Takaitacchunn qasidu

Huduba kan maulidin Annabi Muhammad a Da'irar sa mai Albarka - Gwang District, Maiduguri, Nigeria

admin November 27, 2020 المؤتمرات

Ina neman tsarin Allah ya kare ni daga shaiɗan jefaffe

Ina kuma farawa da sunan Allah mai yawan rahama da jinƙai.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda aka aiko shi domin ya zama rahama ga ɗaukacin halittu, shugaban na farko da na ƙarshe, baiwar rahamar da Allah ya yi wa halittu kyauta da ita, cikakkiyar ni’imar da ya kwararo daga Allah, shugabanmu Annabi Muhammadu ɗan Abdullahi, da Alayensa masu tsarki, masu izza da daraja, da Sahabbansa maɗaukaka, masu fararen fuskoki, da waɗanda suka so su, suka kuma bi su, suka taimaka masu har zuwa ranar da wanda ya bi turbarsu da shiriyarsu zai sami babban rabo.

Mai girma wakilin gwamnan jahar Barno, Farfesa Baba Gana Umara Zulum, wanda malam …………….. ya wakilta.

Mai alfarma Alhaji Dr. Abubakar Bn Umar Garbi al- Kanemi, wanda malam ………… ya wakilta.

Masu girma wakilan ma’aikatun gwamnati a fagage mabambanta na jahar Barno.

Masu girma malamai da muƙaddamai da shugabannin ƙungiyoyi da cibiyoyin Musulunci.

‘Yan uwanmu da ‘ya’yanmu a wannan zawiyya tamu mai albarka, maza da mata, manya da yara, manyan baƙi:

Assalamu alaikum wa rahmatulLahi wa barakatu

Wannan lokacin na murnar haihuwar Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a wannan shekara (1442 / 2020) ya zo ne a lokacin da duniya tun rabin farko na shekarar hijira, da rubu’in farko na shekarar miladiyya har zuwa yanzu ake samun wasu sauye- sauye a duniya baki ɗaya, sauye – sauyen da suka yi tasiri a rayuwar ɗaukacin bil’adama, ba su bar kowa ba, babu wata ƙasa da ba ta shafa ba, lallai kun ga irin tasirin da annobar Korona Bairos (Covid – 19) ya yi a dukan ƙasashe, mafi yawan muhimman maslahohin mutane sun tsaya cak saboda wannan annoba.

A wannan lokacin ina roƙonmu duka, da mu nema wa waɗanda da muka rasa rahamar Allah, mutanen da suke da girma da daraja a wurinmu, waɗanda suke sahun waɗanda suka fi amfanar al’ummar Musulmai cikin manyan halifofi, da malamai, da shugabanni, da jagororin kira zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki, da sarakuna, da masu sarauta, da shugabannin ƙasa a dukan fagage, a jahar Barno da ma a zawiyyarmu mai albarka ta Maiduguri, da ma ƙasarmu Najeriya baki ɗaya, da Senegal, musamman Khalifan Sahihubul Faidhar Tijjaniyya, Maulana Sheikh Ahmad Tijani ɗan Sheikhul Islam Maulana Alhaji Ibrahim Niass, da ‘yar uwarsa mai daraja Sayyida Faɗimatuz Zahra, da ɗan uwansa mai girma Sheikh Mukhtar Allah ya ƙara yarda da su, ya kuma yi masu rahama baki ɗaya. Haka ma da iyalan gidan mai girma Khalifa Abubakar Siy, da abokanmu a garin Tawan, da Mauritania, da Cote d’Ivoire, da Chadi, da Central Africa, da Cameroun, da Niger, da Gambia, da Comoros, da Sudan, da Morocco, da Misra, da Libya, da Syria, da Kuwait, da Yaman, da Algeria da dukan waɗanda suka koma zuwa ga rahamar Allah Maɗaukakin Sarki a wannan lokaci mai tsananin wahala a sauran ƙasashen duniya.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masu, ya kuma yi masu rahama baki ɗaya, ya kuma azurta su da shahada, ya kuma yi masu ni’ima da irin abin da ya yi wa Annabawa, da siddiƙai, da shahidai, da salihai ni’ima da su, lallai abu ne mai matuƙar kyau waɗannan su zamo abokan zama. Lallai waɗannan masibun suna da girma, kuma suna bibiyan juna, amma dai abin da Allah ya ƙaddara shi ne zai kasance, babu wanda ya zai iya hana shi aukuwa, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: ((Dukan rai zai ɗanɗani zafin mutuwa, za kawai a ba ku ladanku ne a ranar alƙiyama, duk wanda aka nesanta shi ga barin wuta, aka shigar da shi aljanna, to kuwa lallai ya sami babban rabo, lallai rayuwar duniya ba komai ba ce banda tarkace mai ruɗi)) [Ali Imran: 185], ((Lallai dukanmu mallaka ne na Allah, kuma dukanmu wurinsa za mu koma)).

