Fatwa
Mata a Gomnati
Matsalar kasanchewar Mata a aiki na gomnati abune da aka Dade ana che-che kuche a kai tsakanin malamai a dukkanin fadin duniya. Za mu iya chewa kuma wannan jayayya ta fara ne tin zamanin Khalifa na farko sayyudna Abubakar (RLA). A halin yanzu wanna abune da yake da hadari a duk nahiya da musulumi ke da Karfin mulki a kasata. Nigeria,sabi da haka wannan abune da yake bukatar fatawa mai Karfi da za a dogara da ita.
Da sunan Allah Mai tsarki mai rahama. Tsira da aminchin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu da alayensa da sahabbansa baki daya.
Matsalar kasanchewar Mata a aiki na gomnati abune da aka Dade ana che-che kuche a kai tsakanin malamai a dukkanin fadin duniya. Za mu iya chewa kuma wannan jayayya ta fara ne tin zamanin Khalifa na farko sayyudna Abubakar (RLA). A halin yanzu wanna abune da yake da hadari a duk nahiya da musulumi ke da Karfin mulki a kasata. Nigeria,sabi da haka wannan abune da yake bukatar fatawa mai Karfi da za a dogara da ita.
Wassu malamai suna da ra'ayin chewa musulunchi bai bawa
mache da ta shugabanchi wata ma'aikata ba a gamnati,suna kuma kafa hujja da
ayannan ne da kuma hadisin Manzon Allah tsira da aminchin Allah ya tabbata a
gresa .
Wassu malaman kuwa suna da ra'ayi chewa mache za ta iya aiki
a ma'aikatu na hukuma tare da kafa hujja da wannan Aya da hadisin Manzon Allah
tsira da aminchin Allah su tabbata a garesa. Ana kuma yawan yi mana a wannan
tambaya a jihohin Nigeria da muyi musu bayani kan ma'anan wanna a'ayoyi da
wa'yennan malamai suke kafa hujja da su. Masu chewa zayyu da masu chewa bazayyu
ba mache tayi aiki a gomnati.
Shi yasa muna ganin chewa wanna abune da yake da muhimmanchi
a rayuwammu ta yau da kullum yayinda muke samun chi gaba a siyasa,
demokradiyya,da kuma abubuwa da suka shafi gomnati. Za muyi kokari Kwarai insha
Allahda muyi bayani a wannan littafi kan hukumchin da ya shafi wannan lamari
dai dai gwargwado da ilimi da Allah ya bamu.
Muna fatan kuma wannan fatwa an anfana da ita da irin niyya
da muka dauka wajen yinta, Wanda shine matsalar aikin mache a gomnati. Allah ya
amshi wannan aiki ya kuma yafe mana duk wani kurakurai da za mu iya yi chikin
aikin,kaman yadda muka sani duk wani mutum mai kuskure ne. Allah shine masanin
komai.
SHEIK SHARIFF IBRAHIM SALEH AL-HUSAINY,CON
Da sunan Allah mai tsarki mai jin kai,tsira da aminchin
Allah ya tabbata ga Manzon Allah Muhammadu SAW da aalayensa da sahabbansa baki
daya.
Malamai da suke da ra'ayin chewa mache baza tayi aiki ba a
ma'aikata ta gomnati suna chewa musulunchi bai baiwa mache daman yin hakan ba
suna kuma kafa hujja da ayannan (الرجال قوامون على النساء)
"Maza su ke da hakkin kare Mata da kulawa da su"
Suna kuma kafa hujja da hadisi da Bukhari,Tirmizi da Ahamad
suka rawaito Wanda Abi Bakrata yake chewa lokachinda labarin rasuwar kisra
sarkin Farisa ya Sami Annabi SAW,ya tambaya wa yane magajin sarkin?akache mar
yersa che mai suna Bauran. Annabu SAW yache :duk mutane da tazamo jagorarsu
mache che to baza su Sami nasara ba.(an rawaitosa a Bukhari)
Gomnan jahar yola ya Nemi ayi bayani kan wannan matsalar da
ma'anan wannan hadisi.
