
chiki,wani hanya ya kamata abi wajen warware wa'yennan matsaloli a ganinka?
Hanya da za abi a bayyane take kuma bata da wani sauyi, ya kamata mu bi
hanyoyi da suka dache wajen chi gaba ta hanyan neman ilimi,aiki,kwarewa chikin
aikin da kuma gaskiya,jagororimmu musulumai nauyi ne da ya rataya kansu baki
daya wajen sanin duk wani abu da yake gudana a kasashenmmu.Manzon Allah tsira
da aminchin Alla ya tabbata a garesa ya bayyana mana a wurare dayawa
muhimmanchi wannan dawainiya,tana chewa a wani hadisi," ba wani bawa na
Allah da zai motsa kafofunsa ranan Gobe kiyama fache ya ansa wa'yennan
tambayoyi guda hudu:shekaru da yayi a duniya me ya aikata chikinsu,samartakansa
ya yayinda,dukiyarsa ya yatarata kuma a ina ya salwantar da ita,na karshe kuwa
shine iliminsa yayi aiki da shi ko bayyi ba.
Wannan hadisi ya kunshi abubuwa muhimmai da yakamata dan Adam ya tashi dasu
a nan duniya,wanda ake nemasa da ya kaddamar da bayani kansu Gobe kiyama Gaban
Allah,wannan muhimman abubuwa sune: lokachi,aiki, Kudi, da ilimi.
Mua'amala a musulinchi
Hidima da kokari da kayi wajen fatawa da mua'amala da kayi ta hanyan
koyarwa...wani hange kakeyi wa mua'amalar musulumai a kasashen Afrika?
Musulumai a ko ina suna da dangantaka kuma suna da biyayya ga duk wani abu
da ya halatta da kuma wanda ya haramta, musulumai a daukakin Africa da kuma
kasarmu Nijeria musamman suna da lura kwarai a mua'amalarsu shi yasa ba sa
barin tambaya ko da yaushe kan halal da haram. Kuma suna da lura kwarai da son
yin mua'amala da bankuna da suke yin aiki bisa sharia'ar musulinchi,kuma muna
neman muga hakan ya yadu a dukkanin kasashen Afrika,kuma goyon baya da ake samu
daga daukakin al'umma abun yabawa ne,da yardar Allah kuwa irin wa'yennan
bankuna za yafara samunsu a kasashe da ba na musulumai ba,a kasashe na Afrika
dama sauran kasashen,my malamai kuwa ako da yaushe za asamu goyon bayammu dari
bisa dari kuma za muchi gaba da wayar da alu'mma kan duk wani abu da yake da
anfani wa rayuwarsu.
Ya make ganin chi gaba a mu'amalar musulumai a yawanchin kasashen duniya?
Mu'amalar musulumai abune na azo ayaba wajen kulawa da halal da gujewa ga
Haram,wannan kuwa abune mai muhimmanchi ga duk wani musulumi da yake da kishin
Addininsa,Kumma irin wannan mua'amal che za tasa mutum ya gujewa wa hatsari a
rayuwansa, zai kuma sashi yin godiya da duniya da yake da ita,kuma muna fatan a
samu moriyar hakam a dukkanin kasashen musulumai da na duniya,kuma muna ganin
chewar irin wannan mu'amala za ta yadu a ki ina,da yaduwanta kuwa za tasa a bar
duk wata gurbatacchiyyar mu'amala tsakanin jama'anmu na musulumai.
Fatawa Amana che kuma nauyi ne kan maj ba da ita,kullum kana gargadi ga
masu fatawa kan gujewa son kai,ya za muguje wa wa'enda suke bada fatawa ba tare
da ilimi ba?
Tabbas magana kan duk wani abu da ya shafi addini ba tare da ilimi ba abune
mai babban muni,kuma yawanchin kasashenmu sun shiga rudani ne sabi da irin
wa'yennan fatawowi,bai kuma tsaya kan wanda suke bada fatawa batare da ilimi
ba.