Wannan shi ne yanayin duniya kaman yanda Allah Maɗaukakin Sarki ya sifanta ta a cikin gagara gasan littafinsa da cewa: ((Ai misalin rayuwar duniya tamkar ruwan da muka saukar daga sama ne, ya kuma cakuɗa da tsirran da suke ƙasa cikin wanda mutane da dabbobi suke ci, kai har sai ƙasa ta yi ado ta ƙawatu, mutanen cikinta ma su zaci cewa su ne masu faɗa a ji a komai nata, sai hukuncinmu ya auko mata da daddare ko da rana, sai mu mayar da ita a girbe kaman ba ita ne a jiya ba, da haka muke bayyana ayoyinmu ga mutanen da suke tunani)) [Yunus: 24].

A wani wuri yana cewa: ((Ka buga masu misalin rayuwar duniya wadda tamkar ruwan da muka saukar ne daga sama, ya kuma cakuɗa da tsirran da suke ƙasa sai daga baya ya zamo karmamin da iska take sheƙi da shi, Allah da ma can Allah mai cikakken iko ne akan komai)) [al- Kahfi: 45].

Ya ‘yan uwana masoyan Allah,

Lallai annobar Korona (Covid- 19) ta shafi dukan duniya, mu a matsayinmu na masu imani da Allah muna kallonta a matsayin runduna ce daga cikin rundunonin Allah Maɗaukakin Sarki, da ke nuna cikan ikonsa da gagararsa, ba tare da la’akari da sauran fassarori ba, muna roƙon Allah mai girma da ɗaukaka ya yaye wa duniya wannan annoba. Sannan kuma wasu bala’o’in suka ƙara ƙaruwa ta hanyar rashin tsaro a wasu yankuna na ƙasarmu Najeriya, da ma ƙasashe masu yawa, laifuffuka iri- iri suka yaɗu kaman fashi- da- makami, da sace mutane domin neman fansa, da fyaɗe, da aukawa dukiyoyin gwamnati da na ɗaiɗaikun mutane, musamman a ‘yan baya- bayan nan, kai nau’o’in ɓarna dai sun riga sun bayyana a ko’ina kaman yanda Allah Maɗaukakin Sarki yake cewa: ((Ɓarna ta bayyana a tudu, da ma a kogi sakamakon abubuwan da mutane suka aikata, domin Allah ya ɗanɗana masu wani sashe na abubuwan da suke aikatawa ko za su koma zuwa ga Allah)) [ar- Rum: 41].

Ya kamata kada mu manta cewa lallai Manzonmu mai girma da karamci (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya riga ya bayyana duk abubuwan da za su bijiro wa ɗan Adam a wannan zamani namu tun lokacin da aka aiko shi, Hadisai masu yawa sun zo akan haka, a ciki akwai Hadisin da Imam Muslim ya kawo a cikin littafinsa, daga Abdurrahman Bn Abdu Rabil Ka’abati (Allah ya ƙara yarda da shi) ya ce: Na shiga Masallaci, sai ga Abdullahi Bn Amru Bn al- As yana zaune a inuwar Ka’aba mutane sun zagaye shi, sai kuwa na zauna a inda yake, sai ya ce: wata rana mun yi tafiya tare da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), a cikinmu akwai wanda yake gyara bukkarsa (da aka yi da gashin dabbobi), a cikinmu kuma akwai wanda yake wasan harbi, akwai kuma wanda yake cikin ayarin ba shi da wurin kwana, a lokacin sai muka ji sankiran Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana shelar: lokacin sallah ya yi (haka ake faɗi idan ana buƙatar mutane su taru domin wani abu muhimmi, ba wai lokacin yin sallah da aka ambata ake nufi ba), duka sai muka haɗu a wurin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), sai ya ce: (Lallai babu wani Annabi cikin Annabawan da suke gabace ni face ya zamo masa dole ne ya shiryatar da al’ummarsa zuwa ga mafi alhairin abin da zai kawo masu gyara, ya kuma yi masu gargaɗi akan sharrin da ya san zai same su. Ku sani lallai wannan al’umma taku an sanya mata alhairanta a farkonta ne, da sannu bala’i da abubuwan da kuke ƙi za su same ta a ƙarshenta; fitintunu su zo, wata tana sauƙaƙa wata, fitintunu za su zo har Mumini ya ce: wannan ne halaka ta, sai kawai ta kwaranye, sai wata fitinar ta zo, ya ce: wannan ne, wannan ne.. Duk wanda yake son a nesanta shi ga barin wuta, ya shiga aljanna, to ya yi iya yinsa har mutuwa ta riske shi a halin yana cikin imani da Allah da ranar lahira, ya kuma riƙa yi wa mutane mu’amalar da yake son su yi masa. Duk wanda ya yi wa wani shugaba mubaya’a, ya miƙa masa ragamar jagorancinsa, to ya yi masa biyayya daidai iyawarsa, idan wani ya zo zai yi rikici da shi akan shugabanci, a kashe ɗayan), sai na ɗan ƙara gusawa kusa da shi, na ce masa: Kai ka ji wannan maganar daga Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam)? Sai ya kai hannayensa zuwa kunnuwansa da zuciyarsa, sannan ya ce: Kunnuwa sun ji daga gare shi, zuciya ta kuma ta kiyaye. Ya ce: sai na ce masa: ga ɗan baffanka nan, Mu’awiyya, yana umurtanmu da mu ci dukiyar juna akan ɓarna, mu kuma kashe junanmu, alhalin Allah yana cewa: ((Ya ku waɗanda kuka yi imani da Allah, kada wani sashe naku ya ci dukiyar wani sashe ba tare da haƙƙi ba, sai dai ya halatta ku yi kasuwanci a tsakanin ku, ta hanyar yarda, kada ku yarda ku halakar da kawunanku ta hanyar saɓa wa umurnin Ubangijnku, kada wani ya yarda ya kashe ɗan uwansa, babu wani rai da yafi wani, lallai Allah mai yawan tausayinku ne a koda yaushe)) [al- Nisa’i: 29]. Sai ya yi shiru na ɗan wani lokaci, sannan ya ce: ka yi masa biyayya a wurin yi wa Allah biyayya, ka saɓa masa a cikin saɓon Allah.