Za mufara da ayannan da ake kafa hujja da ita daga
suratunnisa'i, ayan tana bayani ne kan yadda maza ya kamata su kula da iyalansu
su kuma karesu,Idan ka karanta ayan kaman haka ma'anan zai bayyana maka,(الرجال
قوامون على النساء بما فضل الله بعضهم على (بعض وبما اتفقوا من أموالهم
"Maza sune masu kare Mata suba basu kulawa sabi da
yadda Allah ya sa su kula da chiyarwarsu, wannan kuwa ya kunshi Mata da aka
aura da kuma Wanda ake da dangantaka da su,sabi da haka ayar bata magana kan
shugabanchi.
Allah bai ban banta tsakanin na miji da mache ba sai a wassu
wurare na bauta,karantarwa,imani,da hukunchi,sai dai Inda suke da banbanchi a
halittarsu,kaman a wajen kulawa da yara da shayar da su,hakama wajen Sallah da
azimi sukan yi bayan sunyi tsarki ko kuma yayinda suke jinin Biki.
Allah ya dai daita stsakanin na miji da mache a ayyuka na
addini, misali duk inda Allah ya ambachi muminai maza sai ya ambachi Mata,kaman
yadda yazo a suratul-Hadid aya ta 28
يا أيها الذين
ءامنوا اتفقوا الله ءامنوا برسوله...
Ya ku Wanda kukayi imani kuji tsoron Allah kuyi imani da
manzonsa..
Hakama a yayinda yake ambatan 'yayen Adam a aayoyi dayawa
misali
يا أيها الناس انا
خلقناكم من ذكر وأنثى وجعلناكم شعوبا وقبائل لتعارفوا...
"Ya ku mutane mun haliccheku ne daga na miji da
mache....." suratul hujuraat :13
)ولقد كرمنا بني ءادم وحملناهم في البر والبحر )
"Mun daukaka yayen Adam ....)suratul isra'i :70
A wassu wurare kuwa yana amabatan jinsi na Mata da maza a
tare,kaman a suratul-Ahzab :
إن المسلمين
والمسلمات والمومنين والمومنات.....
Hakazalika Allah ya daidaita tsakanin Mata da maza a wajen
adduaa garesa kaman yadda yazo a surara Aali imran aya ta 193 da 194
ربنا اننا سمعنا
مناديا ينادي للايمان أن ءامنوا بربكم فئامنا.......
Haka kuma Allah ya amsa Adduasnu a wannan Aaya
"فاستجاب لهم ربهم اني لا اضيع عمل عامل منكم من ذكر أو أنثى
بعضكم من بعض..
A takaiche,aya na farko da mukakawo ta nuna yiwa zaban
jagora a a chikin Iyali, yayinda aka baiwa Mata hakkin kulawa,chiyarwa,da duk
wani taimako wa Mata da suke chikin zuria'a, sabi da haka ayan bata da Alaka
kan maganan shugabanchi a hukuma.saura
aayoyin kuwa suna dai daita tsakanin Mata da maza duk da banbanchinsu a halitta,
Sai mukoma kan hadisi da ko da yaushe ake kafa hujja da shi
kan hana mache zama jagora a siyasa ko wani ofisi na hukuma,sabi da mufahimchi
ma'anansa sosai Ababakrata Allah ya yarda dashi yana chewa lokachinda labarin
rasuwan sarkin farisa ya Sami Annabi SAW ya tambaya Wayene zai gajeshi,aka che
mar 'yarsa mai suna Bouran itache za tagajesa, sai Manzon Allah SAW yache لن يفلح
قوم ولو أمرهم امرأة
"Baza suyi nasara wa'yenda mache take jagora
garesu"
Karin Mubada ra'ayinmu kan wannan hadisi bari mubda bayanin
malamai da suke ganin chewa hadisin ba sahihi bane.
Wa'yennan malamai sunche Ababakrata ya rawaito hadisinne
bayan fitinan yakin rakumi kan sayyada Aisha ya Taso, Wanda mutanen da ke tare
da ita akayi galaba akansu. Sukache mai yasa bai rawaito hadisin ba sai bayan
shekara ashirin da biyar.