Babban musiban shine masu tsatssauran ra'ayi wanda suke bada fatawa ba tare
da ilimi ba suna kuma chakuda tsakanin halal da Haram,irin wa'yennan ya kamata
a yi muhawara da su ta ilimi ba ta hanyan karfi ba,sabi da a kiyaye musulumai
daga abubuwa da suke yadawa ta hanyan kafafon zumunta,ta yanda suke chanza
hankalin matasanmmu.
Ta hanyan wannan sananiyyan jaridar taka ina kira ga daukakin musulumai da
sugujewa irin wa'yennan fatawowi da basu da asali a addini,su zabi fatwowin
mutane da suke da ilimi na kwarai,kuma su Guji sauraran masu tsatssauran
ra'ayi,su kuma jajirche wajen bin fatawa da take dai dai da mazhabobi da aka
sani a addini.
Su zamo masu matsakaichin ra'ayi kuma su yada ra'ayi matsakachi.
A kasarka Nijeriya masu tsabanin
ra'ayi sun Samu nasara wajen ingizar da matasa da suka tada hankalin al'umma da
sunan addini?
Ina son intabbatar maka da sauran daukakin al'umman musulumai chewa
musulumai da suke madaidaichiyar hanya da son zaman lafiya sunfi rinjaye a
kasar Nijeriya,musulumai a wajenmmu a ko da yaushe suna gujewa ra'ayi mai
tsauri sai dai yen tsiraru da suka abin irin wannan ra'ayi,kuma kokarin mu
wajen shawo kan masu irin wannan ra'ayi muna chi gaba da shi sabi da mu tsare
hankulan sauran matasan na mu,muna nuna musu chewa musulinchi bai da alaka da wannan
abu.
Domin samun zaman lafiya shin yana da alaka da matsakaichin ra'ayi?
Bin matsakaichin ra'ayi yana da muhimmanchi kwarai wajen zaman lafiya ga
musulumai da suke Afrika wanda wannan yana nufin rashin samun wanda suke da
tsatssauran ra'ayi wanda suke batar da wanda basu da sani.wanda kuma hakan zai
samar da zaman lafiya a tsakanin al'umma,wajen sauraran juna ta hanyar koyarwar
addini da adalchi tsakanin yen Adam,kuma zai samar da jituwa da tausayi da
hadin kai tsakanin yen Adam da wannan kuma za asamu kare jinin da
Adam,dukiyarsa da kuma mutunchinsa,hakzalika za asamu ayyuka da za susamar da
chi gaba da hadin kai mai karfi.
Ya kake ganin hadinkai wajen bada fatawa a dukkanin makarantun addini a
duniya?shin hadin kai tsakaninsu ya Chinma manufofinsa da musulumai a ko ina
suke son gani?
Lalle kuwa a yanzu akwai hadin kai kwarai wajen bada fatawa a kasashen
musulumai,kuma muna fatan asamu chigaba a wannan,kuma Wannan hadin kai yana da
kew wajen musayn ra'ayi da samun Karin ilimi daga juna,dama samun kokari wajen
zirfafwa a binchike,kuma a ko da yaushe ina farinchiki wajen haduwana da babban
limamin Azahar da anfanuwa da irin shawarwari da yake bani. Da kwai dangantaka
mai karfi tsakaninmu da Jami'ar Azhar.
Ya kake ganin matasa da suke zuwa karatu Azhar,shin kana ganin za asamu
kishi a wajensu wajen yada da'awa da fatawa bayan komawansu ?
Godiya ta tabbata ga Allah,muna da tabbachi kan azhar da irin horo da take
bayarwa a karatu shi yasa ko da yaushe muke da kishin muga muntura ya ranmu
izuwa chan,sabi da suyi karatu su kuma sami furarwa Wanda za ta basu karfin
gwuiwa,kasan yin da'awa yana da sauki kan yin fatawa,ana neman mai bada fatawa
da yazama ya san ra'ayin malamai kan matsaloli na da da na yanzu,wannan nauyi
ne da yarataya kan wanda suke da ilimi mai zirfi a malamai.