An ruwaito Hadisi daga Abuhuraira (Allah ya ƙara yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Na rantse da wanda rayuwa ta take hannunsa ba za a yi tashin alƙiyama ba har sai alfasha da rowa sun bayyana, a amince wa maha’inci, amintacce kuma ya yi ha’inci, a kashe “al- wa’ulu”, “at- Tuhutu” kuma su bayyana. Suka ce: ya Manzon Allah, mene ne “al-wa’ulu?” Sai ya ce: (Fitattun mutane masu daraja, waɗannan za su kau, wane ne kuma zai yi saura? Su ne: at- Tuhutu). Sai ya ce: (at- Tuhutu su ne waɗanda suke ƙasa; mutane ba su ma sansu ba)!.

Imam Abu Isah at- Tirmiziy ya kawo a cikin littafinsa ya ce: Abdu Bn Humaid ya ba mu labari daga Hussain Bn Aliyu al- Ja’afiy, daga Imam Hamza az- Zayyat al- Muƙriy, daga Abu al- Mukhtar, daga ɗan ɗan uwan Harisu al- A’awar, daga al- Harisu Bn Abu Usama al- A’awar ya ce: Na bi ta Masallaci, sai na sami mutane suna magana akan mas’alolin saɓani, sai na zo wurin Amirul muminina; Aliyu Bn Abuɗalib (KarramalLahu wajhahu), na ce masa: Ka ga mutane suna kutsa kawunansu cikin mas’alolin saɓani –yana nufin mas’alolin da akwai saɓanin fahimta akansu tsakanin Musulmi a fagagen Aƙida da Shari’a da ayyuka, mas’alolin da suke rarraba kawunan Musulmai ba masu haɗa su ba, masu nesanta su da juna- Ka ga mutane suna kutsa kawunansu cikin mas’alolin saɓani ko?!, sai ya ce: Sun aikata haka?!, sai na ce: na’am, sai ya ce: Ni kuwa na ji Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Fitina za ta faru) sai na ce: mene ne mafita ya Manzon Allah? Sai ya ce: (Littafin Allah; a cikinsa akwai labarin abubuwan da suka gabace ku, da labarun abubuwan da za su zo a bayanku, da hukunce – hukuncen da suke a tsakaninku, shi ne yankakken zance da babu wasa a ciki, duk wanda ya bar shi saboda wani azzalumi (saboda tsoronsa) Allah zai karya shi, duk wanda ya nemi shiriya daga waninsa Allah zai ɓatar da shi. Shi ne igiyar Allah mai ƙarfi, shi ne zikiri mai cike da hikima, shi ne hanya madaidaiciya, shi ne wanda son zuciya ba sa sauya shi, harsuna ba sa rikicewa da shi, malamai ba sa ƙoshi da shi, ba kuma ya tsufa saboda yawan maimaitawa, abubuwan mamakin cikinsa ba sa ƙarewa. Shi ne da aljannu suka ji ba su iya haƙuri ba, sai da suka ce: Lallai mun ji abin karantawa mai ban mamaki da yake jagoranci zuwa shiriya, sai muka yi imani da shi. Duk wanda ya yi magana da shi ya faɗi gaskiya, duk wanda ya yi aiki da shi ya sami lada, duk wanda ya yi hukunci da shi ya yi adalci, duk wanda ya yi kira zuwa gare shi za a shiryatar da shi zuwa ga hanya madaidaiciya). Ya ce: sai ya ce mini: Ka riƙe shi da kyau, ya A’awar.