Bari mufara da chewar hadisin ya na banbanchi wajen Wanda
suka rawaito da kuma yanayin magana da yakunsa,ga kuma bayanin yadda
wa'yennan banbanche banbanchen da suke
chiki
1. Bukhari ya rawaito wannan hadisi a littafin fitunu,yache
Muhammad bin almuthanna ya rawaito mana chewa Khalid Dan alharth ya rawaito
mana chewa Hamid attaweel ta hanyan Alhassan ya fada mana chewa Abi Bakrata
yache Annabi SAW yache:
لن يفلح قوم ولو
أمرهم إمرأة
2. Abu isa Attirmizi ya rawaito a hanya mai kama da haka ya kuma
kara da chewa wannan hadisi Hassanun ne kuma sahih kuma riwayarsa tana da
inganchi
3. Imam Annasa'i ya rawaito wannan haidisi a Babin alkalai a
hanya kaman wadda ta gabata .
4. Imam Ahmad ya rawaito wannan hadisi a littafin zawad
Almusnad chewa, Abdullahi yache: banana ya fada min chewa yahya ta hanyan
uyaina yache min : banbana ya fada min ta hanyan Abi Bakrata chewa Annabi SAW
yache
لن يفلح قوم اسندوا
أمرهم إلى امرأة
5. Abdullahi yafada mana chewa,babansa yafada mar chewa Aswad
bin Ameer ya fada mana chewa Hammad bin Salama ta wajen Himed ta Alhassan ta
wajen Abibakrata chewa Annabi SAW ya che :-
لا يفلح قوم تملكهم
امرأة
6. Abdullahi yafada mana chewa,babansa ya che mar Muhammad bin
Bakr ya fada mana chewa,Uyaina ya ji ta babansa chewa Abibakrata ya che ,yaji
Annabi SAW yana chewa
لن يفلح قوم اسندوا
أمرهم إلى امرأة
7. Abdullahi yache mana,Babana ya fada min Yazid bin Harun chewa
Uyayina ta wajen babansa yaji Abibakrata yache Annabi SAW yana chewa :-
لا يفلح قوم اسندوا
أمرهم إلى امرأة
8. Abdullahi yafada mana chewa babansa yafada
musu chewa yazid Bin harun ya che,Mubarak bin Fudala ta hanyan Alhassan yache,
Abibakrata yache Annabi SAW yache :-
لا يفلح قوم تملكهم
امرأة
9. Abubakrata ya che ,Annabi SAW ya che :-
ما افلح قوم يلي
أمرهم امرأة
Aganinmu Bama shakkan inganchin wannan hadisi
yanayin yadda Wanda suka rawaito suke da yawa abinda ya rage shine sharha kan
yadda hadisin yazo da yanayin da yazo chiki
Abu na farko da yakamata Mugane shine wannan hadisi yana bayani
ne kan jagorchi da ake Kira al-imama al-kubra ko kuma al-khilafa al-kubra a
musulunchi, Wato matsayi mafi girma a musulunchi, shi kisra irin matsayi da
yake kai kenan kuma irin wannan ne Annabu SAW yake ishara garesa.
Wannan irin matsayi da ake Kira imama shine Wanda a
musulunchi ake bawa Wanda yake kai karfi kuma ba baiwa kowa sai Wanda yake da
sani kwarai Wanda zai iya hukunchi ba tare da koma yana neman taimakon wani ba
akan komai,yana kuma sulhunta tsakanin marasa jituwa da kulawa da dukkanin inda
musulumai Suke,kuma dole yazama yana da sani kan duk wani ilimi na musulunchi d
shara'a.wannan imama da muke magana kai ko tasha banban da duk wani matsayi da
ake maganan akai na siyasa a you,khilafa ko Khalifa a musulunchi yanayi ayyuka
ne da suka shafi :-
1. Shine na gaba da kowa dake da karfin iko Wanda duk umurni
dole ne masu bada hukunchi da wazirai da sauran mutane subi,basu da kuma wani
ikon bijire ma umurninsa.