Ya ‘yan uwana masoya Allah,

Najeriya ba ta tsira ga barin waɗannan fitintunu da jarrabawowi ba, lallai a ‘yan kwanakin baya- bayan nan mun ga yanda aka gudanar da zanga- zangar lumana, zanga- zangar da take neman wasu haƙƙoƙi na ‘yan ƙasa, sai dai daga baya ta sauya daga halattacciyar hanyar da ta faro a kai, inda wasu masu manufofi na daban suka yi mata kutse, bayan sun shirya yin hakan da kyau, abin da ya kai zuwa ga kashe rayuka masu ƙima na ‘ya’yan wannan ƙasa mai albarka, aka lalata dukiyoyi, aka kuma dakatar da maslahohin gwamnati da na ɗaiɗaikun al’umma, har yanzu muna jin abubuwan da ba za a lamunta ba suna faruwa, amma dai maganinsu yana buƙatar hikima da azanci daga shugabanni, mu a nan muna goyon bayan a bai wa ‘yan ƙasa daman su nemi haƙƙoƙinsu da dokoki suka ba su, muna kuma kira zuwa ga shugabanni da su tashi tsaye wajen gabatar da abubuwan da suka wajaba akansu game da waɗanda suke shugabanta, su saurare su da kyau, ba ma goyon bayan kowace irin ɓarna, shi kuskure ba a gyara shi da kuskure, haka ma wajibi ne idunuwanmu su zamo a buɗe, mu lura da gadan - zaren da waɗanda ba sa son zaman lafiyar ‘yan ƙasarmu ta ɗaure, mutanen da burinsu shi ne mu cigaba da zama a yanayi na rashin tsaro, da koma baya a dukan fagage.

Wani abin baƙin ciki kuma shi ne, muna cikin gwagwarmaya da waɗannan jarrabawowin sai wata sabuwar fitinar ta sake kunno kai a ‘yan kwanakin nan, tana son kutsawa cikin hurumin shugabanmu mafi girma Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), da yin ɓatanci a gare shi, kuma hakan yana kasancewa ne da goyon baya, gami da kariya daga wata babbar ƙasa da ta yi imani da dimokraɗiyya da ‘yanci, ta kuma yi imani da adalci da daidaito da mutunta juna! Lallai matsayar da ƙasar Faransa ta ɗauka, matsaya ce da ba ma zaton tana wakiltan Faransawan da suke son zaman lafiya, suke kuma goyon bayan rayuwar tare cikin mutunta juna, lallai hankali ba zai ɗauki a ce a wannan zamanin a yaɗa ƙiyayya a kuma sosa zukatan mabiya kowane addini da gangar ba, musamman zukatan Musulmai, domin babu wata fa’ida a tare da yin hakan.

Mu Musulmai ba ma mamakin wannan abu, domin abin da yake faruwa a yanzu na yin ɓatanci ga abubuwa masu tsarkinmu, da jagororinmu cigaba ne na abubuwan da suka faru da Manzonmu mai girma da karamci (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a hannun mushrikan Makka, da cutarwar da suka yi masa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), su da waɗanda suke rayuwa a tsibirin Larabawa a lokacin, cikin waɗanda ba Musulmai ba. Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: ((Ya ku muminai, ku tabbata cewa lallai za a jarraba ku cikin dukiyoyin ku, ko dai da tawaya, ko kuma ta hanyar umurnin ciyarwa, haka ma za a jarrabce ku akan kawunan ku, ko dai da jahadi, ko rashin lafiya da zafin ciwo, kuma lallai za ku ji maganganu masu yawa na zagi, da suka, da za su ɓata maku rai daga Yahudãwã da  Kiristoci da mushrikai, to, ya zama wajibi ku fuskanci haka da haƙuri da tsoron Allah, saboda hakan yana cikin abubuwa masu kyau da ya zama wajibi a yi azamar zartar da su)) [Ali Imran: 186].

Lallai waɗannan ɓatanci da suke yawan maimaituwa a wannan lokaci, har suka zamo ta’addanci ne na zalunci akan Musulmai, abin da yake wajabta yin jahadi domin ɗaukaka kalmar Allah, domin bai wa addini, da rayuka, da mutunci, da dukiya kariya. Lallai har yanzu muna ƙara nanatawa cewa tabbas addinin Musulunci bai yarda da tashin hankali, ko wuce gona da iri, ko ta’addanci ba kwata- kwata, amma dai ya halatta bai wa addini, da rayuka kariya, da kariya ga duk wani abu da yake da jiɓi da ɗan Adam da suka haɗa da: mutunci, da dukiya, da hankali, da ƙasa, ko yanayi. Saboda wajibi ne a bai wa waɗannan abubuwa duka kariya, koda kuwa hakan ya kai ga a yi amfani da ƙarfi wajen yanke akaifar azzalumi, haƙƙin bai wa rai kariya haƙƙi ne da dukan dokoki da al’adu suka san da zamansa.

Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: ((Lallai an yi izini ga waɗanda ake yaƙarsu saboda da zalunci da su mayar da martani, tabbas Allah mai cikakken iko ne na ya taimake su. Su ne waɗanda aka fitar da su daga gidajensu ba tare da wani haƙƙi ba banda kawai sun ce Allah ne Ubangijinmu, ba domin fito na fito tsakanin mutane da junansu ba, da har wuraren bautar Yahudawa da na Kiristoci da Masallatai a ake ambaton Allah da yawa an rushe, lallai tabbas Allah zai taimaki duk wanda yake taimakonsa, lallai Allah mai cikakken ƙarfi ne, kuma buwayayye. Su ne waɗanda idan muka damƙa masu ragamar jagoranci a bayan ƙasa za su tsayar da sallah, su kuma bayar da zakka, su bayar da umurni da aikata ayyuka masu kyau, su kuma hana aikata munanan ayyuka, lallai ƙarshen dukan al’amurra a hannun Allah suke. Idan ma sun ƙaryata ka, to lallai da ma kafinsu, jama’an Annabi Nuhu, da Adawa, da Samudawa sun ƙaryata Annabawansu. Haka ma jama’an Annabi Ibrahim da jama’an Annabi Luɗu suka yi. Da ma mutanen garin Madyana (jama’an Annabi Shu’aib), an ƙaryata Annabi Musa, sai na ɗaga wa kafirai ƙafa, sannan a ƙarshe na kama su da kyau, kai kuwa ka san irin tsananin azabar da ta same su?! Sau da yawa mun halaka alƙaryun da suka zalunci kawunansu, inda muka kifar da su, ga rijiyoyinsu nan da babu masu amfana da su, ga kuma manyan gidajensu nan da aka gina wayam. Shin mene zai hana su yi tafiya a bayan ƙasa domin su sami zukatan da za su sanya su su yi tunani, ko kunnuwan da za su riƙa jin abubuwa da su, shi fa al’amarin ba idanuwa ne suke makancewa ba, zukatan da suke cikin ƙirji ne suka makancewa)) [al- Hajji: 40 -46].

A nan muna tare da hukumomin dukan gwamnatocin ƙasashen Larabawa, da na Musulunci, waɗanda suka yi tir da Allah wadai da wannan aiki na rashin kunya, haka ma muna matuƙar miƙa jinjina ga kiran manyan cibiyoyin Musulunci na duniya suka yi, kaman kiran da Imamul Akbar Farfesa Ahmad Al- Ɗayyib, Sheikhul Azhar, kuma shugaban majalisar dattijan Musulmai (Allah ya kiyaye mana shi) ya yi na wajibcin samar da dokokin da suke haramta yi wa addinai, da jigoginsu ɓatanci, muddin dai da gaske ne muna rayuwa ne a zamanin cigaba, ba a warware al’amurra da ƙarfi, ana warware matsaloli ne ta hanyar aiki da hankali da zai kai zuwa ga samun natsuwa da kwanciyar hankali, ya kuma kiyaye zaman lafiya da tsaro na duniya.

Haka ma a daidai wannan lokacin muna ƙara kira da babban murya zuwa ga Majalisar ɗinkin Duniya, a matsayinta na ƙungiyar da ta haɗa dukan ƙasashe, wanda kuma a cikin muhimman ayyukanta akwai kiyaye tsaro da zaman lafiyan duniya, muna kiranta da ta duba wannan mas’ala ta yin ɓatanci ga addinai, da jigogin addinai da kyau kuma da gaske, domin ta yi mata burki, saboda idan har rikicin addini ya ɓarke babu wanda ya san ranar kawo ƙarshensa, ko yawan asarar da hakan zai haifar a faɗin duniya. Haka ma muna kira zuwa ga ɗaukacin cibiyoyin tattaunawa tsakanin addinai na duniya, da ma shugabannin wasu addinan wato Fastoci da Fada- fada, da malaman Yahudawa, da Majalisar Dattijan Musulmai da a cikin tsare – tsarensu suka rungumi (shirin tattaunawa tsakanin ƙasashen gabashin Duniya da yammancin duniya), da (Yarjejeniyar ‘yan uwantaka ta mutuntaka), da ma cibiyar Muhammadus Sadis na malaman Afrika, da cibiyoyin bincike da muhimman nazari da dokoki a ƙasashen Larabawa da na Musulmai, da su ruɓanya ƙoƙarin da suke yi da nufin kiyaye tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da kuma killace waɗannan munanan ayyuka da kamata ya yi su zamo suna faruwa ne daga ɗaiɗaikun mutane, a kuma tsayar da abin a haka, amma idan har babban ƙasa, ko babban cibiya za ta bayar da kariya ga irin waɗannan ayyuka masu cutarwa, to wannan abu ne da ba za a lamunta ba, akwai buƙatar ɗaukan matakai masu ƙarfi a cikin al’umma domin yi wa tufkar hanci.

A ɓangarenmu mu Musulmai kuma, waɗanda muke murna da wannan lokaci domin mu sami ingantacciyar rayuwa saboda shi, mu kuma farka daga gafalar da muka yi, mu koma zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki ta hanyar tuba ta gaskiya, to wajibi ne mu sake jaddada mubaya’armu ga shugabanmu Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), mu sake bitar kawunanmu, dukanmu, sawa’un shugabanni ne, ko masu manyan muƙamai da ƙanana a gwamnati, ko sarakuna da malamai, ko halifa daga cikin halifofin ɗariƙun Sufaye, ko muƙaddamai da muridai, da shugabannin ƙungiyoyin Musulunci, ko ‘yan kasuwa, ko ‘yan siyasa, mata da maza, tsoho da matashi, dukan mu mu tambayi kawunammu a cikin sirri, muna masu gabatar da gaskiya da kuma yi domin Allah, shin yaya matsayarmu yake game da abin da aka halicce dominsa, lallai a nan ya kamata mu yi koyi da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya saukar masa da wannan ayar da take cewa: ((Lallai a cikin littafin Zabura  a bayansa da At Taura mun riga mun rubuta cewa: lallai bayi na salihai ne za su gaje doron ƙasa. Lallai a cikin hakan akwai isasshen saƙo ga mutanen da suka duƙufa wajen yin ibada. Mu kam ba mu aiko ka ba sai domin ka zama rahama ga ɗaukacin halitta. Ka ce masu: Ni fa kawai wahayi ake yi mini akan cewa Allahnku Allah ne guda ɗaya, shin ba za ku zamo Musulmai ba?!)) [al- Anbiya: 105 -108].

Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: ((Ya ku mutane lallai ku ne masu buƙata a wurin Allah, Allah kam shi ne mawadaci kuma abin gode ma wa. In ya so sai ya ɗauke ku ya kawo wasu halittun na daban. Wannan ba abu ne da zai gagari Allah ba. Wani rai mai zunubi ba zai ɗauki zunubin wani ba, idan wani rai da yake ɗauke da zunubi ya kira wani domin ya ɗauke masa zunubin a maimakonsa babu abin da zai ɗauke masa, koda kuwa ɗan uwa ne makusanci; saboda kowa ya shagalta ne da kansa, saboda haka -ya RasulalLahi- kada taurin kan jama’anka ya dame ka, lallai gargaɗinka kawai zai amfani mutanen da suke tsoron Ubangijinsu ne a fake, suka kuma tsayar da sallah kaman yanda ya kamata, wanda duk ya tsarkaku daga barin dauɗar zunubai ya yi wa kansa ne, gaba ɗayan makoma tana wurin Allah ne, shi ne kuma zai saka wa kowa da abin da ya cancanta)) [Faɗir: 15 – 18].

Ya ‘yan uwana masoya Allah,

Lallai a halin da muke ciki a yau babu abin da zai faranta zukata, in banda mutane kaɗan ɗin da suka tsaya a ƙofar Allah Maɗaukakin Sarki, suna ƙasƙantar da kai, da addu’a ba dare ba rana; domin Allah ya yaye wannan bala’i, ya ɗauke wannan mummunan abu ga barin al’umma. Waɗannan mutane kaɗan ɗin daga cikin malamai salihai, da masu bauta, da bayin Allah na gari, da masu gudun duniya, waɗanda su ne madogara bayan Allah Maɗaukakin Sarki wajen gyara al’umma, dole ne su fara da bitar kawunansu, da sanya wa kawunansu ido da gaske saboda su gyara kura- kurai, su kuma sami ƙarin himma da ɗamfaruwa da Allah, da yin watsi da duk wani abu ba shi ba, suna masu koyi da shugabanmu, kuma masoyinmu zaɓaɓɓen Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a wurin maganganu da ayyuka da yanayi, da haka ne kawai za mu iya ɗaukan amanar da Allah ya ɗaura mana, mu kuma sauke nauyin da ya rataya akanmu game da addininmu da ‘yan uwanmu da ƙasashenmu, mu kuma sami yardar Allah da ƙabuli da ikon Allah.

A daidai wannan lokaci muna son mu isar da saƙo na musamman zuwa ga ‘yan uwanamu halifofi da muƙaddamai da muridai a cikin ɗariƙar Tijjaniyya, kai har ma da sauran ɗariƙu; saboda dukansu hanyoyi ne da suke isarwa zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki, kaman yanda Imam al- Busairiy (Allah ya ƙara masa rahama) ya faɗi cewa:

“Dukansu a wurin Manzon Allah suke neman koda kamfata ɗaya ne na ruwan kogi, ko ɗan yayyafi na mamako”.