2. Yana da ikon ya Sanya dokoki dai da ka'idoji na
musulunchi ba kuma mai irin wannan ikon sai shi
3.ya kuma matsayin Alkalin Alakalai Wanda duk sauran suna
kasanshi
A irin wannan imama ta musulunchi shi Khalifa yana zaban
Wanda za su taimaka masa,da masu basa shawara, a lokachin da aka rasa sa masu
zirfin ilimi da sani za su zauna suzabi mafi chanchanta. Masuyin wannnan kuma
dole ne su duba wa'yennan abubuwa:-
1. Ya zamo na miji
2. Ya zamo yayi karatu mai nisa
3. Ya zamo yana da adalchi chikin duk abinda yake
4. Yazamo yana da karfin hali kuma mai nazari chikin
halayyansa
5. Yazamo mai kaifin basira
6. Ya zamo amintacche
7.Wanda yake wannan matsayi na imama zai bar matsayinne
yayinda wa'yennan abubuwa suka faru misali:-
1. Idan ya rasu
2. Idan ya haukache
3. Idan yayi Rashin lafiya da bata gushewa
4. Ko bai da adalchi a ayyukansa
5. Idan ya bar ka'idoji na musulunchi
6. Idan ya bar koyarwa ta musulunchi. A takaiche shugabanchi
na imamama shugabanchi ne Wanda Annabi SAW ne yafarashi sai sahabbansa khulafau
suna suka chi gaba da shi,hakazalika a sokoto anyi irin wannan shugabanchin mai
na Borno,bai gushe ba sai bayayn zuwan mulkin mallaka, yanzu sai Saudi Arabiya
ne take irin wannan shugabanchi.
Muna son mujawo hankalin yen uwa sugene chewa ayannan na
suratunnisa'i tana magana ne kan shugabanchi na namiji-matarsa-da alaqa ta
zuria'a da kuma yanda na miji ya kamata ya taimaka wa matarsa da duk wata mache
da yake da alaqa da ita,sabi da haka ayan bata da alaqa da yadda mache za ta
iya zama jagora ko ta ra rike wani matsayi a gomnatanche,muna da ministochi da
councillors na kananan hukuma da ma sarakuna Wanda suna aikin wa Jamaa na yau
da kullum. Duk mache da za ta riki wani matsayi ko ta zama jagora dole ne ta
siffantu da wa'yennan abubuwa masu zuwa:-
1. Ta zamo bata tarayya da wani na miji da na muharraminta
ba,ko tayi lafiya da shi
2.ya kamata ta Sanya tufa da za ta suturtatata suturtawa ta
musulunchi
3. Baza tayi duk wani aiki da Yashafi wakoki da kide-kide da
akeyi ba
4. Baza ta rabawa ma'aikiata da suke wajen duk wani Abu da
Yashafi kayan Maye ko abinchin da yake haramtacche ne
5. Za ta girmama iyayyenta mmijinta kuma ta tabbatar da
chewa yaranta basurasa tausayi na uwa ba.
6. Za ta kula da duk wani Abu da zai kawo rudani tsakanin
iyalinta
7. Ta Sami ilimi da yadache musuluma ta sani Kan hani da yi
na musulunchi
Kaman yadda muka bada fatawannan Chewa mache za ta iya duk
wani aiki da bai Sabawa sharaa ba sai dai kawai babbban khilafa ok imama haka
ma salafussalih sukayi,za ta iya zama alkali yadda musulunchi yabada dama
tazamo shaida a kotu.
Ibn Jarir Attabari dai yana da ra'ayin chewa mache za ta iya
rike duk wani matsayi har ma imama amma wanna ra'ayi yawanchi malamai suna tsabani da shi,sabi da ra'ayin
yayi karaw da hadisin da Abibakrata ya rawaito.
Dr Abdul kabir Almadgari na Morocco yayi bayani akan wannna
matsala a lottafinsa da ke magana kan shugabanchi mache shafi na 239 chewa
"ba ma matsala mache ta rike duk wani matsayi sai dai matsayin imama ne
bazayyu ta rike ba,sabi da musulunchi ya baiwa mache Daman ta nuna basiranta a
duk wani matsayi fache na imama,za ta iya zama shugaba a wata
ma'aikata,malema,malakar jami'a, ok shugabar jami'a,soja,matukiyar Jirgi ta
sama ko ta kasa,maga takardar majalisa,.
A karshe muna son a sani chewa ba banbanchi tsakanin matche
da miji a musulunchi. Kuma wannan hadisi na Ababakrata yana magana ne kan
Babban khilafa na dukkan al Ummah,mu sani kuma hadisin bai hana mache ta rike
wani ofisi na siyasa a Nijeriya ko kuma duk wata kasa da ta ke da shugabanchi
mai kama da haka sai dai yakamata ta kula da duk sharruda da mache ya kamata ta
sani a musulunchi.