Lallai a ‘yan baya- bayan nan wani al’amari -wanda ba a san shi ba a baya yana faruwa, ta yiwu ya zama alhairi- wannan abu kuwa shi ne: mutane da yawa suna neman su sami izinin zama muƙaddamai a ɗariƙar Tijaniyya, wannan abu ne da yake nuna kyakkyawan albishir na yaɗuwar ɗariƙa daidai da sharuɗɗanta da suka ginu akan karantarwar Alƙur’ani da Sunna. Sai dai duk da haka, muna son mu jawo hankulan jama’a baki ɗaya, su fa Shaihunai a lokacin da suke bayar da ijaza a haƙiƙanin al’amari suna zaɓen mutane ne akan cewa sun cancanci su yi wa addini hidima da gaskiya kuma cikin Ikhlasi, da yaƙini, da dogaro ga Allah Maɗaukakin Sarki, tare kuma da cikakkiyar tsayuwa akan karantarwar Shari’ar Musulunci, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: ((Saboda haka ka yi kira zuwa ga Allah, ka kuma tsaya da kyau kaman yanda aka umurce ka, kada ka kuskura ka bi son zukatansu, ka ce: Na yi imani da abin da Allah ya saukar na Alƙur’ani, an kuma umurce ni da in yi adalci a tsakaninku, Allah shi ne Ubangiji na kuma Ubangijinku, ayyukanmu namu, ku ma ayyukanku naku ne, babu wani rikici a tsakaninmu da ku, Allah ne zai haɗa tsakaninmu, kuma makomarmu tana gare shi ne)) [as- Shura: 15].

Idan muƙaddami ya yi aiki da Alƙur’ani da Sunna daidai iyawarsa, ba kuma tare da ya jirkita, ko ya sauya, ko ya saɓa ba, ya kuma yi kira zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, abin da har ya kai ga Allah ya bayyanar da albarkar ayyukansa masu kyau ga mutane na kusa da na nesa, mutanen zamaninsa suke yi masa shaida da tsoron Allah da zamowarsa na gari, gami da tsayawa akan hanyar gaskiya, to kuwa lallai hakan dalili ne da yake nuna cewa Allah Maɗaukakin Sarki ya riga ya ƙaddamar da shi wajen shiryatar da halittu, da mayar da su zuwa ga bin hanyar waɗanda suka koma zuwa gare shi, ya kuma yi masu ni’ima cikin Annabawa, da siddiƙai, da shahidai, da salihai, a wannan lokacin Allah zai azurta shi da dacewa da kuma yin daidai a dukan yanayin da yake ciki, ya sanya shi cikin mataimaka Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) wajen isar da kiransa gami da saƙonsa, to a wannan lokacin ne Allah Maɗaukakin Sarki zai amshi wannan zaɓin, ya ƙaddamar da shi, domin da ma Allah Maɗaukakin Sarki shi ne mai ƙaddamarwa na haƙiƙa.

Idan wannan da aka ƙaddamar ya kauce hanya, kaman yanda muke gani a tare da da yawa daga cikin masu intisabi da janabi mafi girma, ya bi son zuciyarsa, ya aikata abin da ya ga dama na saɓa wa Shari’a, da kuma halatta haka, hasali ma da kiran mutane zuwa ga aikata haka, da kuma ƙarfafa masu gwiwa, tare kuma da amincewa da makrulLahi, to wannan mutumin za a ce yana da takardar izinin muƙaddamanci, sai dai fa ayyukansa su ne za su koma da shi baya, ya zamo jana- baya, a nan Allah ne ya dawo da shi baya; saboda shi ne haƙiƙanin mai dawowa da bayi baya, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: ((Yanzu sun aminta da makrulLahi ne?!, lallai kam babu wanda zai aminta da makrulLahi sai jama’an da suka yi asara)) [al- A’araf: 99].

Saboda haka da gaske muke kiran ‘yan uwanmu da su sake nazari game da wannan al’amari, kowa ya koma bisa ga ƙa’idojin asali da akansu ne aka gina zama da salihan bayin Allah, da ma zama da su ɗin ya zamo saboda Allah, wanda a duk sanda muridi ya tafi wurin shaihi, to ya tafi domin ya yi masa mubaya’a akan Alƙur’ani da Sunna, domin a isar da shi zuwa ga cikakken sanin Allah Maɗaukakin Sarki na ainihi, ba wai saboda wata manufa ba, ana kuma yin haka ne har zuwa lokacin da wannan muridin zai tsarkaka, ya zamo al’umma ta musamman da yake kira zuwa ga alhairi, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya sa mu dace, mu zamo akan hanya madaidaiciya.

A ƙarshe, ya ‘yan uwana masoya Allah,

Muna kiranku da ku dawwama wajen fuskantar Allah Maɗaukakin Sarki da addu’o’i dare da rana, akan Allah ya haɗa kawunanmu cikin soyayya, da tsarkin zukata, da kuma taimakekeniya mai alfanu, wanda za ta kai mu zuwa ga haɗin kan al’ummar Musulunci a ko’ina a faɗin duniya da ikon Allah.

Kaman yanda muke yin addu’a ta musamman ga jagororinmu a dukan matakai, musamman mai girma Muhammadu Buhari, shugaban ƙasar Jamhoriyar tarayyar Najeriya, da mataimakansa cikin shugabanni a gwamnatin tarayya, Allah ya kiyaye mana su baki ɗaya. Haka ma gwamnan Jahar Barno, jahar zaman lafiya, mai girma Alhaji Baba Gana Umara Zulum, da mataimakansa a jaha. Haka ma dukan mambobi na majalisar dattijai, da na wakilai a matakin tarayya da na jahohi, da dukan gwamnoni, da ministoci da shugabannin tsaro, da mai alfarma Sultan Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Sokoto, da mai alfarma Shehun Barno Alhaji Dr. Abubakar Bn Umar Garbi al- Kanemi, da sauran sarakuna, da masu girma malamai, da shugabannin ƙungiyoyin Musulunci da na matasa da na mata, da shugabannin jam’iyyun siyasa, da ma sauran shugabanni da suke jagorantar ‘yan ƙasa Najeriya, Allah ya kiyaye mana su gaba ɗaya. Muna roƙa masu –gaba ɗaya- Allah ya yi masu jagoranci wajen ɗaukan matakan da suka dace, matakan da za su kai zuwa tabbatar da tsaro, da zaman lafiya, da kwanciyar hankali a faɗin ƙasa baki ɗaya, su kuma kai zuwa ga yaye damuwa da wahalhalun da ‘yan ƙasa suke fama da su a dukan fagagen rayuwa, ya kuma cigaba da zaunar da Najeriya lafiya a matsayin ƙasa ɗaya al’umma ɗaya, inda dukan ‘yan ƙasa za su sami cikakken haƙƙoƙinsu da dokoki suka tabbatar masu da ikon Allah. Haka ma muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya kiyaye matasanmu daga faɗawa cikin gadan - zaren da maƙiya suke shiryawa, waɗanda za su kai zuwa ga cutar da ƙasarmu da muke matuƙar sonta, ƙasar da ya zama wajibi mu kiyaye ta saboda al’umma masu tasowa su amfana da ita, kaman yanda magabatanmu masu daraja (Allah ya ƙara masu rahama) suka kiyaye mana ita.

Haka ma wannan saƙon muke aikawa zuwa ga matasa a ko’ina a faɗin duniya, musamman a ƙasar Yaman, da Syria da Libya da Misra da Sudan da Chadi da sauran ƙasashen Larabawa da na Musulunci, su rinƙa sauraron malamai da masana, kowa a fagensa, cikin dattijai da masu hikima, su amfana da ƙwarewa gami da ilimin da Allah ya ba su domin su haskaka masu wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, da cigaban ƙasashensu ta hanyoyin ilimi da cigaba, ba kuma tare da sun auka cikin tarkon maƙiya, sakamakon amsa kiran son zuciya da ruɗi, ko ƙare-rayin ‘yan jarida ba, haka ma dole ne a faɗaka a san cewa: kyawon manufa ba zai taɓa halatta bin karkatacciyar hanya ba a cikin shari’armu mai girma, domin Allah ya ɗaura mana wajibcin bin nagartattun hanyoyi kaman yanda ya wajabta mana isa zuwa ga manufofi masu kyau. Lallai duk wata matsala ta duniya akwai cikakken maganinta a cikin shiryatarwar Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), sam bai kamata mu yi amfani da ƙarfin matasa a matsayin makamashin da za a cutar da al’ummar Musulmai da shi, a kuma mayar da ita baya ba, a daidai lokacin da maƙiyanmu suke amfana da waɗannan rikice – rikice da suka shirya masu tun da daɗewa, wannan shi ne abin da yake faruwa a yau –abin baƙin ciki- a ƙasashe masu yawa.

Allah ya amsa dukan ayyukanmu, ya kuma saka wa duk wanda ya bayar da gudummuwa wajen nasarar wannan taro mai girma, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya ba mu –mu da ku- cikakkiyar lafiya da tsawon kwana, ya kuma biya mana dukan buƙatu na zahiri da na baɗini, haka ma muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya mayar da dukan waɗanda suka halarci wannan taro daga garuruwa masu nisa zuwa gidajensu lafiya cikin aminci da samun lada albarkar wanda aka yi taron dominsa, masoyinmu Zaɓaɓɓen Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam). Kaman yanda muke roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya sake maimaita mana, a lokacin al’amurra sun sauya sakamakon sauya ɗabi’unmu zuwa ga abin da ya fi dacewa, har zuwa mu sami zamowa cikin waɗanda suka cancanci samun yardar Allah Maɗaukakin Sarki da ta Manzonsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), ya kuma faranta zukatan muminai da ikon Allah, wannan ba abu ne da zai gagari Allah ba.

Ku huta lafiya, Allah ya maimaita mana.

Wassalamu alaikum wa rahmatulLahi ta’ala wa barakatuhu.